Leadership News Hausa:
2025-10-15@16:40:57 GMT

Newcastle Na Gab Da Samun Gurbi A Gasar Zakarun Turai

Published: 13th, April 2025 GMT

Newcastle Na Gab Da Samun Gurbi A Gasar Zakarun Turai

Newcastle ta lallasa Leicester da ci 3-0 a ranar Litinin a gasar Firimiya Lig ta Kasar Ingila, wasan wanda ya kasance na 8 a jere da Leicester City ta buga ba tareda jefa kwallo a raga ba, Newcastle da Eddie Howe ke jagoranta na fatan ganin sun samu gurbi a gasar Zakarun Turai na badi, tun da farko dai sun lashe gasar League Cup a watan da ya gabata.

Yanzu haka su na matsayi na biyar a kan teburin Firimiya, inda suke da maki daya da Chelsea da ta ke matsayi na hudu, Leicester City kuma a nata bangaren ka iya komawa gasar ‘yan dagaji ta Championship idan aka doke su a wasansu na gaba a gasar.

Yadda Tashar Jirgen Ruwan Apapa-Moniya Za Ta Taimaka Wa Masu Safarar Fitar Da Kaya NIMASA Za Ta Adana Wa Nijeriya Dala Biliyan 400 A Shekara Daga Cazar Kudaden Safarar Kaya

Newcastle, wacce arzikinta ya bunkasa tun bayan da mamallakanta ‘yan Kasar Saudiyya su ka karbi iko a shekarar 2021, ta na neman sake samun damar buga gasar Zakarun Turai tun bayan wanda aka kore ta a shekarar 2023/24 bayan shafe shekaru ashirin.

Howe, wanda ya jagoranci Newcastle lashe babban kofi na farko cikin shekaru 56 a wasan da su ka doke Liverpool a Wembley a watan da ya gabata, ya na da damar kara haskakawa a wannan kakar wasanni ta bana mai dimbin tarihi a wajen Newcastle.

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

উৎস: Leadership News Hausa

কীওয়ার্ড: Gasar Zakarun Turai

এছাড়াও পড়ুন:

An Janye Wajibcin Samun Kiredit A Darasin Lissafi Ga Ɗaliban Fannin Zamantakewa Don Shiga Manyan Makarantu 

ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai Majalisar Wakilai Ta Buƙaci Hukumomin Tsaro Su Kai Agajin Gaggawa A Sakkwato October 14, 2025 Labarai An Kashe Mutum 3, Wasu 7 Sun Jikkata Sakamakon Ɓarkewar Rikici A Jihar Jigawa October 14, 2025 Manyan Labarai Rashin Tsaro A Nijeriya Ba Zai Ƙare Ba Matuƙar Ba A Samar da Ayyukan Yi Da Mulki Na Adalci Ba – Amaechi October 14, 2025

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • An Bukaci An Bukaci Asusun JICHIMA Ya Fadada Hanyoyin Samun Kudade Baya Ga Gwamnatin Jigawa
  • Shugaba Tinubu Ya Taya Super Eagles Murnar Samun Cancantar Shiga Gasar Kwallon Kafa Ta Duniya
  • Madugun ’yan adawar kasar Kenya, Raila Odinga, ya mutu
  • Dalilin Da Ya Sa Mutane Ke Dawowa Jam’iyyar APC — Shettima
  • Gidauniyar Sheikh Dahiru Bauchi Ta Tura Ɗalibai 117 Karatu Ƙasar Algeria 
  • An kama mata da miji suna safarar makamai a Kaduna
  • An Janye Wajibcin Samun Kiredit A Darasin Lissafi Ga Ɗaliban Fannin Zamantakewa Don Shiga Manyan Makarantu 
  • Sakin Maryam Sanda shi ne ƙololuwar zalunci —Dangin Bilyaminu
  • Faɗa ya ɓarke tsakanin Palasɗinawa da Hamas bayan sulhu da Isra’ila
  • An Sauya Kwamishinan Ƴansandan Abuja Saboda Rashin Tsaro