Jami’an tsaro Gwamnatin Tarayya suna sassauta wa masu kashe mutane babu gaira babu dalili a Jihar Filato, a cewar tsohon jihar na mulkin soji, Rear Admiral Samuel Bitrus Atukum.

Da yake tsokaci kan kisan gillar da ka yi wa mutane 52 tare da lalata kadarori na miliyoyin naira baya-bayan nan a yankin Ƙaramar Hukumar Bokkos, Atukum ya ce, “Ina da matsala kan yadda jami’an tsaro ke tunkarar matsalar.

A gani na suna sassauta musu. Mene ne abu mai wahala a ba wa sojoji umarni su je maɓoyar masu wannan aika-aika su kamo su?

“Daga kan tsaunuka mutanen nan suke saukowa ɗauke da makamai su halaka jama’a, sannan su ɓace, kuma a nan suke ɓoye makamansu. Saboda haka ya kamata jami’an tsaro su yi fiye da  abin da suke yi yanzu.

“Kamata ya yi a ayyana waɗannan mutane a matsayin ’yan ta’adda, saboda ta’addanci suke yi, amma an kasa, sai a je ana kama masu ƙananan laifi da sunan manyan laifuka,” in ji Atukum wanda shi ne gwamnan Filato daga 1984 zuwa 1985.

Mahaifi ya yi wa ’yarsa ciki a Bauchi An gano gawar makiyayi da ƙwato shanu a Filato Mutane 300 sun kamu da cutar sanƙarau Sakkwato

Ya bayyana cewa a lokacin da yake gwamna rikicin addini na ƙungiyar Maitatsine ya ɓarke, amma cikin ɗan ƙanƙanin lokaci aka murƙushe shi, saboda gwamnati ta tari matsalar tun daga tushe kafin a je ko’ina.

Ya ce idan za a ɗauki irin matakin daga sama a kan matsalar tsaron Filato, shugaban ƙasa ya ba wa jami’an tsaro umarni a matsayinsa na Babban Kwamandan Tsaron Ƙasa, za su yi abin da ya kamata.

“Amma ba a ba da umarni ko ɗaukar mataki ba, sai mutane sun yi ta ƙorafi kan matakin da gwamnati ta ɗauka, sai a fito ana cewa za a kamo waɗanda suka aikata abin, a hukunta su daidai da abin da doka ta tanada. Wannan shi ne abin da muke ta ji.”

Ya ce, “Da ni ke da iko, da umarni da wa’adi ƙarara zan na wa jami’an tsaro cewa ga abin da nake so. Idan shugaban ƙasa da gaske yake kan matsalar tsaro, umarni kawai zai bayar kuma yana da tasiri a kan Majalisar Dokoki ta Ƙasa, duk abin da yake so za ta yi aiki a kai, kuma a tafi tare da ɗaukacin al’ummar ƙasa.

“Amma ya za a yi ka ce kana maganin abun, amma ba a ga alamar komai ba? Wa zai ɗauka da gaske kake, alhali ba a ga an kamo masu aikata laifin an hukunta su ba?

“A wannan yanayi da matsala ke fama da matsalar rashin aiki, mutane za su yi ta amfani da irin wannan giɓi wajen yin irin waɗannan aika-aika da muke gani.

“Har ta kai ga masu yin wannan ta’asa na ba da umarnin cewa ga wanda suke so a naɗa a matsayin shugaɓan wata hukumar tsaro, ko kuma a sauke wanda yake kai,” in ji tsohon gwamnan sojin.

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: hukumomin tsaro Jami an Tsaro jami an tsaro

এছাড়াও পড়ুন:

An Kama Direban Gwamnati Da Hannu A Satar Motar Ofishin Mataimakin Gwamnan Kano

A cikin wata sanarwa da aka fitar a ranar Laraba, Sakataren Yada Labarai na ofishin mataimakin gwamna, Ibrahim Shu’aibu, ya bayyana lamarin a matsayin “cin amana a fili da direban da aka kama ya yi.”

 

“Ofishin Mataimakin Gwamna ya yaba wa binciken gaggawa da rundunar tsaron ta yi ta hanyar amfani da kaifin basira da kwarewa,” in ji sanarwar.

ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai Za Mu Kare Sojojin Da Ke Bakin Aiki — Ministan Tsaro November 12, 2025 Manyan Labarai Bayanan Da Muka Samu Sun Nuna An Fara Samun Tsaro A Nijeriya – Hafsan Sojin Ƙasa November 12, 2025 Manyan Labarai Yadda Ɓarawo Ya Shiga Gidan Gwamnatin Kano Ya Saci Motar Ayarin Mataimakin Gwamna November 12, 2025

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Mutum ɗaya ya rasu yayin da ’yan sanda da ’yan bindiga suka yi artabu a Kwara
  • Tsohon Gwamnan Anambra, Willie Obiano, Ya Rasu Yana Da Shekaru 70
  • An dakatar da Hakimi da Dagaci kan rikicin manoma da makiyaya a Gombe
  • Madalla Da Sabon Binciken Jami’ar Nankai Ta Kasar Sin Kan Mata Marasa Haihuwa
  • Wike: Za mu kare duk wani soja da ke aiki bisa doka — Ministan Tsaro
  • An Kama Direban Gwamnati Da Hannu A Satar Motar Ofishin Mataimakin Gwamnan Kano
  • AIG Zubairu Ya Umurci ‘Yan Sanda a Kwara Su Ninka Kokarinsu Don Karfafa Tsaro
  • ‘Yan Bindiga Sun Kashe Mutane 3 Tare Da Sace Babur A Nasarawa
  • ‘Yansanda Sun Kama Masu Laifi Sama Da 200 A Katsina
  • DAGA LARABA: Tasirin Da Tura Jami’an ‘Yan Sanda Kare Manyan Mutane Zai Haifar Ga Tsaron Al’umma