DAGA LARABA: Abin Da Ya Sa ‘Matar Bahaushe Ba Ta Iya Kiran Sunan Mijinta’
Published: 9th, April 2025 GMT
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba
Tun kaka da kakanni an san Hausawa da kawaici da kunya da kuma girmama na gaba da su.
Mai yiwuwa wadannan dabi’u ne suka sa matar Bahaushe ba ta iya hada ido da mijinta, balle ta kira shi da sunansa na yanka.
To amma a zamanin yau ba abin mamaki ba ne a samu matar aure ta kalli kwayar idon mijinta, ta kuma kira shi da sunansa na yanka.
A kan wannan al’ada – asalinta da alfanunta da dalilan sauyawarta – shirin Daga Laraba na wannan makon za iyi nazari.
Domin sauke shirin, latsa nan
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: kiran sunan miji kunya matar bahaushe
এছাড়াও পড়ুন:
Tinubu ya karɓi baƙuncin Abdulmumin Jibrin Kofa
Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya karɓi baƙuncin ɗan Majalisar Tarayya mai wakiltar ƙananan hukumomin Kiru da Bebeji na Jihar Kano, Abdulmumin Jibrin Kofa.
Aminiya ta ruwaito cewa Kofa, wanda makusanci ne ga jagoran Kwankwasiyya, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso, kuma ɗaya daga cikin jiga-jigai a jam’iyyar NNPP, ya ziyarci shugaban ƙasar ne a yau Laraba.
Za a kammala shimfiɗa layin dogo daga Kaduna zuwa Kano a 2026 — Gwamnatin Tarayya Tattalin arzikin Nijeriya zai ci gaba da bunƙasa har zuwa baɗi — IMFHar yanzu dai babu wasu bayanai dangane da abin da suka tattauna, amma ziyarar wadda hadimai daga ɓangarorin biyu suka riƙa yaɗawa na ci gaba da ɗaukar hankalin jama’a.