Matsalar tsaro: Ba za mu lamunci zagon ƙasa ba — Gwamnatin Sakkwato
Published: 8th, April 2025 GMT
Gwamnatin Sakkwato ta yi barazanar sanya ƙafar wando da waɗanda ta yi zargi suna ƙoƙarin kawo mata cikas a yaƙin da take yi da ’yan bindiga da sauran matsalolin tsaro a Jihar.
Ta gargaɗi mazauna da su shiga taitayinsu game da yin kalamai da za su iya kawo cikas ga ƙoƙarinta na magance matsalar rashin tsaro a jihar.
Wannan gargaɗin ya biyo bayan wata sanarwa da ake dangantawa wani mai suna Basharu Altine Guyawa wanda ya yi ƙoƙarin nuna cewa gwamnati ba ta yi abin da ya kamata ba a fannin tsaro.
Mai ba Gwamna Ahmed Aliyu shawara na musamman kan harkokin tsaro, Kanar Ahmed Usman mai ritaya, ya yi wannan gargaɗin a cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Litinin.
Mahara sun yi garkuwa da fiye da mutum 50 a Katsina NAJERIYA A YAU: Dabarun Samun Kuɗaɗe Ta Hanyar Amfani Da Wayar HannuUsman ya ce irin wannan kalaman suna iya sanya mutane butulce wa abin da gwamnati da jami’an tsaro suke yi wajen kawo ƙarshen matsalar tsaro a jihar.
Ya ce “Ya kamata mutanenmu su guji yin magana da tayar da hankali da kuma siyasantar da matsalar tsaro. A maimakon haka, ya kamata su goyi bayan gwamnati a ƙoƙarinta na neman hanyoyin magance matsalolin tsaronmu na dindindin.
“Gwamnati ba za ta lamunci duk wani yunƙurin wani mutum ko ƙungiya na kawo cikas ga ƙoƙarinta ko kuma shagaltar da ita a wannan batun ba.
“Gwamnatin jihar tare da haɗin gwiwar hukumomin tsaro sun kasance suna aiki tuƙuru don maido da zaman lafiya, musamman a yankin gabashin jihar da ke fuskantar ƙalubalen tsaro.
“Gwamnati kwanan nan ta yi wani aiki na haɗin gwiwa a yankin wanda ya samu gagarumar nasara yayin da aka lalata maboyar ’yan bindiga da dama da aka gano tare da kashe ’yan ta’adda da dama a cikin aikin. Bugu da ƙari, an kuma ceto daruruwan waɗanda aka yi garkuwa da su a lokacin aikin.”
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: gargaɗi Sakkwato Tsaro
এছাড়াও পড়ুন:
Gwamna Yusuf Ya Kafa Kwamitin Bincike Kan Mutumin Da Ake Tuhuma Da Safarar Miyagun Kwayoyi
A kokarinsa na gano hakikanin dalilan da suka sa aka bayar da beli ga wani sanannen mai safarar miyagun kwayoyi, Sulaiman Aminu Dan Wawu, da aka ce an sako shi bisa umarnin Kwamishinan Sufuri na Kano, Ibrahim Ali Namadi, Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf ya kaddamar da wani kwamiti na mutum takwas domin gudanar da bincike mai zurfi.
Sakataren Gwamnatin Jihar Kano, Alhaji Umar Faruk Ibrahim ne ya kaddamar da kwamitin a madadin gwamnan.
An umurci kwamitin da ya gudanar da binciken cikin mako guda, domin gano hakikanin abin da ya faru da kuma ba da shawarwari kan matakin da ya dace a dauka.
Shugaban kwamitin shi ne Mai Bai wa Gwamna Shawara kan Harkokin Shari’a da Dokoki, Barista Aminu Hussaini, yayin da Mambobin kwamitin suka hada da Barista Hamza Haladu, Barista Hamza Nuhu Dantani, Darakta Janar na Hukumar Ayyuka na Musamman, Manjo Janar Muhammad Sani (rtd), Comrade Kabiru Dakata, da Farfesa Mamun Mustapha daga Jami’ar Kimiyya da Fasaha ta Aliko Dangote da ke Wudil.
Sauran mambobin sun hada da Alhaji Abdullahi Mahmud Umar, Kwamishina II na Hukumar Kula da Ma’aikata, da Hajiya Bilkisu Shehu Mai Mota, Babbar Sakatariya a Sashen Gudanarwa da Sauran Ayyuka na ofishin Sakataren Gwamnatin .Jihar, wadda za ta rike matsayin Sakatariya ga kwamitin.
Gwamna Yusuf ya bayyana damuwarsa matuka kan zargin da ake yi, inda ya sake jaddada kudirinsa na yaki da safarar miyagun kwayoyi da duk wani nau’in barna a cikin al’umma.
Sakataren Gwamnatin Jihar ya bayyana kwarin gwiwarsa kan mambobin kwamitin, yana mai cewa an zabo su ne bisa cancanta, kwarewa, karsashi, da kuma kwarin gwiwar cewa za su gudanar da wannan aiki yadda ya kamata.
Abdullahi Jalaluddeen