Girgizar ƙasa ta hallaka sama da mutum 1000 a Myanmar
Published: 29th, March 2025 GMT
Gwamnatin Soji ta Myanmar, ta bayyana cewa mutum 1,002 sun rasa rayukansu sakamakon girgizar ƙasa mai ƙarfi da ta auku a ranar Juma’a.
Sama da mutum 2,000 sun jikkata, kuma ana ci gaba da ceto waɗanda suka maƙale a ƙarƙashin gine-ginen da suka rushe.
Mutum 14 sun shiga hannu kan kisan ’yan Arewa a Edo An kashe mutum 10 a wani sabon hari a FilatoJami’an agaji sun ce girgizar ƙasar ta fi shafar birnin Mandalay, inda asibitoci suka cika maƙil da waɗanda suka jikkata.
Shugaban mulkin soji na Myanmar, ya nemi taimakon ƙasashen duniya, amma ana fargabar yaƙin basasa da ke ci gaba a ƙasar zai hana ayyukan jin-ƙai tafiya yadda ya kamata.
Hukumar kare haƙƙin bil adama ta Majalisar Ɗinkin Duniya, ta ce Myanmar na cikin yaƙi tun shekaru huɗu da suka wuce, wanda ya haifar da zargin cewa dakarun soji na tsare ɗaruruwan mutane.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Girgizar kasa Gwamnatin Soji Mutuwa Myanmar
এছাড়াও পড়ুন:
An kashe mafarauta 10 a Adamawa
Aƙalla wasu mutum 10 mafarauta sun rasa rayukansu yayin aikin ceto a ƙauyen Kopire da ke Ƙaramar Hukumar Hong ta Jihar Adamawa.
Shugaban ƙungiyar mafarautan Nijeriya reshen Arewa maso Gabas, Shawulu Yohanna ne ya tabbatar wa Aminiya hakan a ranar Talata.
Wani abin fashewa ya kashe mutum 26 a Borno An dawo da wutar lantarki a Sifaniya da PortugalA cewarsa, ajali ya katse hanzarin mafarautan ne yayin wani arbatu da mayaƙan Boko Haram da suka yi musu kwanton ɓauna a jeji.
Ya bayyana cewa, mafarautan sun tunkari maharan ne bayan samun bayanan sirri da ke nuna cewa suna shirin kai hari.
“Abin takaicin shi yadda ake yi wa Gwamnan Borno ƙafar ungulu a ƙoƙarin da yake yi na ganin an kawo ƙarshen wannan hare-hare a yankin,” in ji shi.
Yohanna ya bayyana damuwa kan yadda mayaƙan Boko Haram ke ci gaba da ƙara ƙarfi a bayan nan da ke zama abin fargaba ga mazauna yankunan da abin ya shafa.
“Mun samu labarin cewa wani jirgi mai saukar ungulu ne yake jigilar mayaƙan daga sansaninsu zuwa wuraren da suke sheƙe ayarsu ba tare fuskantar wata tirjiya ba.
“Amma ina mai tabbatar da cewa muddin Gwamnatin Tarayya ta ɗauki mataki ta hanyar tanadar makamai na zamani, za a kawo ƙarshen waɗannan maƙiya cikin lokacin ƙanƙani.”
Ya roƙi Gwamnatin Tarayya da ta tanadar wa mafarauta da ’yan sa-kai manyan makamai na zamani domin kawo ƙarshen mayaƙan Boko Haram a yankin.
Wannan harin dai na zuwa ne ƙasa da sa’o’i 12 da wasu ’yan ta’adda suka kashe fiye da mutum 30 ciki har da mata da ƙananan yara a ƙananan hukumomin Kala Balge da Gambarou Ngala da ke jihar.