’Yan sanda sun ƙwato wa mutumin da aka sace kuɗin fansarsa a Kano
Published: 28th, March 2025 GMT
Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kano,m, ta ƙwato kuɗi Naira 4,850,000 tare da mayar da su ga wani mutum da aka sace, bayan sun ceto shi.
A wata sanarwa da kakakin rundunar, SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya fitar, ya bayyana cewa an yi garkuwa da mutumin ne a garin Zakirai, a Ƙaramar Hukumar Gabasawa.
An kashe ƙasurgumin ɗan bindiga Isuhu Yellow a Zamfara Lakurawa sun kashe jami’an Kwastam 2 a KebbiMasu garkuwar sun fara neman kuɗin fansa Naira miliyan 15 kafin daga bisani jami’an tsaro suka shiga lamarin.
“Bayan samun labarin garkuwar, jami’anmu sun ƙaddamar da bincike, inda suka kama mutum biyar da ake zargi, sannan suka ceto wanda aka sace a ranar 17 ga watan Maris,” in ji sanarwar.
An mayar da kuɗin ne ta hannun shugaban Ƙaramar Hukumar Gabasawa, Sagir Usman Abubakar, wanda ya bayyana godiyarsa a madadin wanda aka sace da mutanen yankin.
Kwamishinan ’yan sandan jihar, CP Ibrahim Adamu Bakori, ya yi kira ga al’umma da su ci gaba da bai wa jami’an tsaro haɗin kai, ta hanyar kai rahoton duk wani abu da suke zargi domin daƙile ayyukan miyagu a Kano.
উৎস: Aminiya
এছাড়াও পড়ুন:
Bom ɗin Boko Haram ya kashe mutane 26 a Borno
Wasu abubuwan fashewa da ake zargin ’yan ta’addan Boko Haram ne suka dasa, sun kashe kimanin mutane 26, ciki har da mata da ƙananan yara a kusa da garin Rann da ke Ƙaramar Hukumar Kala Balge ta Jihar Borno.
Majiyoyin tsaro da na cikin gari sun bayyana cewa mutane da dama sun jikkata bayan da motar da ke ɗauke da wadanda abin ya shafa zuwa Gambarou Ngala ta taka abin fashewar.
Wata majiya ta ce, “Ba a tantance adadin mutanen da suka mutu ba, amma rahotanni na farko sun nuna cewa mata huɗu da yara shida da maza 16 ne suka mutu a wannan fashewar.”
Ta ci gaba da cewa lamarin ya faru ne a kan hanyar Furunduma, kimanin kilomita 11 daga garin Rann, da misalin karfe 11 na safe a ranar Litinin.
Mutanen da talauci ya yi wa katutu zai ƙaru a Nijeriya — Bankin Duniya NAJERIYA A YAU: Dalilin karyewar farashin shinkafa a kasuwannin NajeriyaTa ƙara da cewa an kai wasu da suka jikkata asibitin Rann domin kula da su.
Babu wata sanarwa a hukumance daga bangaren sojoji ko ’yan sanda game da faruwar lamarin.
Sai dai kuma, kokarin jin ta bakin kakakin rundunar ’yan sandan Jihar Borno, Kenneth Daso, bai yiwu ba saboda layin wayarsa ba ya shiga.