Nigeria: An Kashe Sojoji Da DAma A Wani Hari Da Aka Kai Wa Sansanonin Soja Biyu Hari A Jihar Borno
Published: 26th, March 2025 GMT
Kamfanin dillancin labarun “Reuters” ya nakalto cewa; An kai harinn ne wanda ya yi sanadiyyar mutuwa da kuma jikkatar wasu sojoji da dama a wasu sansanoni biyu dake Jihar Borno.
Mayakan kungiyoyin Boko Haram da Daesh suna kai wa fararen hula hare-hare a kasashen yammacin Afirka daga ciki har da Najeriya, inda suke kashe fararen hula da jami’an tsaro.
Majiyar ta kamfanin dillancin labarun “Reuters’ ta ce, kungiyoyin na “Da’esh’ da Boko Haram sun kai harin ne a yankin Wajiroko dake jihar borno, tare da cinna wuta a wurin da hakan ya yi sanadiyyar konewar kayan soja.
Wani soja ya bayyana cewa, a kalla 4 daga cikin sojoji ne su ka wanta dama sanadiyyar wannan harin, tare da jikkata wasu da dama daga cikinsu har da kwamanda.
Wasu madau dauke da makaman sun kai wani harin ne a garin Wolgu dake kan iyaka da kasar Kamaru, sai dai babu cikakken bayani akan yawan wadanda su ka kwanta dama ko su ka jikkata.
Wani daga cikin rundunar farar hula masu taimakawa sojoji a yaki da Bko haram din, mai suna Makinta Modu, ya fada wa manema labaru cewa, maharani sun kwace iko da sansanin sojan da su ka kai wa hari a Wajiroko.
Sai dai kuma an kawo dauki daga sojan sama da misalin karfi 10;30 na dare, da su ka yi nasarar kashe masu dauke da makaman da dama.. Sai dai babu cikakken bayani akan ko sojojin sun sake kwato sansanin nasu da ya shiga hannun ‘yan ta’adda.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Da Alamu Amurka Ta Fara Dandana Kudarta
Kamar yadda Sin da masana suka sha fada, mummunan matakin na Amurka, zai fi yi mata illa maimakon kasashen da take neman cin zalinsu.
Tabbas Sin ta yi gaskiya da ta ce bayar da kai ko ja da baya, dama ce ga mai cin zali. Don haka, Sin ta yi daidai da ta tsaya haikan wajen mayar da martani ba tare da bada kai ba, domin Amurka ta gane kuskurenta, kana ta fahimci cewa, lokaci ya wuce da za a rika biye mata tana yin abun da ta ga dama.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp