HausaTv:
2025-05-01@04:36:17 GMT

Amurka ta sake kai hare-hare Yemen

Published: 23rd, March 2025 GMT

Rahotanni daga Yemen na cewa sojojin Amurka sun kai hari a filin tashi da saukar jiragen sama na Hudayda a wani sabon hari kan kasar Yemen tun bayan da Washington ta sanar da kai munanan hare-hare kan kasar dake adawa da hare-haren da Isra’ila ke kai wa al’ummar Gaza.

Tashar talabijin ta al-Masirah ta kasar Yemen ta ce an kai hare-hare ta sama har sau uku a filin jirgin saman da ke gabar tekun Bahar Maliya a daren Asabar.

Kafafan yada labaran Yaman sun kuma bayar da rahoton cewa, an kai hari da jiragen yakin Amurka a tashar jiragen ruwa ta Salif da ke lardin Hudaidah.

Jiragen yakin Amurka sun kara kai hare-hare biyar a gundumar Majzar da ke lardin Ma’rib da ke tsakiyar kasar Yemen.

A wani labarin kuma a lardin Sa’ada dake arewa maso yammacin kasar, sojojin Amurka sun kaddamar da hare-hare ta sama a yankunan Sahar da Kitaf wa al-Boqe’e.

A ranar 15 ga watan Maris ma Amurka ta sanar da kai wani hari ta sama wanda jami’an Yemen suka ce ya kashe mutane 53.

Hare-haren, wanda shi ne na farko tun bayan da Shugaba Donald Trump ya koma kan karagar mulki, ya zo ne bayan da sojojin Yaman suka yi alkawarin sabunta ayyukansu na hana duk wata safarar jiragen ruwa na Isra’ila ko kuma wadanda ke da alaka da Tel Aviv, domin nuna goyan baya  ga al’ummar Falasdinu.

উৎস: HausaTv

এছাড়াও পড়ুন:

Karin Wata Kasa Da Bai San Ta Ba A Doron Duniya

Ba wannan ne karo na farko da shugaba Trump ya nuna girman kai da rashin sani game da Afirka ba. A watan da ya gabata, lokacin da yake bayani game da dalilin da ya sa gwamnatinsa ke rage gudummawar jin kai da take bayarwa a duniya, ya ce a baya, Amurka ta samar wa kasar Lesotho gudummawar dala miliyan 8, amma “ba wanda ya taba jin sunan wannan kasa”. Amma ita wannan kasar da ko sunanta shugaba Trump bai taba ji ba, ya sanya ta cikin jerin kasashen da ya sanar da zai kakaba musu haraji, har ma ya sanya mata haraji na kaso 50%. Idan ba mu manta ba kuma, a wa’adin shugabancinsa na farko, shugaba Trump ya taba bayyana kasashen Afirka a matsayin “shithole” a lokacin da ya tabo maganar bakin haure.

 

Sai dai ban da girman kai da rashin sani, kalaman shugaba Trump ya kuma bayyana matsayin da gwamnatin kasar Amurka ta dade tana dauka a game da kasashen Afirka, wato a maimakon abokan hadin gwiwa na zaman daidaito da martaba juna, tana kallonsu a matsayin abin da take iya amfani da su wajen takara da sauran manyan kasashe, kuma muna iya ganin haka ne daga manufofin da mahukuntan kasar suka dauka cikin ‘yan shekarun baya.

 

A shekarar 2014, gwamnatin Barack Obama ta shirya taron kolin Amurka da kasashen Afirka karo na farko, inda ta dauki alkawura a gaban kasashen Afirka. Sai dai bayan taron, a maimakon ta kara samar da gudummawa, sai ta rage, har da kudaden da take samarwa a fannin yaki da cutar kanjamau a Afirka. A gun taron, Amurka ta kuma yi alkawarin zurfafa huldarta da kasashen Afirka da ma gudanar da taron a kai a kai, amma ba a sake yin taron ba har sai bayan tsawon shekaru 8. A karshen shekarar 2022, Amurka ta gudanar da taron karo na biyu, inda tsohon shugaban kasar Joe Biden ya yi alkawarin samar da iya abin da kasarsa take iya bayarwa don tabbatar da kyautata makomar Afirka, kuma a cewarsa zai kai ziyara Afirka a shekarar 2023, amma bai cika wannan alkawari ba sai zuwa karshen bara, lokacin da ya kusan sauka daga kujerar shugabanci, kuma ba mu san yaushe za a cika sauran alkawuran da ya dauka ba.

 

Bayan da gwamnati mai ci ta fara aiki, jerin matakan da ta dauka sun haifar da munanan illoli ga kasashen Afirka. In mun dauki misali da harajin kwastam na ramuwar gayya da ta dauka a baya bayan nan, inda ta sanya haraji mai yawa kan kasashen Afirka 51, ciki har da 50% a kan Lesotho da 47% a kan Madagascar da 40% a kan Mauritius, matakin da ya kasance tamkar yi wa kasashen fashi. Abin lura kuma shi ne, harajin ya dakatar da dokar samar da ci gaba da damammaki a Afirka da aka san ta da AGOA, tun kafin wa’adinta ya cika, lamarin da ya jefa kasashen Afirka da dama cikin mawuyacin hali wajen yin ciniki da Amurka.

 

Har kullum kasar Sin na ganin cewa, Afirka dandali ne na hadin gwiwar kasa da kasa, a maimakon wajen yin takara tsakanin manyan kasashe. Rashin girmamawa ne ga kasashen Afirka da al’ummarsu yadda Amurka take da rashin sanin nahiyar, kuma rashin sahihancin da take wa hadin gwiwarta da kasashen Afirka ya shaida gazarwata ta daukar kasashen Afirka da muhimmanci. Kasashen Afirka na bukatar kawaye na gaske. Idan gwamnatin Trump tana son samun karbuwa daga kasashen Afirka, dole ne ta gyara matsayinta, kuma ya kamata ta fara da fahimtar kowace kasa da ke nahiyar. (Mai Zane: Mustapha Bulama)

 

 

 

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Kar A Mika Wuya Ga “Damisar Takarda”
  • Amurka ta sake laftawa wasu kamfaninin mai na Iran takunkumi
  • Katafaren Jirgin Daukar Jiragen Yaki Na Kasar Amurka Harry Truman Zai Fice Daga Tekun Maliya
  • Sabbin Bayanai Kan Fashe-Fashe Wasu Abubuwa A Tashar Jiragen Ruwan Kasar Iran
  • Karin Wata Kasa Da Bai San Ta Ba A Doron Duniya
  • Boko Haram Sun Hallaka ‘Yan Zaman Makoki 7, Sun Jikkata Wasu A Borno
  • Shugaban Putin Na Rasha Ya Bada Sanarwan Tsagaita Wuta Da Ukraine Na Sa’o’ii 72
  • Jagora Ya Bada Umurnin A Gudanar Bincike Mai Zurfi A Fashewar Tashar Jiragen Ruwa Na Shaheed Rajae
  • Jiragen Yakin Amurka Sun Kashe Mutane Da Dama A lardin Sa’ada Na Kasar Yemen
  • Lebanon:  Isra’ila Ta Kai Hari Akan Unguwar Dhahiya A Birnin Beirut