Dokar Ta-ɓaci: Fubara ya fice daga gidan gwamnatin Ribas
Published: 19th, March 2025 GMT
Gwamnan Jihar Ribas da aka dakatar, Similanayi Fubara, ya fice Fadar Gwamnatin Jihar da ke Fatakwal.
Majiyoyi sun shaida wa Aminiya cewa Fubara ya fice daga Fadar Gwamnatin da safiyar Laraba, a daidai lokacin da sabon Shugaban Riƙn Ƙwarya, Admiral Ekwe Ibas (mai ritaya), ke shirin karɓar ragamar mulki.
Wakilin Aminiya ya ziyarci Fadar Gwamnatin, inda ya lura cewa akwai kwanciyar hankali a yankin, inda aka girke motocin yaƙi guda uku a kofar shiga gidan gwamnatin.
Wani jami’in tsaro ya tabbatar da cewa an sauya dukkanin jami’an tsaron da ke aiki a Fadar Gwamnatin Jihar.
“Gwamna ya fice daga ciki, kuma muna jiran sabon shugaba ya iso. Komai na tafiya lafiya,” in ji shi.
A halin yanzu, al’ummar Fatakwal na ci gaba da harkokinsu yadda suka saba ba tare da wata matsala ba.
Shugaba Bola Tinubu ya ayyana dokar ta-ɓaci a Jihar Ribas a ranar Talata, sakamakon ikicin siyasa da ya dabaibaye jihar.
Sai dai matakin na Shugaban Ƙasa, ya bar baya da ƙura inda mutane ke tofa albarkacin bakinsu kan lamarin.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Dokar Ta Ɓaci Fubara rikicin siyasa Fadar Gwamnatin
এছাড়াও পড়ুন:
Remi Tinubu ta ba da tallafin Naira biliyan ɗaya ga waɗanda harin Benuwe ya shafa
Uwargidan Shugaban Nijeriya, Sanata Remi Tinubu ta bayar da tallafin naira biliyan daya ga wadanda harin nan ya rutsa da su a yankin Yelwata na Ƙaramar Hukumar Guma a Jihar Benuwe.
Sanata Tinubu wadda ta miƙa cakin kuɗin ga Gwamna Hyacinth Alia ta sanar da bayar da tallafin ne a jawabinta na jaje wanda ta kai Fadar Gwamnatin Benuwe da ke Makurdi.
Gwamnatin Zamfara ta amince da naɗin sabon Sarkin Katsinan Gusau Ambaliya ta yi ajalin mutum 30 a ChinaUwargidan shugaban ƙasar ta buƙaci a yi amfani da wannan tallafin a matsayin gudunmawar farfaɗo da yankin da waɗanda suka tsallake rijiya da baya a yayin harin musamman yaran da yanzu ke buƙatar komawa makarantu.
Ana iya tuna cewa, tun a daren ranar 13 ga watan Yuni zuwa wayewar gari 14 ga watan ne aka kashe fiye da mutum 100 a ƙauyen Yelwata, lamarin da ya janyo Allah wadai daga sassa daban-daban a faɗin ƙasar.
Jihar Benuwe dai na daga cikin jihohin da ke fuskantar matsalar tsaro a Nijeriya, musamman rikicin manoma da makiyaya da kuma na ƙabilanci, wanda ke sanadiyyar salwantar rayuka da dama.