An Bukaci Jama’a Su Rika Binciken Lafiyarsu Don Kare Kai Daga Cutar Koda
Published: 13th, March 2025 GMT
Babban Rajistara na Sashen kula da lafiyar Koda a Asibitin Koyarwa na Tarayya da ke Gombe (FTHG), Dr. Fidelis Linga, ya yi kira ga jama’a da su kula da lafiyarsu domin kaucewa kamuwa da cututtukan koda.
Ya bayyana hakan ga manema labarai a Gombe yayin bikin Ranar Koda ta Duniya.
Dr. Fidelis Linga ya jaddada cewa wasu munanan dabi’u kamar shan barasa, da taba, da cin abinci mara kyau, da zama babu motsa jiki na daga cikin dalilan da ke haddasa karuwar cututtukan da suka shafi Koda.
Ya yi nuni da mahimmancin yin gwaje-gwaje a asibiti akai-akai, da cin abinci mai kyau, da motsa jiki domin hana cutar koda.
Ya bayyana cewa, a duniya gaba ɗaya, mutane miliyan 850 na fama da cututtukan Koda, kuma daga cikinsu, mutane miliyan 11 ke mutuwa kowace shekara. Ya bayyana wannan matsala a matsayin abin damuwa.
Dr. Fidelis Linga ya ce Asibitin FTH Gombe na kokarin samar da karin na’urorin wanke koda da kuma ƙarin ma’aikatan lafiya domin kula da yawan marasa lafiya da ke zuwa asibitin don wanke Koda.
Ya ce wannan yunƙuri na da nufin inganta samun damar wanke Koda ga marasa lafiya da ke fama da cututtukan koda.
HUDU SHEHU
উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa
কীওয়ার্ড: Cutar Koda
এছাড়াও পড়ুন:
Gwamna Namadi Ya Taya Malaman Makarantu Da Suka Yi Fice A Jihar Murna
Gwamnan Jihar Jigawa, Malam Umar Namadi, ya yabawa Hukumar Makarantun Kimiyya da Fasaha ta Jiha bisa ƙirƙirar Kyautar Malami Mafi Nagarta, yana mai bayyana hakan da ɗaya daga cikin manyan manufofin da za su ƙarfafa koyo da koyarwa a fadin jihar.
A cikin wata sanarwa da Babban Jami’in Yaɗa Labaran sa, Hamisu Mohammed Gumel, ya fitar, gwamnan ya bayyana cewa bikin na farko na bada lambar yabo da aka gudanar a Dutse ya dace domin girmama malamai da suka yi fice ta hanyar jajircewa da sadaukar da kai.
Ya ƙara da cewa wannan mataki zai ƙara kwarin gwiwa, ya samar da gasa mai kyau, tare da inganta darussa a makarantu.
Namadi ya jaddada cewa ingancin ilimi bai tsaya kan gina makarantu kawai ba, yana ta’allaka ne ga ingancin malamai, kayan koyarwa da kuma yanayin makarantu.
Ya bayyana cewa gwamnatinsa ta fara ɗaukar malamai tare da horas da su akai-akai domin rage cunkoson ɗalibai da malamai da kuma horar da su sabbin dabarun koyarwa.
“Wannan shiri ɗaya ne daga cikin mafi kyawu da muka gani. Idan wani ya yi kuskure, sai a hukunta shi, yayin da duk wanda ya yi fice, wajibi ne a yaba masa. Wannan shi ne yadda ake samun cigaba,” in ji gwamnan.
Ya bukaci sauran hukumomin ilimi kamar Hukumar Gudanar da Makarantun Sakandare, Hukumar Ilimin Addinin Musulunci, da Ma’aikatar Ilimin Firamare su yi koyi da wannan tsari domin ƙara ƙarfafa gwanintar malamai a dukkan matakai.
Gwamnan ya kuma sake jaddada cewa gwamnatinsa za ta ci gaba da maida hankali wajen gina makarantu, horar da malamai, da walwalar su.
Ya tabbatar da cewa za a ci gaba da baiwa bangaren ilimi goyon baya don inganta sakamakon koyo a makarantu a fadin Jihar Jigawa.
Usman Muhammad Zaria