Ina yi wa ‘yan’uwana da abokan arzki barka da juma’a da kuma barka da azumi Allah ya karbi ibadunmu kamar su; Badi’a, Habiba, Zulaihat, Nuwaira, Rashida, Munir, Habib, Farhan, Yasmin da dai sauransu, asha ruwa lafiya.
Sako daga Sakeena Tijjani Ahmad Jihar Jigawa:
Ina gaida Kawu sambo, Adda Atine, Yakumbo Ummi, Junaidiyya, Adda Nafi, Adda Jamila, Fatima, Adda Hadiza, Nurain, Fatima Danjuma, Jamila Sa’id, Fiddausi Habib, Zeenat, Fauziyya, Mahmah, Sajida, Kawu Yakubu, Meenah, da fatan sun yi juma’a lafiyya kuma da fatan za su sha ruwa lafiya.
Sako daga Haydar Salisu Jihar Bauchi
Ina gaida yayana Yusuf, Dawud, Bello, Marwan, da, Ummana da Abbana da kuma abokaina Muhammad, Usman, Salisu, da Aisha da fatan sun yi juma’a lafiya.
Sako daga Shukra Ibrahim Jihar Sokoto:
Ina gaida Babana Alh. Ibrahim Mai Turare da Mamana Haj. Bilkisu, sai Rahma, Khadija, Amina, Yahanasu, Saudat, ina fatan za su yi juma’a lafiya.
Sako daga Meerah’s Kitchen:*
Ina gaida Mum da Dad dina sai sisters dina da brothers dina, abokaina da kawaye na, Meenah, Yesmin, Labiba, Abidah, Asma’u(Husna), Ahmad, Umar, Haydar da Zakiyya, sai colleagues dina; Zee-Zee, Princess Aisha, Rahma’s Delight, Grace, Promise, Charity, Gift, Faith, Peace, Unity, Aisha (first daughter), Beauty, Bily, Zunairah, Glory, Fati Seemah, Maryam Sha’aban, Nafisa (Ifan Beauty), Yusra, Fatima Auta, Jidda (Arsu), Nadiya, da dai sauransu da fatan za a sha ruwa lafiya.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppএছাড়াও পড়ুন:
Karamar Hukumar Malam Madori Ta Horar Da Mata Kare Kai Daga Cututtukan Mahaifa
A ƙoƙarinta na ƙara wayar da kan jama’a game da harkokin lafiya a birane da karkara na Malam Madori, majalisar ƙaramar hukumar ta horar da mata da ‘yan mata 50 kan tsafta a lokutan al’ada domin kare kansu daga cututtukan mahaifa.
Jami’in shirin, Malam Ali Haruna, ya ce an zaɓi mahalarta horon ne daga kowace gunduma ta yankin
A cewarsa, manufar horon ita ce koyar da mahalarta yadda za su samar da kariya yayin al’ada da kansu domin rage kashe kuɗi da kuma kare kansu daga kamuwa da cututtukan mahaifa.
Shi ma shugaban sashen ruwa da tsafta, Malam Shehu Sani Gwadayi, ya bayyana cewa tsafta na da matuƙar muhimmanci ga rayuwar ɗan adam domin inganta rayuwa da ƙarfafa garkuwar jiki.
A nasa jawabin, mataimakin shugaban sashen ruwa da tsafta, Malam Muhammad Abdullahi, ya yi wa mahalarta horon bayani kan muhimmancin tsafta yayin al’ada domin gujewa kamuwa da cututtuka.
Shugaban ƙaramar hukumar Malam Madori, Alhaji Salisu Sani Garun Gabas, ya shawarci mahalarta da su mai da hankali ga sashen aikace-aikace na yadda ake sarrafa audugar mata a gida yayin horon.
Usman Muhammad Zaria