Wani mutum wanda aka bayyana a matsayin Abdulrashid Usman, ya yanke jiki ya mutu a yayin da yake buɗa-baki a yankin Babban Birnin Tarayya.
Wani shaida mai suna Suleiman Bala, ya ce lamarin ya faru ne a ranar Asabar da aka ɗauki azumi, lokacin da mamacin da abokansa suke buɗe-baki a majalisarsu da ke yankin Kutunu a Ƙaramar Hukumar Gwagwalada.
Ya ce Usman da abokansa suna zaune a kan benci suna cin ’ya’yan itatuwa ne ya yanke jiki ya faɗi, rai ya yi halinsa.
Nan take abokan suka garzaya da shi zuwa asibiti, inda likita ya tabbatar cewa rai ya yi halinsa.
A cewarsa, marigayin, wanda yake cikin koshin lafiya, ya dawo daga Kaduna ganin buɗa-baki, daga nan ya je majalisarsu ya haɗu da abokansa, bayan an sha ruwa suna tsaka da buɗa-baki lamarin ya faru.
“Wani ɗan uwan marigayin ya ce mamacin ya dawo daga Kaduna kuma ya je shiga cikin abokansa inda suke annashuwa.
“Bayan kiran Sallah suna buɗa-baki lamarin ya faru,” in ji shaidar.
Ya ce an binne shi bisa tsarin addinin Musulunci.
উৎস: Aminiya
এছাড়াও পড়ুন:
Nijeriya Na Ke Yi Wa Biyayya Ba Wani Ko Jam’iyya Ba – El-Rufai
“Lokacin da abubuwa suka fara lalacewa a lokacin shugaba Buhari, na fito na faɗi gaskiya. Lokacin da tsarin sauya fasalin Naira ya jefa jama’a cikin wahala, na ƙalubalanci gwamnati duk da cewa jam’iyyar APC ce ke kan mulki. Na fi biyayya ga Nijeriya fiye da kowane mutum,” in ji shi.
El-Rufai ya ƙaryata jita-jitar cewa fushinsa da gwamnatin Shugaba Tinubu ne ya sa ya fice daga APC.
Ya ce yana da shekaru 65, kuma babu wani abu da ya rage masa a siyasa da zai nema, sai dai kawai yana jin cewa matsalolin Nijeriya sun yi tsanani sosai wanda ba zai zauna ya yu shiru ba.
“Zan iya yin ritaya cikin kwanciyar hankali, amma Nijeriya na fuskantar babbar barazana. Wannan ba don kaina ba ne – don ceton ƙasa ne,” in ji shi.
Ya kuma bayyana cewa dole a zaɓi shugaban ƙasa mai nagarta da hangen nesa, ba wai kawai din ya fito daga wata jiha ba.
“Matsalolin da muke fuskanta sun fi girman la’akari da inda mutum ya fito. Muna buƙatar shugabanni masu hangen nesa da ƙwarewa don gyara Nijeriya,” ya bayyana.
Da yake magana kan sauya sheƙar wasu ‘yan siyasa zuwa APC, El-Rufai ya ce jam’iyyar SDP tana mayar da hankali ne kan gina goyon baya daga jama’a, ba wai kawai neman manyan ‘yan siyasa ba.
“Gwamna ɗaya yana da ƙuri’a ɗaya ne kawai. Jama’a ne ke yin zaɓe, ba manyan ‘yan siyasa ba,” ya jaddada.
A ƙarshe, El-Rufai ya ce tafiyar SDP tana ci gaba da karɓuwa a dukkanin sassan Nijeriya, ba a yankuna kaɗan kaɗai ba.
“Muna ci gaba da gina goyon baya a faɗin ƙasar nan. Aikin gina ƙasa yana faruwa ne a tsakanin talakawa, ba kawai a kafafen yaɗa labarai ba,” in ji shi.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp