Gwamna Namadi Ya Kaddamar Da Shirin Noman Rani Na Zamani A Karamar Hukumar Maigatari
Published: 3rd, March 2025 GMT
Gwamna Umar Namadi ya kaddamar da shirin noman rani ta hanyar amfani da rijiyoyin burtsatse a karamar hukumar Maigatari.
Hakan wani muhimmin mataki ne na samar da abinci da zamanantar da noma a jihar Jigawa.
A cikin wata sanarwa da babban sakataren yada labarai na gwamnan Hamisu Mohammed Gumel ya rabawa gidan rediyon Najeriya ya ce, gwamnan ya bayyana cewa, aikin da ake amfani da shi ta hanyar amfani da hasken rana da kuma amfani da dabarun noman rani, yana yana taimakawa wajen yin noma a kowane lokaci na shekara tare da bunkasa tattalin arzikin manoma.
A cewarsa, shirin mai fadin hekta 10 wanda aka samar da rijiyoyin burtsatse na zamani guda hudu do tallafa wa kananan manoma 80 kai tsaye, zai habbaka noman abinci tare da inganta rayuwar al’umma.
Gwamna Umar Namadi ya jaddada kudirin gwamnatinsa na aiwatar da manufofinta guda 12, inda ya jaddada fadada ayyukan ban ruwa da suka hada da madatsun ruwa da rijiyoyin burtsatse.
Ya ce nan ba da jimawa ba za a kammala irin wadannan ayyuka a kananan hukumomin Birniwa da Kafin Hausa.
Namadi ya ce kasafin kudi na 2025 ya hada da kara ayyukan noman noman rani a Gumel, da Sule Tankarkar, da Gagarawa.
Ya kuma bayyana irin rawar da shirin ke takawa wajen rage dogaro da nomar damina kadai, tare da inganta ayyukan noma, da samar da karin kudaden shiga ga manoma.
Usman Muhammad Zaria
উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa
কীওয়ার্ড: Jigawa Noman Rani
এছাড়াও পড়ুন:
Gwamnatin Jihar Kano Ta Kaddamar da Manufar Sauyin Yanayi
Gwamnatin jihar Kano tare da hadin gwiwar wata kungiya mai suna Partnership for Agile Governance and Climate Change (PACE) ta kaddamar da manufofinta na sauyin yanayi a hukumance. Wannan manufa mai mahimmanci ta samar da taswirar dabaru don ragewa, daidaitawa, da tsarin tafiyar da yanayi mai hadewa a duk sassan ci gaba a jihar.
Da yake jawabi a wajen taron kaddamar da taron wanda aka gudanar a dakin taro na Armani Event Centre dake Kano, Gwamna Abba Yusuf wanda sakataren gwamnatin jihar Ibrahim Farouk ya wakilta, ya bayyana taron a matsayin wani babban ci gaba a kokarin gwamnatinsa na mayar da jihar Kano a matsayin mai ci gaba a harkokin tafiyar da yanayi da muhalli.
Gwamna Yusuf ya jadadda cewa, manufar tana cike da shirin aiwatar da sauyin yanayi, wanda ke fassara kudirin siyasar gwamnati zuwa tsarin aiwatarwa a aikace.
Ya kuma yi tsokaci kan shirye-shiryen da gwamnati ke yi na samar da makamashi ta hasken rana da ababen more rayuwa.
Gwamnan ya nanata shirin gwamnatin sa na dasa itatuwa miliyan 5 a shekarar 2025 domin rage zaizaiyar kasa, da inganta iskan shaka, da inganta kyawawan birane.
ABDULLAHI JALALUDDEEN KANO