Saliyo Ta Kaddamar Da Cibiyar Likitancin Gargajiya Na Sin Ta Farko
Published: 2nd, March 2025 GMT
An kaddamar da cibiyar likitancin gargajiya na Sin ta farko, ranar Juma’a a Freetown, babban birnin kasar Saliyo, wadda ta zama muhimmin mataki a yunkurin kasar na amfani da likitancin gargajiya na Sin domin amfanawa al’umma.
Kadammar da cibiyar ta biyo bayan kammala wani aikin binciken kiwon lafiyar al’umma a kasar wanda likitocin kasar Sin suka jagoranta, wanda ke da nufin tallafawa kasar inganta matakan kariya da maganin cututtuka gama gari kamar hawan jinni da ciwo mai tsanin.
Da yake gabatar da jawabi yayin bikin kaddamar da cibiyar, mataimakin ministan lafiya na kasar Saliyo Charles Senessie, ya yabawa dangantaka mai karfi dake tsakanin Sin da Saliyo a bangaren kiwon lafiya, musammam wajen amfani da likitancin gargajiya na Sin. Ya ce Saliyo ta samu nasarori wajen hada likitancin gargajiya na Sin da tsarin kiwon lafiya na kasar. (Mai fassara: Fa’iza Mustapha)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppকীওয়ার্ড: likitancin gargajiya na Sin
এছাড়াও পড়ুন:
Sin Ta Dade Tana Aiki Tukuru Kan Kiyaye Zaman Lafiya Da Kwanciyar Hankali Na Yanki
Dangane da tattaunawar tattalin arziki da cinikayya tsakanin Sin da Amurka da aka gudanar a kwanan nan, Guo Jiakun ya bayyana cewa, ana fatan bangaren Amurka zai yi aiki tare da Sin wajen amfani da tsarin tattaunawa kan tattalin arziki da cinikayya tsakanin kasashen biyu, don sa kaimi ga bunkasa dangantakar dake tsakanin Sin da Amurka cikin kwanciyar hankali.
Dangane da batun Falasdinu kuwa, Guo Jiakun ya ce, “manufar kafa kasashe biyu” ita ce hanya daya tilo ta hakika ta warware matsalar Falasdinu, kuma kasar Sin tana goyon bayan al’ummar Falasdinu wajen kafa kasa mai cin gashin kanta.(Safiyah Ma)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp