An Nada Tsoffin Shugabannin Najeriya, Kenya, Da Ethiopia Domin Shiga Tsakani A Rikicin Congo
Published: 26th, February 2025 GMT
A kokarin da ake yin a shawo kan rikicin kasar Jamhuriya imukradiyyar Congo, an nada wasu daga cikin tsoffin shugabannin kasashen Afirka a matsayin masu shiga tsakani domin warware rikicin da yaki ci yaki cinyewa tsakanin ’yan tawayen M23 da gwamnatin Dimokuraɗiyyar Congo.
Hakan kuwa yana zuwa ne bayan da Kungiyoyin raya kasashen gabashi (EAC) da kudancin nahiyar Afirka (SADC) suka yanke shawarar daukar wanan mataki, inda suka nada tsoffin shugabannin Habasha da Kenya da Nijeriya domin sanya idanu a kan batun sulhu a Jamhuriyyar Dimokuradiyyar Congo wanda kullum yake kara ta’azzara, duk kuwa da yarjeniyoyin suhu da dama da aka rattabawa hannu.
Wadannan kungiyoyin EAc da SADC sun nada tsohon shugaban Kenya, Uhuru Kenyatta da tsohon Firai Ministan Habasha, Hailemariam Desalegn da kuma tsohon shugaban Nijeriya Olusegun Obasanjo domin ganin sun taimaka saboda tabbatar da sabuwar yarjejeniyar da kuma yin aiki da ita.
Bangarori na kasa da kasa da suka hada da Majalisar Dinkin Duniya da kuma ita kanta Tarayyar Afirka, sun dauki tsawon shekaru suna fadi tashin ganin sun kawo kan wannan matsala ta Congo, amma lamarin ya ci tura.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Za A Yi Allurar Rigakafi Ga Dabbobi Sama Da Miliyan Daya A Babura
Dabbobi sama da miliyan guda ne ake sa ran za a yi wa rigakafi a fadin karamar hukumar Babura da ke jihar Jigawa.
Shugaban karamar hukumar Babura, Alhaji Hamisu Muhammad Garu, ne ya bayyana hakan yayin kaddamar da aikin rigakafin dabbobi na bana.
A cewarsa, fiye da tumaki da awaki miliyan daya da shanu dubu ashirin ake sa ran za a yi wa rigakafi a fadin karamar hukumar.
Ya jaddada cewa karamar hukumar na da cikakken shiri da kudurin tallafawa sauyin noma na Gwamna Umar Namadi, domin inganta rayuwa da tattalin arzikin al’ummar jihar.
Shugaban ya jaddada muhimmancin masu kiwon dabbobi su bada hadin kai yayin aikin rigakafin domin tabbatar da lafiyar dabbobinsu.
Alhaji Hamisu Garu ya kuma nuna jin dadinsa game da zaman lafiya tsakanin manoma da makiyaya a yankin, yana mai kira gare su da su ci gaba da gudanar da rayuwa cikin fahimta da hadin kai.
Haka zalika, yayin taron, Shugaban Sashen Noma da Albarkatun Kasa, Malam Lawan Sabo Kaugama, ya bayyana cewa an ware cibiyoyi guda goma sha biyu domin gudanar da aikin rigakafin wanda ake sa ran zai dauki kwanaki hudu.
Ya yaba da kokarin gwamnatin jiha da ta karamar hukuma wajen samar da allurar rrigakafn da kuma duk wasu kayan aiki da ake bukata.
Usman Muhammad Zaria