An Gudanar Da Taron Dandalin Ciniki Tsakanin Sin Da Habasha A Addis Ababa
Published: 26th, February 2025 GMT
An gudanar da taron dandalin ciniki tsakanin Sin da Habasha kana taron sa kaimi ga dandalin baje kolin tsarin samar da kayayyaki na kasa da kasa wato CISCE karo na 3 a jiya Litinin a Addis Ababa, hedkwatar kasar Habasha.
Kwamitin sa kaimi ga cinikin Sin da ketare da kwamiti mai kula da harkar zuba jari na Habasha da kungiyar kasuwanci da kungiyar sana’o’in Habasha sun gudanar da taro mai taken “Shiga Habasha: Habaka hadin gwiwar tsarin samar da kayayyaki tsakanin Sin da Afirka” cikin hadin kai.
Jakadan Sin dake Habasha Chen Hai ya gabatar da wani jawabi, inda ya ce, dandalin CISCE irinsa na farko a duniya dake mai da hankali kan tsarin samar da kayayyaki a duniya, zai samar da wani muhimmin dandali ga mabambantan kamfanonin kasashen duniya wajen habaka kasuwaninsu a ketare da jawo jari daga waje da mu’amalar kimiyya da daga kimar kasashensu da dai sauransu.
Darektan kwamiti mai kula da zuba jari na Habasha Zeleke Temesgen ya ce, a halin yanzu, Sin ta zama daya daga cikin abokai mafi karfi a bangaren ciniki da zuba jari ga Habasha. Yana fatan ’yan kasuwan kasar Sin za su nazarci babbar damar zuba jari a kasarsa, da kafa huldar abokantaka mai karfi da dorewa tsakaninsu, a cewarsa. Yana mai fatan shigowar Sin wannan bangare zai gaggauta bunkasa tattalin arzikin kasar, har ma da samar da karin guraben aikin yi da ingiza samun wadata cikin hadin gwiwa baki daya. (Amina Xu)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppএছাড়াও পড়ুন:
An Fara Baje Kolin Kayakin Da Ake Kerawa A Iran Tare Da Taron Iran Da Afirka Karo Na Uku
An fara kasuwar baje koli na kayakin kasuwancin da ake samarwa a cikin Iran ko IRAN EXPO 2025, karo na 3 a nan Tehran.
Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya bayyana cewa kasuwar baje koli na Iran EXPO 2025 zai jawa masu zuna jari daga kasashen Afirka.
Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Aragchi ya fadawa kamfanin dillancin labaran IP kan cewa Kasuwar ta bana dai, za ta tara kamfanonin masu samar da kayaki daga yankuna daban daban na kasar Iran da dama, kuma akwai fatan cewa wannan kasuwar ta zama mabudi ga kyautatuwan tattalin arzikin kasar.
EXPO dai ita ce kasuwar baje koli na kayakin kasar Iran mafi girma wanda ake gudanarwa a ko wace shekara, sannan daga nan take samun kasuwa a kasashen duniya. Kuma yan kasuwa daga kasahe fiya da 100 ne suka shigo kasar don halattan kasuwar.
Esma’il Bakaee, kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran ya ce ya na fatan a wannan kasuwar, kasashen Afirka da Iran za su amfani juna a harkokin kasuwancin da ake bunkasa a tsakaninsu.