Tattalin arzikin Nijeriya ya haɓaka da kashi 3.84 — NBS
Published: 25th, February 2025 GMT
Hukumar Ƙididdiga ta Nijeriya NBS ta ce tattalin arzikin ƙasar ya haɓaka da kaso 3.84 cikin 100 a zango na 4 na shekarar 2024.
A cewar rahoton da hukumar NBS ta fitar a yau Talata, bunƙasar ta ɗara kaso 3.46 da aka samu a zango na 3 na 2024.
An naɗa Obasanjo mai shiga tsakani a rikicin Kongo Manoman tumatir na tafka asara saboda faɗuwar farashiAlƙaluman game da zango na 4 na shekarar 2024 sun kuma ɗara kaso 3.
“Ɓangaren ayyuka ne kan gaba a bunƙasar ta zango na 4 na 2024, wanda ya ƙaru da kaso 5.37 cikin 100 tare da ba da gudunmawar kaso 57.38 cikin 100 na jimillar tattalin arzikin,” a cewar NBS.
A jimillar ƙididdigar shekarar ta 2024, tattalin arzikin Nijeriya ya haɓaka ne da kashi 3.40 idan aka kwatanta da kashi 2.74 a 2023.
Sai dai duk da haka, haɓakar ba ta cimma alƙawarin da Shugaba Bola Tinubu ya ɗauka na haɓaka tattalin arziƙin ƙasar da kashi 6 ba a shekarar ta 2024.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Nijeriya Tattalin Arziki tattalin arzikin
এছাড়াও পড়ুন:
Tinubu ya bai wa ’yan ƙwallon Nijeriya mata kyautar kuɗi da gida da lambar yabo
Shugaba Bola Tinubu ya karrama ’yan wasan tawagar ƙwallon ƙafa ta mata ta Nijeriya da lambar yabo ta OON.
Shugaban ya bai kowacce ’yar wasa a tawagar ta Super Falcons kyautar gida mai ɗakuna 3 a rukunin gidaje na Renewed Hope da kuɗi dala dubu 100.
Haka kuma, shugaban ya kuma bai wa masu horas da tawagar kyautar dala dubu 50.