Aminiya:
2025-06-18@03:04:00 GMT

NAJERIYA A YAU: Azumin Ramadana: Ko Kun San Dabinon Da Kuke Shan Ruwa Da Shi?

Published: 25th, February 2025 GMT

More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba

Ko kun san sunan dabinon da kuka fi so ku ci a lokacin shan ruwa?

Dan Agadas ne, ko Ruwa-Ruwa, ko Annakhiyl?

NAJERIYA A YAU: Matakan Kariya Daga Cutar Ƙyandar Biri DAGA LARABA: Dalilan Da ’Yan Najeriya Ke Haɗa Buga-Buga Da Aikin Albashi

A yayin da ake shirye-shiryen tarbar watan Ramadana, shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci zai yi nazari ne kan nau’ukan dabino da alfanunsa ga dan Adam, musamman mai azumi.

Domin sauke shirin, latsa nan

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: Azumin Ramadan Watan Azumin Ramadan

এছাড়াও পড়ুন:

Takarar Tinubu: Rikici ya ɓarke a APC bayan Ganduje ya ƙi goyon bayan Shettima

An samu saɓani a wani taron shugabannin jam’iyyar APC a yankin Arewa Maso Gabas da aka gudanar a Jihar Gombe.

Rikicin ya fara ne bayan da Kwamared Mustapha Salihu, Mataimakin Shugaban APC na ƙasa mai kula da Arewa Maso Gabas, ya bayyana goyon bayansa ga takarar Shugaba Bola Tinubu don ya sake tsayawa takara a karo na biyu.

Yadda wani ɗan sanda ya rasu a hanyar zuwa ɗaurin aurensa HOTUNA: Yadda aka yi sulhu da ƙasurgumin ɗan fashin daji Ado Aliero a Katsina

Sai dai bai ambaci mataimakin shugaban ƙasa Kashim Shettima ba.

Manyan jiga-jigan jam’iyyar APC daga yankin sun halarci taron, ciki har da gwamnoni, ministoci, da ‘yan majalisa.

Shugaban jam’iyyar APC na ƙasa, Abdullahi Ganduje, shi ma ya halarci taron.

Bayan Salihu ya gama jawabi, wasu daga cikin mahalarta taron sun fusata.

Take suka fara yi masa ihu, wasu ma suna barazanar kai masa hari.

Sai jami’an tsaro sun fito da shi daga ɗakin taron don kare lafiyarsa.

Don kwantar da rikicin da ya taso, Mataimakin Shugaban jam’iyyar na ƙasa, Bukar Dalori, ya fito ya bayyana goyon baya ga Tinubu da kuma Shettima don su ci gaba da mulki.

Amma lamarin ya ƙara dagulewa bayan da Ganduje ya yi jawabi, inda ya ayyana goyon bayansa ga Tinubu kaɗai, ba tare da ya ambaci Shettima ba.

A yayin jawabin da ya yi na kusan minti 10, bai ambaci sunan Shettima ba.

Shi ma sai da jami’an tsaro suka fita da shi daga wajen taron saboda gudun rikicin da zai je ya dawo.

Shettima dai ɗan Jihar Borno ne, ɗaya daga cikin jihohin yankin Arewa Maso Gabas.

Mutane da dama sun ji ba ɗadi kan rashin ambaton sunan a wajen taro da aka yi a yankinsa.

Taron ya kare cikin gaggawa saboda tashin hankali.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Majalisar Wakilai Ta Fara Binciken Yadda Aka Raba Naira Tiriliyan 1.12 Kan Shirin Lamuni Ga Manoma Da Masana’antu
  • Sabon Shirin Gwamnatin Katsina: Za A Fara Sauya Tunanin Tubabbun ‘Yan Bindiga
  • NAJERIYA A YAU: Yadda Cin Ganyayyaki Ke Yi Wa ‘Yan Najeriya Wahala
  • Atalanta Na Neman Yuro Miliyan 50 Daga Duk Kungiyar Da Ke Son Daukar Lookman
  • NAJERIYA A YAU: Dalilan Durƙushewar Sababbin Sana’o’i Tun Ba A Je Ko’ina Ba
  • Rundunar Sojin Ruwa Ta Nijeriya Ta Lalata Haramtattun Matatun Mai 5 A Ribas
  • Iran ta kai sabbin hare-hare birnin Tel Aviv da Haifa
  • Takarar Tinubu: Rikici ya ɓarke a APC bayan Ganduje ya ƙi goyon bayan Shettima
  • NAF Na Shirin Siyo Jiragen Yaki Masu Saukar Ungulu Daga Amurka
  • ‘Yan Wasa Biyar Da Suka Taka Rawar Gani A Kofin Zakarun Turai