Hajj 2025: NAHCON Ta Rage N54bn Daga Kudaden Cajin Maniyyata
Published: 24th, February 2025 GMT
Hukumar Alhazai ta Ƙasa (NAHCON) ta sanar da tsawaita lokacin yin rajistar maniyyata zuwa Hajjin 2025 a Ƙasar Saudiyya har bayan Azumin Ramadan.
Shugaban Hukumar, Farfesa Abdullahi Sale Usman, ya bayyana hakan a wata hira da aka yi da shi a Abuja.
Farfesa Usman ya kuma bayyana cewa an rage naira biliyan 54 daga kudaden da masu ruwa da tsaki ke caji domin saukaka wa maniyyata wajen biyan kuɗin tafiya.
Ya tabbatar da cewa ana duba sabbin hanyoyin inganta muhimman ayyuka kamar abinci, masauki, da kula da lafiyar alhazai yayin da suke ƙasa mai tsarki.
A cewarsa, hukumar za ta ɗauki nauyin kuɗin tafiyar ƙwararrun masu dafa abinci 60 da za su sa ido kan shirye-shiryen abinci a wuraren da aka tanada, sakamakon korafe-korafen matsaloli da aka fuskanta a shekarar da ta gabata.
উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa
কীওয়ার্ড: Maniyyata Ragewa Tsawaita Rajistar
এছাড়াও পড়ুন:
Kwamitin Aikin Hajjin 2025 Na Jihar Kano Ya Kammala Rahoton Aikinsa Na Wucin Gadi
Kwamitin Aikin Hajjin 2025 Na Jihar Kano ƙarƙashin jagorancin Sarkin Karaye, Mai Martaba Alhaji Muhammad Mahraz Karaye, ya kammala rahoton aikinsa na wucin gadi.
Darakta Janar na Hukumar, Alhaji Lamin Rabi’u Danbappa, ne ya bayyana hakan a fadar Sarkin da ke Karaye.
Ya ce rahoton ya ƙunshi dukkan abubuwan da suka shafi aikin Hajji tun daga lokacin da aka ƙaddamar da kwamitin a birnin Makkah, ƙarƙashin jagorancin Gwamnan Jihar Kano, Mai Girma Alhaji Abba Kabir Yusuf.
“Rahoton ya kunshi cikakken bayani kan ayyukan da kwamitin ya gudanar zuwa yanzu, kuma zai kasance muhimmin ɓangare na rahoton ƙarshe da za a miƙa ga Gwamna,” In ji shi.
Alhaji Lamin Rabi’u ya bayyana cewa Hukumar Jin Daɗin Alhazai ta Jihar Kano ta rigaya ta tattara nata cikakken rahoton, wanda za a mika wa Gwamnan nan ba da daɗewa ba.
A nasa jawabin, Sarkin Karaye ya nuna godiya ƙwarai ga Gwamnan Jihar bisa amincewa da baiwa kwamitin damar gudanar da wannan aiki mai muhimmanci.
Shugaban Hukumar gudanarwa na hukumar Alhaji Yusif Lawan, ya bayyana godiya ga Sarkin Karaye bisa sadaukarwa da haɗin kai da ya bayar, wanda ya taimaka wajen samun nasarar aikin kwamitin.
Abdullahi Jalaluddeen