Wani mutum ya yi wa agolarsa fyaɗe ta samu juna biyu
Published: 22nd, February 2025 GMT
Rundunar ’yan sandan Jihar Legas ta cafke wani mutum mai shekaru 28, Samuel Alfred bisa zargin yi wa wata agolarsa fyaɗe har ta samu juna biyu.
An cafke mutumin ne tare da wani abokinsa, Ikechukwu Obi mai shekaru 30 kan zargin wannan aika-aikar.
An haifi alade mai fuskar mutum a Philippines Ko Real Madrid za ta iya lashe Gasar Zakarun Turai bana?Bayanai sun ce ababen zargin sun kai budurwar mai shekaru 14 wani ɗaki da ke yankin Ojo na jihar ta Legas inda suka raba ta da budurcinta.
Mai magana da yawun rundunar, Benjamin Hundeyin, ya tabbatar da faruwar lamarin wanda ya ce mahaifiyar yarinyar mai suna Deborah ce ta kai ƙorafi ofishinsu da ke Okokomaiko.
Hundeyin ya ce za a gurfanar da ababen zargin biyu a gaban kuliya domin su girbi abin da suka shuka.
“A halin yanzu yarinyar tana ɗauke da ciki da har ya kai watanni tara kuma za a miƙa lamarin zuwa kotu,” in ji Hundeyin.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: fyaɗe Jihar Legas
এছাড়াও পড়ুন:
‘An Kashe Masu Zanga-zanga Akalla 500 a Tanzania’
Jami’an diflomasiyya a Tanzania sun ce akwai kwararan hujjoji da ke tabbatar da an kashe akalla mutum 500 a cikin kwana biyu da barkewar zanga-zangar kin amincewa da sakamakon zaben da aka gudanar a ranar Laraba.
Sai dai a wani bangaren kuma, alkalumman Yan’adawa sun zarta haka.
Wakiliyar BBC ta ce ministan harakokin wajen Tanzania Mahmoud Kombo Thabit ya musanta rahotannin, amma wani jagoran adawa John Kitoka ya ce ‘yansanda da wasu sojojin haya na kasashen waje ne suka aiwatar da kisan mutane cikin dare.
Majalisar Dinkin Dauniya ta yi kiran gudanar da bincike kan zargin amfani da karfin da ya wuce kima a kan masu zanga-zangar.
BBC