An ƙwace miliyoyin daloli, gidajen da ke da alaƙa da Emefiele
Published: 21st, February 2025 GMT
Wata babbar kotun tarayya da ke zamanta a Legas ta bayar da umarnin a ƙwace Dala miliyan 4.7 da Naira miliyan 830 da wasu kadarori da dama da ke da alaƙa da tsohon Gwamnan babban bankin Najeriya (CBN) Godwin Emefiele.
Da yake yanke hukunci a ranar Juma’a, Mai shari’a Yellim Bogoro, wanda a baya ya yi watsi da buƙatar kama Emefiele, ya amince da buƙatar hukumar yaƙi da yi wa tattalin arzikin ƙasa zagon ƙasa ta EFCC, wadda lauya Bilkisu Buhari-Bala ta wakilta.
Kuɗaɗen da a halin yanzu gwamnatin tarayya ta ƙwace, sun kasance a cikin asusun bankunan: First Bank, Titan Bank da Zenith Bank da wasu mutane da hukumomi suke kula da su da suka haɗa da: Omoile Anita Joy, kamfanin Deep Blue Energy Serɓice Limited, kamfanin Exactquote Bureau De Change Ltd, Kamfanin Lipam Investment Services Limited, kamfanin Tatler Services Limited, kamfanin Rosajul Global Resources Ltd, da kamfanin TIL Communication Nigeria Ltd.
Kaddarorin da aka ƙwace na wucin gadi sun haɗa da: Ɗakuna 94 na wani bene mai hawa 11 da ake ginawa a 2 Otunba Elegushi 2nd Aɓenue, Ikoyi, Legas; da AM Plaza, ofisoshi mai hawa 11 a ginin Otunba Adedoyin Crescent, Lekki Peninsula Scheme 1, a Legas; da Imore Industrial Park 1 a Esa Street, Imoore Land, a Ƙaramar Hukumar Amuwo Odofin a Legas; Mitrewood and Tatler Warehouse kusa da Elemoro, Village Owolomi, Ibeju-Lekki LGA, Lagos; da kadarori biyu da aka saya daga kamfanin Chevron Nigeria, da ke cikin rukunin gidaje na Estate Lakes a Lekki da ke Legas.
Mai shari’a Bogoro ya bayyana cewa, duk waɗannan kadarori da kuɗaɗe ne na wasu ayyuka da suka saɓawa ƙa’ida, waɗanda gwamnatin tarayyar Najeriya za ta iya kwace su.
Alƙalin ya ce: “Na ga cewa ayyukan waɗanda ake ƙara a nan ba halastattu be ne. Me zai sa su samu matsalar dala nan take, Godwin Emefiele ya bar CBN a matsayin gwamnan Banki kuma an kasa biyan albashi?
উৎস: Aminiya
এছাড়াও পড়ুন:
Tsokaci Dangane Da Juyin Mulki A Nahiyar Afirka
Ba tare da nausawa daji ba, babban abin da ya kamata mu mayar da hankali a kai shi ne, mu fahimci sabubban da ke bayuwa zuwa ga afkuwar irin wadannan juye-juyen mulki a wannan nahiya tamu ta Afirka, a daya hannun kuma, gano dalilan da zai sanya a kauce musu, na da gayar muhimmanci. Sai dai, mu sani cewa; rashin daukar matakan kaucewa faruwar Juyin Mulkin, to fa tamkar guzurin tad-da shi ne, ko mun sani ko ba mu sani ba, musamman shugabanni, wadanda su ne ake tankwabe wani abu da suka fi kauna sama da komai cikin rayuwar duniya daga hannayensu, a halin suna numfashi ko akasin haka. Da farko ma tukuna, me ake nufi da juyin mulki?.
Ma’anar Juyin Mulki:
Ko mutum bai je makaranta ba, zai kai ga fahimtar juyin mulki na nufin tankwabar ko barar da gwamnati mai-ci ne, sawa’un, ta soja ce ko ta farar-hula. Ko a ilmance ma haka batun yake, wala’alla sai dan wasu karin bayani da za a iya samu. Ga wasu daga fassarorin masana game da hakikanin irin yadda za a kalli, ko fassara “juyin mulki” da; “wasu tsirarin mutane cikin gwamnati, su kifar da gwamnati mai-ci babu zato babu tsammani, a sau da yawan lokuta juyin mulkin kan afku ne cikin yanayi na gumurzu, kuma sau da yawa za a ga sojoji ne ke yin juyin tare da maye-gurbin manyan jagororin gwamnatin (da aka kifar) da wasu mutane na daban” (Decalo, 1990). A wata fassarar an ce, juyin mulki na nufin, “wani yunkuri ne karara da ya saba da tsarin mulkin kasa, wanda sojoji ko wasu manyan mutane cikin gwamnati ke yi na kifar da gwamnati mai-ci” (Powell & Thyne, 2011).
Rabe-raben Juyin Mulki:
Da yawan masana da masharhanta sun kasa juyin mulki zuwa gida hudu tare da gabatar da bayanansu daya bayan daya. Ga su kamar haka;
1- Kilasik Kuu “Classic Coup”.
2- Fales Kuu “Palace Coup”.
3- Kawunta Kuu “Counter Coup”, da kuma
4- Sibil-Militiri Kuu “Cibil-Military Coup”.
Akwai bukatar dan yin karin haske game da wadannan mabanbantan nau’o’i na juyin mulki hudu da aka lasafto:
Kilasik Kuu “Classic Coup
Yayin da sojoji suka game-baki tare da hambarar da wata gwamnati mai-ci, shi ake kira da Kilasik Kuu. Misali, a nan Nijeriya cikin shekarar 1983, inda sojojin wannan kasa suka hade-baki suka kifar da gwamnatin marigayi Alhaji Shehu Shagari, suka maye-gurbinsa da marigayi Janar Muhammadu Buhari.
Fales Kuu “Palace Coup
Yayin da wani sashe na jagororin mulki a kasa, suka tsige shugaban kasa ba tare da sun yi ittifaki da daukacin sojin kasar ba (face wasu tsirari daga cikinsu), shi ake kira Fales Kuu. Irin nau’in wannan juyin mulki, an yi shi a Kasar Mauritania, cikin shekarar 2008.
Kawunta Kuu “Counter Coup
Yayin da wasu suka yi juyin mulki, sai kuma wasu mutane daban suka sake yin wani juyin mulkin, don kalubalantar juyin mulkin farko, shi ake kira da Kawunta Kuu. Misali, bayan juyin mulkin da su Ironsi suka yi a Nijeriya cikin shekarar 1966, bayan wata shida kacal, sai wasu daga sojojin kasar suka hambarar da gwamnatin ta Aguiyi Ironsi.
Sibil-Militiri Kuu “Cibil-Military Coup
Yayin da sojoji da wasu daga cikin jama’ar gari ko ‘yan siyasa a kasa suka hade-baki wajen kifar da wata gwamnati mai-ci, shi ake kira da Sibil-Militiri Kuu. Irin wannan juyin mulki ne ya afku a Kasar Ghana cikin shekarar 1981, inda Jerry Rawlings ya hada-kai da wasu mutanen gari suka yi wa gwamnatin lokacin juyin mulki.
Sai dai, masana da sauran masharhanta na fadin cewa, yawancin juyin mulki na samar da canjin shugabanci ne kawai nan da nan, amma sai ya gadar da rashin kwanciyar hankali na tsawon lokaci a kasa. Ko a nan gida Nijeriya, za a ga cewa; tunanin da kabilar Ibo ke yi a yau cewa; an kange su ga barin samun damar shugabancin wannan kasa, na da alaka ta kud-da-kud da juyin mulki na farko da aka yi a kasar, shekara 51 da suka gabata, wanda sojoji “yan kabilar ta Ibo suka jagoranta. Bugu da kari, ana kallon juyin mulki da wata guguwa da ke barar da tsarin mulkin dimukradiyya, tare da yin silar samar da yanayi na take hakkin Dan’adam a kasa. Sannan, juyin mulkin, kan raunana karfin iko, ko ‘yancin gudanar da ayyukan da wasu hukumomi ke da shi, misali, bangaren shari’a. Juyin mulkin, kan jaza ci gaba da afkuwar wasu juyin mulkin a kasa daga lokaci zuwa lokaci.
Cikin lokuta da dama, za a ga jagororin juyin mulkin, na da’awar dawo da doka da oda ne a kasa tare da nuna cewa; za su zo da nagartattun tsare-tsare, don ciyar da kasa gaba, amma a karshen lamari, irin wadancan alkawura ba kasafai suke cikuwa ba.
Akwai ci gaba a mako na gaba inshaAllah.
ShareTweetSendShare MASU ALAKA