MDD ta bada sanarwan cewa tattalin arzikin kasar Siriya na bukatar shekaru 50 nan gaba kafin ta koma kamar yadda take kafin yakin basasa a kasar.

Tashar talabijan ta Presstv ta nakalato shugaban hukumar UNDP Achim Steiner yana fadar haka a jiya Alhamis, ta kuma kara da cewa hukumar ta ta gudanar da bincike kuma ta gano cewa, rikici da yakin basasa da kuma mamayar kasar da sojojin kasashen yamma suka yiwa kasar, ya sa al-amura sun lalace a kasar, ta yadda idan tana bukatar komawa matsayinta kafin shekara ta 2011 tana bukatar rabin karni kafin hakan ya samu.

Wato kasar Siriya ba zata koma kamar yadda take a shekara ta 2011 ba sai nan da shekara 2080.

Tace Siriya tana bukatar zuba jari mai yawa a ko wace shekara kafin ta sami wannan ci gaban. A halin yanzu dai kasha 90% na mutanen kasar Siriya suna rayuwan talaka. Sannan kasha 50% daga cikinsu basa da aikin yi. Sannan tattalin arzikin kasar GDP na kasar yana rabin matsayinsa a shekara ta 2011. Banda tallafi daga kasashen waje kasar Siriya tana bukatar zuba jari mai yawa don komawa kamar yadda take.

উৎস: HausaTv

কীওয়ার্ড: kasar Siriya tana bukatar

এছাড়াও পড়ুন:

An Fitar Da Kudaden Farfado Da Sassan Birnin Beijing Da Bala’in Ambaliyar Ruwa Ya Shafa

Yau Talata, kwamitin kwaskwarima da raya kasar Sin, ya fitar da kudin Sin RMB yuan miliyan 200, kwatankwacin dalar Amurka miliyan 28, domin tallafawa wajen farfado da sassan birnin Beijing da bala’in ambaliyar ruwa ya shafa, musamman ma fannin sake gina ababen more rayuwar jama’a na sufuri, da samar da ruwan sha, da kiwon lafiya, da na hidimomin al’umma a gundumomin Miyun da Huairou, a kokarin ganin rayuwa ta dawo kamar yadda take a wuraren, an kuma dawo da ayyuka kamar yadda aka saba.

Ban da haka kuma, ma’aikatar kudi, da ma’aikatar lura da ayyukan gaggawa ta kasar sun zuba kudin Sin yuan miliyan 350, kwatankwacin dalar Amurka miliyan 49 don tallafawa biranen Beijing, da Tianjin, da lardunan Hebei, da Shanxi, da Jilin, da Shandong, da Guangdong, da Shaanxi da jihar Mongolia ta Gida, ta yadda za su samu zarafin gudanar da ayyukan ceto, da rage radadin bala’u, da kuma taimakawa wadanda bala’in ya shafa. (Tasallah Yuan)

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Ministan Harkokin Wajen Siriya Yana Rasha Don Bude Sabon Shafi Tsakaninsu
  • Kananan Yan Wasan Dabben Gargajiya Na Iran Sun Zama Zakara A Gasar Wannan Shekara
  • Binciken CGTN: Za A Ci Gaba Da Nuna Kyakkyawan Fata Ga Bunkasar Sin Nan Da Shekaru 5
  • Siriya Da HKI Zasu Gudanar Da Taro A Baku
  • Tattalin arzikin Nijeriya zai ci gaba da bunƙasa har zuwa baɗi — IMF
  • Mataimakin Firaministan Kasar Sin Ya Yi Kira Da A Karfafa Hadin Gwiwar Sin Da Amurka
  • Shugaban Kasar Ivory Coast Ya Bayyana Shirinsa Na Sake Tsayawa Takarar Shugabanci Karo Na Hudu
  • Majalisa ta ba NNPCL mako uku ya yi mata bayanin inda tirilyan 210 ta shiga
  • Amincewa Da Kasar Falasɗinu: Birtaniya Ta Gindaya Wa Isra’ila Sharuɗɗa
  • An Fitar Da Kudaden Farfado Da Sassan Birnin Beijing Da Bala’in Ambaliyar Ruwa Ya Shafa