Amurka Ba Ta Sauya Ba Ko Kadan
Published: 19th, February 2025 GMT
Ban da haka, idan mun mai da hankali kan cudanyar kasashe daban daban, da zamansu tare a cikin duniya, za mu san huldar da ake da ita tare da Amurka, wani bangare ne kawai na huldar kasa da kasa. Saboda haka, yayin da wata kasa ta gamu da matsala, idan wata kasa ta nade hannu, ba ta son ba da taimako, tabbas ba za a rasa bangarorin da ke son samar da taimakon ba.
Sai dai idan mun nazarci sabbin matakan gwamnatin kasar Amurka, za mu ga kusan dukkansu na da nufin tsimin kudi da tabbatar da karin kudin shiga, inda ake iya ganin alamar sauyawar matsayin kasar daga mai cikakken yakini zuwa mai ra’ayin rikau, har ma ta yi watsi da kimarta da kwarjininta. Dalilin da ya sa Amurka yin haka, shi ne, ci gaban kasashe masu tasowa bisa hadin gwiwarsu na haifar da ainihin sauyawar yanayi ga tsare-tsaren kasa da kasa. (Bello Wang)
এছাড়াও পড়ুন:
CMG Ta Kammala Gabatar Da Rahoto Kan Ganawar Shugabannin Sin Da Amurka
Babban rukunin gidajen rediyo da talabijin na Sin CMG, ya gabatar da labarin ganawar da aka yi jiya Alhamis tsakanin shugabannin Sin da Amurka a Busan na Korea ta Kudu, cikin harsuna 85. Kuma zuwa yau Juma’a, mutanen da suka karanta rahotanni masu alaka da ganawar ta hanyoyin watsa labarai na dandalin CMG sun kai miliyan 712. Haka kuma, kafafen watsa labarai na kasa da kasa 1678, sun wallafa tare da tura rahotanni da bidiyon labaran CMG na harsuna daban daban game da ganawar, har sau 4431.
Har ila yau a wannan rana, an gudanar taron tattaunawa na kasa da kasa kan bude kofa da kirkire kirkire da ci gaba na bai daya a kasar Uruguay, wanda CMG da hadin gwiwar ofishin jakadancin Sin dake kasar suka shirya a Montevideo babban birnin Uruguay. (Mai fassara: FMM)
ShareTweetSendShare MASU ALAKA