Gwamnatin Niger Ta Hana Yan Najeriya Dauke Da Passpor Ta Na ECOWAS Shiga Kasar
Published: 19th, February 2025 GMT
Gwamnatin Jumhuriyar Nijer daga jiya Talata ta fara aikin hana yan Najeriya dauke da Passport na kungiyar ECOWAS shiga kasar.
Kafin haka dai mutane daga kasashen ECOWAS suna shiga kasashen kungiyar ba tare da bukatar visar shiga ko wace kasa daga cikin kasashe kungiyar ba.
Amma bayan da kasashe 3 Nijer, Burkina Faso da kuma Mali suka fice daga kungiyar sannan suka samar da sabon Passport a tsakanin kasashen uku, sai al-amura suka fara sauyi tsakaninu da Ecowas.
Sun fara hana wadanda suke rike da Passpory na kasashen ECOWAS shiga kasashen ba tare da visa ba.
Gwamnatin Nijer bata bada sanarwan fara aiki da wannan dokar ba. Kuma wani jami’in shige da fice na Niger ya ce umurnin ne aka basu.
A bangaren Najeriya kuma gwamnatin kasar ta ce bata da masaniyya dangane da hakan. Amma za ta fara bincike don tabbatar da yadda al-amarin yake.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Xi Jinping Ya Ziyarci Sabon Bankin Raya Kasashen BRICS
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp