An Nuna Nezha 2 A Zama Na Musamman A Hedikwatar MDD Dake Birnin New York
Published: 19th, February 2025 GMT
A ranar 17 ga watan Fabrairu, agogon birnin New York ne, aka yi wani zama na musamman na nuna fim din Nezha 2 a hedikwatar Majalisar Dinkin Duniya dake birnin New York na kasar Amurka, wanda hukumar kula da fina-finai ta kasar Sin, da babban rukunin gidajen radiyo da talabijin na kasar Sin wato CMG, da kuma kungiyar masu sha’awar karanta littattafai na kasar Sin dake MDD suka dauki nauyin shiryawa tare.
Xu Haoliang, mataimakin babban sakataren MDD ya bayyana cewa, sakin fim din Nezha 2 a kasashe da yankuna da dama na duniya ya sa kaimi ga mu’amala tsakanin jama’a da al’adu tsakanin kasar Sin da sauran kasashe. Fim din ya hada kasashe da al’adu daban-daban ta hanyar ba da tatsuniyoyi da labaru a cikin al’adun gargajiya na kasar Sin, wanda ya kara samun fahimtar juna tsakanin al’umma. Yadda aka shirya fim din Nezha 2 ya kuma nuna cewa, bunkasuwar fasahar shirya fina-finan cartoon ta kasar Sin ta kai matsayi na duniya. (Mohammed Yahaya)
এছাড়াও পড়ুন:
An Bude Sabon Babin Huldar Sin Da Koriya Ta Kudu
ShareTweetSendShare MASU ALAKA