HausaTv:
2025-05-01@04:07:46 GMT

Mahamoud Ali Youssouf Ya Zama Sabon Shugaban Kwamitin Gudanarwar AU

Published: 15th, February 2025 GMT

An zabi dan takarar kasar Djibouti Mahamoud Ali Youssouf a matsayin sabon shugaban kwamitin gudanarwar kungiyar tarayyar Afrika ta AU.

An zabe shi ne a yayin zaman taron kungiyar a birnin Addis Ababa na kasar Habasha da yammacin yau Asabar.

Ya samu nasara ne a zagaye na 7 da kuri’u 33 daga cikin 49.

Dan shekaru 59 da haihuwa, wanda shi ne ministan harkokin wajen kasar Djibouti zai gaji Moussa Faki Mahamat na Chadi wanda wa’adinsa na biyu kan shugabancin kungiyar zai kare a ranar 15 ga watan Maris.

Manyan kalubalen dake gaban sabon shugaban kwamitin gudanarwa na kungiyar ta AU sun hada da rikicin gabashin Jamhuriyar Demokuradiyyar Kwango da Sudan da kuma matakin da shugaban Amurka Donald Trump ya dauka na rage taimakon da Amurka ke bayarwa, lamarin da ya shafi nahiyar.

A daya bangaren kuma an zabi Selma Haddadi ‘yar kasar Aljeriya a matsayin mataimakiyar shugaban kwamitin na Tarayyar Afirka.

Ta yi nasara da kuri’u 33 a kan sauran ‘yan takara biyu na Morocco da Masar.

Kungiyar mai kasashe 55 dake wakiltar kusan mutum biliyan 1.5 an dade ana sukarta kan rashin tabaka komai kan matsalolin da suka shafi nahiyar.

উৎস: HausaTv

এছাড়াও পড়ুন:

Tarayyar Afirka ta dage takunkumin da ta kakabawa Gabon

Kungiyar Tarayyar Afirka ta dage takunkumin da ta kakabawa kasar Gabon tare da maida ta a cikin cibiyoyinta.

AU, ta sanar da hakan ne yayin taron kwamitin zaman lafiya da tsaro na kungiyar yau Laraba a Addis Ababa.

Hakan dai ya karshen dakatarwar da aka yi wa kasar ta Gaban daga kungiyar, watanni 20 bayan juyin mulkin da sojoji suka yi a watan Agustan 2023.

Kwamitin zaman lafiya da tsaro na AU, ya yi la’akari da mika mulki da ya hambarar da Ali Bongo “gaba daya cikin nasara,” saboda haka ya yanke shawarar dage takunkumin nan take.

‘’Tsarin siyasar Gabon yana da ” gamsarwa” inji sanarwar kungiyar.

Wannan matakin na AU ya zo ne kwanaki uku gabanin rantsar da Janar Brice Oligui Nguema, wanda aka zaba a matsayin shugaban kasar a ranar 12 ga Afrilu.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Gwamnati Ta ƙaddamar Da Sabon Shafin Intanet Don Inganta Sayayya A Tsakanin Ma’aikatunta 
  • Tarayyar Afirka ta dage takunkumin da ta kakabawa Gabon
  • Dokta Bashir ya zama shugaban Majalisar Shari’ar Musulunci ta Nijeriya
  • Riza’i: Babu Hannun  Waje A Cikin Hatsarin Da Ya Faru A Tashar Ruwa Ta Shahid Raja’i
  • Shugaba Tinubu Ya Taya Sabon Firaiministan Kanada Mark Carney Murna
  • Gwamnati Ta Kafa Kwamitin Binciken Yawaitar Haɗurran Tankokin Man Fetur A Nijeriya 
  • Shugaban Kungiyar Hizbullah Ya Abbaci Abubuwa 3 Wadanda Yakamata Kasar Ta Maida Hankali A Kansu
  • Shugaban Kasar Yana Maraba Da Masu Zuba Hannun Jari A Kasarsa Daga Kasashen Waje
  • Tawagar Jami’ai Da ‘Yan Kasuwar Ta Tunusiya Ta Gana Da Mataimakin Shugaban kasar Iran
  • Ministan Harkokin Wajen Kasar Iran Ya Tattauana Da Shugaban Hukumar IAEA