Aminiya:
2025-11-03@03:09:27 GMT

Dalilin da ’yan siyasa ke sauya sheƙa zuwa APC — Tambuwal

Published: 15th, February 2025 GMT

Tsohon Gwamnan Sakkwato, Aminu Waziri Tambuwal, ya bayyana cewa guguwar sauyin sheƙa da ta fara kaɗawa a tsakanin jam’iyyun siyasa a Arewa maso Yammacin ƙasar na da alaƙa na son zuciyar ’yan siyasar yankin.

Tambuwal ya bayyana hakan ne yayin ganawa da manema labarai a taron ƙusoshin jam’iyyar PDP da ya gudana yau Asabar a Jihar Kaduna.

Ɗan Nijeriya ya lashe kyautar Kundin Bajinta na Duniya a fagen ɗaukar hoto Makwabta sun kai karar ma’aurata saboda carar zakaransu

Tambuwal ya zargi ’yan siyasar da ke sauya sheƙa zuwa jam’iyyar APC mai mulki a ƙasar da son zuciya waɗanda ya ce ba sa kishin al’umma.

Tsohon gwamnan ya ce akwai dalilai da ’yan siyasa ke sauya sheƙa daga wannan jam’iyyar zuwa wata, “sai dai abin da na fahimta shi ne galibi ’yan siyasar na yin hakan ne ba don kishin al’umma ba face sai don buƙatunsu na ƙashin kai.

“Sannan kuma a yanzu duk wani ɗan siyasar da ya san abin da ya kamata, ba zai koma jam’iyyar APC ba saboda ƙuncin rayuwa da Gwamnatin Shugaba Bola Tinubu ta jefa ’yan Nijeriya a ciki.

Tambuwal wanda ƙusa ne a jam’iyyar PDP a Nijeriya, ya caccaki Gwamnatin Tarayya ƙarƙashin jagorancin APC da cewa ba ta wata madafar kamawa ballanta sanin inda ta dosa haɗi da rashin tausayin ’yan ƙasar.

Sanatan Sakkwato ta Kudu ya yi kira ga duk jam’iyyun adawa a ƙasar da su haɗa ƙarfi domin kawo wa ’yan Nijeriya sauyin da suke buƙata a Zaɓen 2027.

Aminiya ta ruwaito cewa, daga cikin manyan ’yan siyasar da suka halarci taron akwai tsohon Gwamnan Kaduna, Sanata Ahmed Makarfi da takwaransa na Kano, Sanata Ibrahim Shekarau da tsohon ɗan takarar Gwamnan Jigawa, Mustapha Sule Lamido da Sanata Lado Dan Marke, da Honarabul Isa Ashiri Kudan da Ango Abdullahi da Shugaban Matasa na PDP, Muhammad Kadade Suleiman da sauransu.

 

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: Aminu Waziri Tambuwal zaɓen 2023 Zaɓen 2027 yan siyasar

এছাড়াও পড়ুন:

Zaɓen Tanzania: Shugaba Samia Suluhu Hassan ta yi tazarce

Shugaba Samia Suluhu Hassan ta kasar Tanzania ta sake lashe zaɓen shugaban ƙasar mai cike da ruɗani.

Hukumomin zaɓen ƙasar sun sanar da cewa Shugaba Samia Suluhu ta lashe zaɓen ne da kashi 97 na kuri’un da aka jefa.

Hukamar zaɓen ƙasar ta bayyana cewa mutum 31,913,866 ne suka kaɗa kuri’a a zaɓen, wanda ya gudana a yayin da kasar ke fama da ƙazamar zanga-zanga.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • 2027: Yadda Gwamnoni Suka Yi Fatali Da Mataimakansu Wajen Zaɓo Waɗanda Za Su Gaje Su
  • Gwamnatin Isra’ila Tana Ci Gaba Da Hana Masu Jinya Zuwa Kasashen Waje Neman Magani Daga Gaza
  • Kisan Kiristoci: Ba zan yaƙi ƙasar iyayena kan labaran ƙarya ba — Sojan Amurka
  • Dalilin Da Ya Sa Hukumar NIWA Ta Fara Gyaran Hanyoyin Ruwa A Jihar Legsa
  • Kisan Kiristoci: Za mu kai hari Najeriya — Trump
  • Dalilin Gwamnatin Jihar Kuros Riba Na Raba Wa Manoma Taraktoci
  • Sanata Sunday Marshall Katung Ya Sauya Sheka Zuwa Jam’iyyar APC
  • Zaɓen Tanzania: Shugaba Samia Suluhu Hassan ta yi tazarce
  • Trump Ya Ayyana Nijeriya A Matsayin Ƙasar Da Rayuwar Kiristoci Ke Cikin Hatsari
  • Kotu ta tsige dan majalisar da ya sauya sheka zuwa APC