2025-06-04@02:59:51 GMT
إجمالي نتائج البحث: 4423
«ga gwamnati»:
Sanarwar tafiyar tasa ta biyo bayan ganawar da Inzaghi ya yi da jami’an Inter a ranar Talata, sanarwar da Inter Milan ta fitar ta ce Kulob din da Simone Inzaghi sun yanke shawarar rabuwa, “Wannan shi ne shawarar da aka dauka bisa yarjejeniyar juna”, shugaban Inter Giuseppe Marotta ya kara da cewa “Ina so in gode wa Simone Inzaghi saboda aikin da ya yi, ya matukar taka rawar gani a shekaru 4 da muka shafe muna aiki tare, don haka Inter Milan na yi mashi fatan alheri a duk inda zai samu kanshi a nan gaba”. Inzaghi ya lashe gasar Seria A daya, Coppa Italia biyu da kuma Supercoppa Italia sau uku a lokacin da ya ke San Siro,...
Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Lin Jian, a yau Talata ya yi watsi da ikirarin da Amurka ta yi na cewa kasar ta Sin na karya yarjejeniyar da aka cimma a tsakanin kasashen biyu a tattaunawar tattalin arziki da kasuwanci da aka yi a Geneva, inda ya bukaci Amurka da ta daina yada labarun kanzon kurege. A yayin taron manema labarai na yau da kullum, Lin ya bayyana cewa, kasar Sin ta dauki matakin da ya dace, tare da daukar yarjejeniyar da aka cimma a shawarwarin Geneva da muhimmanci, tare da aiwatarwa yadda ya kamata. Yanzu-yanzu: JUSUN Ta Dakatar Da Yajin Aikin Da Fara A Faɗin Ƙasa Baki Ɗaya Sallah: Gwamnatin Kebbi Ta Raba Naira Miliyan...
“Saboda haka, rundunar ‘yansandan ta nanata cewa, dokar hana duk wani nau’in hawan Sallah a jihar yana nan, zai ci gaba da wanzuwa har zuwa lokacin bukukuwan Sallar Layya ta bana ta 2025 da ake shirin yi domin har yanzu, akwai barazanar tsaro mai karfi a jihar. “An yanke wannan shawarar ne bayan tattaunawa da masu ruwa da tsaki a harkar tsaro biyo bayan rahotannin sirri da ke nuni da shirin wasu bata gari da masu daukar nauyinsu na yin amfani da bukukuwan hawan Sallah wajen gurgunta tsaro da zaman lafiya a jihar, kamar yadda aka tabbatar a lokacin Sallar Azumi.” In ji Rundunar Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin...
“Saboda haka, rundunar ‘yansandan ta nanata cewa, dokar hana duk wani nau’in hawan Sallah a jihar yana nan, zai ci gaba da wanzuwa har zuwa lokacin bukukuwan Sallar Layya ta bana ta 2025 da ake shirin yi domin har yanzu, akwai barazanar tsaro mai karfi a jihar. “An yanke wannan shawarar ne bayan tattaunawa da masu ruwa da tsaki a harkar tsaro biyo bayan rahotannin sirri da ke nuni da shirin wasu bata gari da masu daukar nauyinsu na yin amfani da bukukuwan hawan Sallah wajen gurgunta tsaro da zaman lafiya a jihar, kamar yadda aka tabbatar a lokacin Sallar Azumi.” In ji Rundunar Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin...
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp

An Samu Karuwar Kaso 2.7 Na Yawan Tafiye-Tafiye Zuwa Ketare Yayin Hutun Bikin Dragon Boat Na Kasar Sin
Cikin kwanaki uku na hutun bikin Dragon Boat na kasar Sin, an samu karuwar tafiye-tafiye zuwa ketare da suka kusa miliyan 5.91. Masu tafiye-tafiye sun karu matuka tun daga Asabar har jiya Litinin, inda aka samu karuwar kaso 2.7 bisa dari kan adadin da aka samu a bara. Alkaluman da hukumar lura da shige da ficen al’umma ta kasar Sin ta fitar a Talatar nan, sun nuna karuwar baki masu shigowa kasar Sin daga ketare, musamman wadanda suka ci gajiyar manufar nan ta kawar da bukatar biza. Albarkacin wannan manufa, adadin baki daga ketare da suka shigo kasar Sin yayin ranaku uku na bikin ya kai 231,000, adadin da ya karu da kaso 59.4 bisa dari kan na shekarar bara....
“Bisa ga hakan ne, Gwamnan jihar, Dakta Nasir Idris ya bayar da wannan tallafin don gudanar da shagalin sallar cikin walwala da Jin dadi”. Shugaban ya gode wa Gwamnan jihar kan wannan kokarin da yayi na tunanin a zakulo mata uku a kowace rumfar zabe a duk mazabun kananan hukumomin 21 na jihar don basu tallafin N30,000 don gudanar da shagalin sallar Eid-kabir, “muna masa godiya a madadin matan da suka ci gajiyar tallafin”. Daga karshe, Zuru ya yi kira ga sauran shugabanni da su yi koyi da Gwamnatin jihar Kebbi kan tallafa wa al’umma a jihar musamman a irin wannan lokaci ga wannan lokaci da jama’a ke da bukatar yin layya. Daga kanmu, magana ta ƙare....

Guardian: Isra’ila Tana Kai Wa Makarantun Dake Dauke Da ‘Yan Gudun Hijira a gaza Hari, Tana Sane Da Hakan
Jaridar Guardian ta ta kasar Birtaniya ta bada labarin cewa, Hare-haren da sojojin HKI su ka kai kan wata makaranta, inda yan gudun hijira Falasdinawa suke samun mafaka da gangan suka yi shi, suna sane, kuma a halin yanzu suna Shirin kai wa wasu makarantun guda 4 hare-hare nan gaba. Jaridar ta kara da cewa: Isra’ila ta ayyana wasu Karin makarantu wadanda Falasdinawa suke samun mafaka a cikinsu domin kai musu hare-hare a nan gaba. A lokacinda HKI ta kasa ganin mayakan Hamas a fili sojojinta sun koma kan kissan Falasdinawa fararen hula, wadanda suke samun mafaka a makarantu. A cikin watanni da suka gabata sojojin mamayar sun kai hare-hare akan wasu gine-ginen 6 wadanda suka kasance makarantu ne, wadanda...
Daya daga cikin manyan-manyan jami’an gwamnatin tsohon shugaban kasar Amurka Joe Biden, ya bayyana cewa: “Babu tantama gwamnatin HK Isra’ila ta tafka laifukan yaki a kan Falasdinawa a zirin Gaza da ta killace. Matthew Miller wanda ya yi aiki a matsayin kakakin ma’aikatar harkokin wajen Amurka tun daga 2023 har zuwa karshen gwamnatin Joe Biden, ya fada wa tashar talabijin ta Sky News kan cewa; Isra’ilan ta tafka laifukan yaki. Da aka yi masa tambaya a kan yakin Gaza a fadar White House, Miller ya ce; An yi ta samun tsabani dangane da yakin, sabani manya-manya wani lokacin kuma kananan sabani, kan yadda za a kare dangantakar Amurka da HK Isra’ila duk tare da abinda take aikatawa.”. Amma Miller ya...
Ofishin shugaban kasar Turkiya, ya bayyana fatan cewa tattaunawar da ake yi a tsakanin Rasha da Ukiraniya a birnin Istanbul, za ta kai ga tsayar da tsagaita budewa juna wuta wanda kuma zai ga, kawo karshen yakin baki daya. Ofishin shugaban kasar Turkiya ya bayyana haka a yau Talata, ta kuma kara da cewa,; Tattaunawar da aka gudanar a jiya Litinin a tsakanin Rasha da Ukiraniya a kuma fadar shugaban kasar Turkiyya dake birnin Istanbul tana cike da fata na tsayar da yakin. Kamfanin dilalncin labarun “Sputnik” na kasar rasha ya ambato majiyar fadar shugaban kasar ta Turkiya tana cewa; Shakka babu duk wata tattaunawa da bangarori za su zauna akan teburi, tana tattare da kyakkyawan fata, a dalilin haka,...
A cikin sanarwar da dukkan bangarorin da suka halarci taron suka sanya wa hannu, an amince da cewa, kungiyar za ta ba da wata guda domin tattauna bukatun JUSUN. Wani bangare na yarjejeniyar ya bukaci Gwamnatin Tarayya ta saki kudaden da suka wajaba ga bangaren ma’aikatan shari’a a cikin wannan watan. Sanarwar ta jaddada cewa, da zarar an fitar da kudaden, dole ne a aiwatar da duk wasu bukatu da kungiyar ta JUSUN ta gabatar ba tare da bata lokaci ba. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe...
Yau Talata, kungiyar masu jigilar kayayyaki da sayayya ta kasar Sin ta gabatar da alkaluman watanni 4 na farko na bana, wadanda suka nuna cewa, a watan Afrilu, sha’anin jigilar kayayyaki ya bayyana inganci da boyayyen karfi, kuma duk da kalubaloli da matsin lamba daga ketare da aka fuskanta, ya tafi yadda ya kamata tare da samun bunkasuwa. Kana daga watan Janairu zuwa na Afrilu, darajar hajojin da aka yi jigilarsu a kasar ta kai dalar Amurka triliyan 16, wadda ta karu da kashi 5.6 cikin kashi 100 bisa na makamancin lokaci a bara. Kazalika, yawan hajojin da aka yi jigila yana cikin wani yanayi mai dorewa, bisa la’akari da yadda jigilar kayayyaki ta amfani da layin dogo da...
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Ministan Yada Labarai da Wayar da Kan Jama’a, Mohammed Idris, yace nasarorin da gwamnatin Tinubu ta samu cikin shekaru biyu kadai shaida ce ta shugabanci mai hangen nesa da jaruntaka. Ya bayyana haka ne a yayin taron farko na National Dialogue on Citizen Engagement and National Security da aka gudanar a Abuja, mai taken “One Voice, One Vision: Uniting Perspectives for a Stronger Nigeria.” A cewar Ministan, wannan taro ya zo a daidai lokacin da Najeriya ke kokari yi amfani da damamaki da ke gabanta. Ya jaddada cewa wannan dandali da Voice of Nigeria (VON) ta shirya ba kawai taron tattaunawa kan manufofi bane, sai dai wata kafa ce da aka tanada domin hada ra’ayoyi da...
Iftila’in ambaliyar ruwa a garin Mokwa a Ƙaramar Hukumar Mokwa ta Jihar Neja ta yi ajalin mutane sama da 200, yayin da wasu sama da 500 suka bata. Ambaliyar, wadda ita ce mafi muni a yankin cikin shekaru 60, ta shafi yankunan Tiffin Maza da Anguwan Hausawa, bayan ruwan sama kamar da bakin ƙwarya a ranar Laraba da ta gabata da daddare. Ɗaruruwan gidaje sun lalace, inda mutane da yawa suka rasa matsugunansu. Kafar yaɗa Labarai ta BBC ta ruwaito a ranar Litinin cewa yawan mutanen da suka mutu ya ƙaru zuwa sama da 200, kuma an dakatar da ayyukan ceto saboda hukumomi sun yanke ƙauna daga samun wasu da rai. Babbar Sallah: Farashin kayan miya ya yi tashin...

Ministan Harkokin Wajen Iran Ya Ce: Alakar Iran Da Lebanon Tarihi Ce Mai Tushe Da Ta Ginu Kan Mutunta Juna
Ministan harkokin wajen Iran ya bayyana cewa; Dangantakar Iran da Lebanon tarihi ce, mai tushe, kuma ta ginu ne bisa mutunta juna Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Araqchi ya bayyana alakar da ke tsakaninta da kasar Lebanon a matsayin mai tarihi, mai tushe, kuma ta ginu ce bisa mutunta juna. Ya ce: “Kasashen biyu sun kuduri aniyar bunkasa wannan alakar. A jawabin da ya yi a filin jirgin sama na birnin Beirut, inda wakilin kakakin majalisar dokokin kasar Lebanon ya tarbe shi, Araqchi ya yi nuni da cewa ziyarar wani bangare ne na rangadin da yake yi a yankin bayan ziyarar da ya kai birnin Alkahira na Masar, kuma zai gana da jami’an kasar ta Lebanon. Ya kara da...

Ministan Harkokin Wajen Iran Ya Soki Rahoton Hukumar Kula Da Makamashin Nukiliya Ta Duniya Kan Kasarsa
Ministan harkokin wajen Iran ya soki rahoton hukumar kula da makamashin nukiliya ta duniya yayin ganawa da Grossi a birnin Alkahira Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Araqchi ya soki sabon rahoton da hukumar ta IAEA ta fitar kan shirin makamashin nukiliyar kasar Iran yayin ganawarsa da babban darektan hukumar ta makamashin nukiliya ta duniya Rafa’el Grossi a birnin Alkahira. A yayin taron, wanda aka gudanar a babban birnin Masar bisa bukatar Grossi, Araqchi ya tunatar da hukumar ta IAEA da babban daraktan ta game da alhakin da ya rataya a wuyansu na gudanar da ayyukansu cikin kwarewa. Har ila yau ministan harkokin wajen na Iran ya soki zarge-zarge marasa tushe da ke kunshe cikin sabon rahoton hukumar ta IAEA...

Iran Ta Yi Watsi Da Da’awar Kungiyar Hadin Kan Kasashen Larabawa Na Da’awar Mallakar Wasu Yankunan Iran
Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Iran ya jaddada cewa: Tsibiran guda uku na Tunb Babba da Tunb Karami da Abu Musa yankuna ne Iran Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran Isma’il Baqa’i ya yi watsi da ikirari da kungiyar hadin kan kasashen Larabawan yankin tekun Fasha (PGCC) ta yi dangane da tsibiran Iran guda uku, yana mai jaddada cewa: Jamhuriyar Musulunci ta Iran za ta dauki dukkan matakan da suka dace don tabbatar da tsaro da muradun kasar a cikin tsibiran guda uku. Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar ta Iran ya jaddada matsayin Jamhuriyar Musulunci ta Iran tare da yin watsi da ikirarin da ke kunshe a cikin bayanin karshe na taron ministocin harkokin wajen kasashen yankin tekun Fasha karo na...
Sojojin mamayar Isra’ilan sun sake aiwatar da wani sabon kisan kiyashi a birnin Rafah, inda suka kashe mutane da dama a kusa da cibiyar rarraba kayan agaji Fararen hula 23 ne suka yi shahada yayin da wasu kusan 200 suka jikkata a yau Talata lokacin da sojojin mamayar Isra’ila suka bude wuta kan mai uwa da wabi wa fararen hula a kusa da wata cibiyar rarraba kayan agaji a birnin Rafah da ke kudancin Zirin Gaza. Majiyoyin kiwon lafiya sun bayyana cewa: Shahidan sun fadi ne a lokacin da suke jiran agajin jin kai a titunan Rafah, lokacin da jirage masu saukar ungulu suka bude musu wuta. An tantance biyar daga cikin shahidan, yayin da wasu fiye da 20 kuma...
Ya ce yanzu lokaci ne da Arewa za ta nuna adalci ta hanyar barin shugaba daga Kudu ya kammala wa’adin mulkinsa. Ya ƙara da cewa, “Idan za a fitar da wani ɗan takarar shugaban ƙasa daga ‘yan adawa a nan gaba, to ya dace ya fito daga Kudu maso Yamma. Wannan ne dai-daito da adalci.” Sanatan ya kuma soki gwamnatin baya da cewa ko da yake kusan dukkan shugabannin tsaro sun fito ne daga Arewa, amma hakan bai dakatar da ta’addanci a yankin ba, kuma bai hana hare-hare da kashe-kashe a jihohin Filato, Binuwai da sauran jihohin Arewa ta Tsakiya ba. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na...
Farashin kayan miya, musamman kayan gwari ya yi tashin gwauron zabo a yayin da Babbar Sallah ta bana ta kawo jiki. Kuɗin kayan lambu ya ninka sau uku a cikin mako biyu, a yayin da Babbar Sallar ta zo wa iyalai da dama a Najeriya a hagunce, a sakamakon fama da matsananciyar matsalar tsadar rayuwa. Wannan hauhawan farashin, wana ta zarce abin da aka saba gani a lokutan rani, ya kasaara ƙarfin iyalai yin sayayya domin girki abincin Sallah, wanda hakan ya haifar da damuwa, musamman a jihohin Kano, Taraba, Kwara, da Jigawa. Tsadar da ba a taɓa gani ba a Kano Al’umma a Jihar Kano sun koka bisa mummunan tasirin wannan tsadar rayuwa. Wani ma’aikacin gwamnati mai ’ya’ya biyar,...
Hukumar ta buƙaci jama’a da su kasance cikin shiri tare da bibiyar sabbin rahotannin yanayi da ta ke fitarwa. Ta kuma ja hankalin hukumomin da ke kula da madatsun ruwa da su saka ido kan matakin ruwa domin gujewa cike-ciken da ka iya haddasa ambaliya. Rahoton ya ƙara da cewa jihohin kudancin Nijeriya da kuma na Arewa ta Tsakiya za su riƙa samun ruwan sama da iska a kai a kai. Sai dai NiMet ta ce jihohin Kwara, Kogi, Neja, Nasarawa, Benuwe, Taraba, Adamawa, Kaduna, Kano, Katsina, Sakkwato, Edo, Delta da Abuja ba za su samu ruwan sama da yawa kamar yadda aka saba ba. Hukumar ta buƙaci manoma da su yi amfani da dabarun zamani da ilimin kimiyya wajen...
Gwamna Dauda Lawal na jihar Zamfara ya amince da biyan ma’aikatan gwamnati da ‘yan fansho da ke fadin jihar kyautar Sallah (Eid-el-Kabir) a matsayin alawus-alawus da ake yi a fadin jihar domin nuna tausayi da jajircewa wajen kyautata rayuwar ma’aikata. Kwamishinan yada labarai da al’adu na jihar, Mahmud Muhammad Dantawasa ne ya bayyana haka a wata sanarwa da ya rabawa manema labarai a Gusau. A cewar sanarwar, matakin na Gwamnan na da nufin rage wa ‘yan kasa matsalar kudi a lokacin bukukuwan Sallah da kuma ba su damar gudanar da bukukuwan cikin farin ciki da mutuntawa. Gwamnan wanda a halin yanzu yake aikin hajji a birnin Makkah na kasar Saudiyya ya mika gaisuwar Sallah ga al’ummar Zamfara....
Masu sayar da rago a jihar Zamfara sun nuna damuwarsu kan rashin samun ciniki gabanin bikin Eid-el-Kabir, duk da cewa ana samun dabbobi a kasuwanni. Shugaban kungiyar masu sayar da dabbobi ta jihar Zamfara, Malam Saidu Ibrahim Gusau ya bayyana haka a wata tattaunawa da gidan rediyon Najeriya a Gusau. Malam Gusau ya bayyana cewa, duk da cewa ana samun raguna da yawa, amma an samu karancin masu saye. Sai dai ya bayyana fatan cewa lamarin zai iya gyaruwa yayin da bukukuwan Sallah ke kara gabatowa. “Amma idan abubuwa sun ci gaba da haka, to gaskiya, akwai matsala ta gaske,” “Har yanzu, na yi imani cewa da sauran kwanaki abubuwa za su iya canzawa, in...
Dillalan rago a jihar Kano sun nuna damuwarsu kan rashin zuwan masaya da suke fuskanta duk da ‘yan kwanaki da suka rage ayi bukukuwan Sallah. Ziyarar da aka kai kasuwar dabbobi ta Gandun Albasa ta nuna cewa, da yawa daga cikin masu sayar da kayayyaki sun shafe tsawon yini ba tare da yin cinikin komai ba, inda masu saye kadan ke zuwa sayen dabbobin hadaya. Da yake zantawa da gidan rediyon Najeriya shugaban kasuwar dabbobi ta Gandun Albasa, Alhaji Yusuf Ahmed Muhammad ya bayyana cewa duk da cewa mutane na zuwa kasuwar domin tambayar farashin, amma a zahiri kadan ne ke saye. Ya bayyana cewa yayin da wasu kwastomomi ke siyan kananan raguna da farashinsu ya kai...
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
’Yan bindiga sun sako wani magidanci da suka yi garkuwa da shi da amaryarsa na tsawon wata bakwai, bayan sun bindige matar tasa tare da karɓar kuɗin fansa Naira miliyan 30 daga iyalansa. A watan Oktobar 2024 ne ’yan bindiga suka yi garkuwa da mutumin suna Yakubu Dada tare da amaryarsa, a yayin da ma’auratan ke tafiya a kan babban titin zuwa Kontagora a Jihar Neja. A lokacin ’yan bindigar sun buƙaci kuɗin fansa Naira miliyan 10 daga iyalan mutumin, wanda tsohon ma’aikacin gwamnati ne. Ba su sako shi ba sai a ranar Litinin, bayan da suka karɓi ƙarin Naira miliyan 20 daga iyalansa, jimilla Naira miliyan 30 ke nan. A lokacin da suka yi garkuwa da ma’auratan sun buƙaci...
’Yan bindiga sun sako wani magidanci da suka yi garkuwa da shi da amaryarsa na tsawon wata bakwai, bayan sun bindige matar tasa tare da karɓar kuɗin fansa Naira miliyan 30 daga iyalansa. A watan Oktobar 2024 ne ’yan bindiga suka yi garkuwa da mutumin suna Yakubu Dada tare da amaryarsa, a yayin da ma’auratan ke tafiya a kan babban titin zuwa Kontagora a Jihar Neja. A lokacin ’yan bindigar sun buƙaci kuɗin fansa Naira miliyan 10 daga iyalan mutumin, wanda tsohon ma’aikacin gwamnati ne. Ba su sako shi ba sai a ranar Litinin, bayan da suka karɓi ƙarin Naira miliyan 20 daga iyalansa, jimilla Naira miliyan 30 ke nan. A lokacin da suka yi garkuwa da ma’auratan sun buƙaci...
Bidiyon ya jawo martani daban-daban a tsakanin jama’a. Wasu sun goyi bayan matakin malamin, inda suka bayyana cewa yana da ‘yancin kare kansa a irin wannan lokaci na rashin tsaro. Amma wasu sun soki abin da ya yi, inda suka ce zuwa da makami wajen taron jama’a ko addini hatsari ne mai girman gaske. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Ya ƙara da cewa FRSC ta fara bincike kan dalilan da ke jawo hatsarin, kuma za ta gabatar da sakamakon binciken ga hedikwatarta da kuma Gwamnatin Jihar Kano domin ɗaukar matakan da suka dace don hana irin faruwar irin wannan iftila’i a gaba. Hukumar ta kuma sake jaddada ƙudirinta na wayar da kan al’umma kan amfani da hanya yadda ya dace da kiyaye lafiyar masu amfani da hanya. A nasa ɓangaren, Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, wanda mataimakinsa, Kwamared Aminu Gwarzo, ya wakilta, ya gode wa FRSC bisa ziyarar. Ya bayyana damuwarsa cewa wajen da hatsarin ya faru ya daɗe yana haddasa mummunan haɗura, inda ya bayyana cewa gwamnati za ta yi duk abin da ya kamata don hana...
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Ambaliyar ruwa na ci gaba da raba dubban mutane da matsugunansu, tare da lalata dukiyoyi a faɗin Najeriya. Ko a makon da ya gabata, wasu al’ummomi a Karamar Hukumar Mokwa da ke Jihar Neja sun fuskanci irin wannan ambaliya da ta yi sanadiyyar rasa ɗaruruwan rayuka da dukiyoyi masu yawa. NAJERIYA A YAU: Mokwa: Tsakanin Taraddadin Rashin Matsuguni Da Jimamin Rashin ’Yan-Uwa DAGA LARABA: “Sai Na Tara Kudin Cin Abinci Na Nake Iya Siyan Audugar Al’ada” Ko waɗanne hanyoyi za a bi domin kauce wa ɓarnar ambaliya a Najeriya? Wannan ne batun da shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci zai yi nazari a kai. Domin sauke shirin, latsa nan
Kasar Sin ta yi hasashen cewa an yi balaguro miliyan 657 a tsakanin yankunan kasarta lokacin hutun bikin Duanwu, wato Dragon Boat, daga ranar 31 ga watan Mayu zuwa ranar 2 ga watan Yuni, inda matsakaicin adadin tafiye-tafiyen da aka samu lokacin hutun bikin a kowace rana ya kai miliyan 219. Ma’aikatar sufuri ta kasar ta bayyana cewa, an samu karuwar kaso 3 bisa dari na adadin tafiye-tafiyen da ake samu lokacin bikin a mizanin shekara-shekara. (Abdulrazaq Yahuza Jere) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na...
Ya ce an kai farmakin ne a kudancin yankin Mai-Galma a karamar hukumar Maru, domin dakile wani gagarumin farmaki da ‘yan bindiga suka shirya kai wa wasu al’ummomi. Bayan harin ta sama, sai aka tura sojojin kasa domin bin sahun ‘yan ta’addan da aka tarwatsa. “Sun tabbatar da lalata babura tare da kashe ‘yan ta’adda sama da 20. “Abin takaici, a yayin harin ta sama, ‘yan banga biyu a yankin, an kuskure su yayin da wasu kuma suka samu raunuka,” inji shi. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya...
Sabon fira ministan kasar Sudan Kamil Idris ya yi kira ga kasashen waje masu taimaka wa dakarun daukin gaggawa “RSF” da su kawo karshen taimakon da suke bawa masu aikata laifi.” Idris wanda yake jawabin bayan kama aiki a jiya ya ce; Jami’an tsaro da kuma mahukuntan kasar ta Sudan suna da cikakken goyon baya a kasar don kawo karsehn ‘yan tawaye, masu dauke da makamai.” Idris ya kuma ce; A shirye yake ya yi wa kasa aiki a cikin kekyawar anniyya da kwazo.” Gwamantin kasar Sudan dai tana zargin Hadaddiyar Daular Larabawa da taimaka wa dakarun kai daukin gaggawa “RFS” wacce ta dauki shekaru biyu tana fafatawa da sojojin kasar. Wasu daga cikin kasashen da Sudan take zargi da...
Ministan harkokin wajen Jamhuriyar musuluinci ta Iran wanda ya kai Ziyarar aiki kasar Masar ya bayyana cewa, cinikayya a tsakanin kasashen biyu za ta karu. Ministan harkokin wajen na Iran wanda ya gabatar da taron manema labaru na hadin gwiwa da takwaransa na kasar Masar ya ce: “A bisa yarjejeniyar da bangarorin biyu su ka cimmawa za a kara girman kasuwancin da ake tsakanin Iran da Masar.” Abbas Aragchi ya godewa mai masaukinsa na Masar Badar Abdulatif, saboda tattaunawa mai muhimmanci da su ka yi.” Bugu da kari Abbas Arakci ya yi wa shugaban kasar Masar godiya saboda ganawa da ya yi da shi, yace: Wannan Shi ne ganawata ta hudu da shugaban da shi daga sheakarar da ta gabata’....
Sabon fira ministan kasar Sudan Kamil Idris ya yi kira ga kasashen waje masu taimaka wa dakarun daukin gaggawa “RSF” da su kawo karshen taimakon da suke bawa masu aikata laifi.” Idris wanda yake jawabin bayan kama aiki a jiya ya ce; Jami’an tsaro da kuma mahukuntan kasar ta Sudan suna da cikakken goyon baya a kasar don kawo karsehn ‘yan tawaye, masu dauke da makamai.” Idris ya kuma ce; A shirye yake ya yi wa kasa aiki a cikin kekyawar anniyya da kwazo.” Gwamantin kasar Sudan dai tana zargin Hadaddiyar Daular Larabawa da taimaka wa dakarun kai daukin gaggawa “RFS” wacce ta dauki shekaru biyu tana fafatawa da sojojin kasar. Wasu daga cikin kasashen da Sudan take zargi da...
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Gwamnan Babban Bankin Iran ya wanda yake Ziyara a kasar China ya gabaatr da shawarar a kafa bankin hadin gwiwa a tsakanin kasashe mambobi a kungiyar Shangai. Muhammad Riza Farzin ya isa kasar ta China ne domin halartar taron gwamnonin manyan bankunan kasashen da suke mambobi a cikin wanann kungiya, domin yin nazarin hanyoyin aiki tare a tsakaninsu da kuma musayar kudade. Muhammad Riza Farzin ya kuma kara da cewa; Daga cikin ajandar taron kungiyar a China, akwai tattauna batun kafa bankin hadin gwiwa wanda daga cikin ayyukansa a akwai aiwatar da hada-hadar kudade da mu’amala a tsakanin Bankuna.” Gwamnan babban bankin na Iran ya bayyana cewa, wannan kungiyar tana da matukar muhimmanci, domin tana kunshe da kasashe goma daga...
Ministan harkokin wajen Turkiya Hakan Fidan ya jaddada goyon bayan da kasarsa take bai wa tattaunawar da ake yi a tsakanin Rasha da Ukiraniya, ya kuma kara da cewa; Ana yin nazarin yadda za a gana, a kuma tattauna tsakanin shugabannin kasashen biyu.” Fidan ya kuma bayyana fatansa na ganin cewa tattaunawar da aka bude a yau ta kai ga haifar da daa mai ido. Haka nan kuma ya ce, kasarsa za ta yi duk abinda za ta iya, domin ganin cewa kasashen biyu sun kai ga cimma yarjejeniyar zaman lafiya a tsakaninsu. Kafar watsa labaru ta Axios; ta ambato majiyar Ukiraniya na cewa, Rasha ta gabatar da tsarin zaman lafiya wanda ya kunshi yadda za a kawo karshen yaki....
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Gwamnatin Kano ta ba makarantu hutun kwanaki goma domin bikin Babbar Sallah da za a yi ranar Juma’ar wannan makon. Ma’aikatar Ilimi ta Jihar Kano, a cikin wata sanarwa ta bayyana cewa makarantun za su fara hutun ne daga ranar Laraba, 4 ga watan nan na Yuni da muke ciki, zuwa ranar Lahadi, 15 ga wata. Sanarwar ta kuma bukaci iyaye da ’ya’yansu suke makarantun kwana da su je da wuri domin daukar yaran a ranar Laraba. Kwamishinan mai kula da ma’aikatar, Ali Makoda, ya kuma bukaci iyaye da su tabbata daliban sun dawo makaranta a kan kari bayan kare hutun Babbar Sallar. An lakaɗa wa Mataimakin Firinsifal duka saboda hana satar a jarabawa Uba ya harbe ɗansa har lahira...
Wani magidanci ya yi mutuwar kasko da wani mai sana’ar jari-bola, bayan da gungun wasu ’yan jari-bola suka yi kokarin cire tagar gidansa da karfin tsiya a yankin Babban Birnin Tarayya. Magidancin, wanda ke sana’ar sayar da tufafin gwanjo ya gamu da ajalinsa ne bayan bata-garin sun caka masa wuka a yankin Tsohuwar Kutunku da ke Karamar Hukumar Gwagwalada. Wani dan unguwar mai suna Francis Nnamdi, ya ce da misalin karfe 9.26 na dare ne wasu mutum uku masu sana’ar bola-jari suka je gidan mutumin, suna kokarin cire karfen tagarsa. Ya ce cewa bayan mai gidan ya gan su ne ya tunkare su domin jin dalilinsu na neman cire masa tagogi, inda a garin haka daya daga cikinsu ya zaro...
Rundunar ‘yansanda a jihar Gombe ta umurci rufe duk wata tashar sauka ko daukar fasinjoji a cikin garin Gombe ciki har da fitacciyar tashar Dadin Kowa, inda ta ce, tashar Ibrahim Hassan Dan-Kwambo ce kadai halastacciya. Bugu da kari, motocin haya da ke dauke da amintaccen launin kala na gwamnati a cikin garin Gombe ne kadai suke da izinin zirga-zirgar daukar fasinjoji a birnin. Gwamnatin Jihar Gombe Ta Rattaba Hannu Kan Yarjejeniya Domin Gina Mayankar Dabbobi Ma’aikatar Tsaron Kasar Sin Ta Maida Martani Game Da Munanan Kalaman Sakataren Tsaron Amurka Kan Kasar Sin Wannan umarni na kunshe ne acikin wata sanarwar manema labarai da jami’in hulda da jama’a na rundunar a jihar, DSP Buhari Abdullahi ya fitar, a ranar...
Ranar Laraba, ruwan sama da hazo za su afkawa jihohin Zamfara, Adamawa, Kaduna, Sokoto, Kebbi da Taraba. Daga baya kuma, za a samu ruwan sama a jihohin Katsina, Bauchi da Sakkwato. Arewa ta rsakiya za ta fuskanci ruwan sama a Abuja, Nasarawa, Neja da Binuwe da safe, yayin da yamma za ta shafi Nasarawa, Filato, Kwara da Kogi. A Kudu, ana hasashen ruwan sama da safe a Ogun, Ondo, Oyo, Edo, Enugu, Ebonyi, Cross River, Rivers da Akwa Ibom, sannan daga bisani a rana, za a sami ruwan sama a fadin yankin. NiMet ta gargjama’a su ɗauki matakan kariya, musamman inda hadari zai faru, domin iska mai ƙarfi na iya gabatar da haɗari. An shawarci mutane su guji tuƙi a...
Rundunar ‘Yan Sanda ta Jihar Nasarawa ta cafke wasu gungun masu satar motoci tare da dawo da wata mota da aka sace. A cikin wata sanarwa da Jami’in hulɗa da jama’a na ‘yan sanda, SP Ramhan Nansel ya fitar, ya bayyana cewa jami’an ‘yan sanda sun kama wasu mutane huɗu da ake zargi da hannu a cikin wannan aika-aika, a kan hanyar Doma zuwa Lafia, bisa sahihan bayanan sirri. Sanarwar ta kara da cewa, ana zargin waɗanda ake tuhuma da haɗa kai wajen satar mota da bindiga a Jihar Enugu, inda suka kwace wata mota kirar Toyota Venza mai launin baki da karfin bindiga. Sanarwar ta bayyana cewa, saboda saurin tattara bayanan sirri da haɗin gwiwar jihohi ba tare...
Ma’aikatar Harkokin Wajen Iran ta bayyana cewa: Rahoton IAEA na nuna son kai kuma an shirya shi ne a karkashin tasirin wasu kasashe Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran ya bayyana cewa: Rahoton da hukumar kula da makamashin nukiliya ta duniya ta fitar ya kunshi maimaici da wuce gona da iri, yana mai jaddada cewa, an shirya wannan rahoton ne karkashin tasirin wasu kasashen Turai. Ya bayyana takaicinsa kan yadda kasashen yammacin duniya ke cutar da martabar wata kungiya ta duniya ta hanyar siyasantar da ayyukanta. A farkon taron manema labarai na mako-mako, Baghaei ya yi la’akari da zagayowar ranar wafatin Imam Khumaini (Allah ya kara masa yarda) da shahidan juyin juya halin Musulunci. Ya kara da cewa: Ma’aikatar harkokin...
Ministan harkokin wajen kasar Iran ya gana da shugaban kasar Masar a birnin Alkahira Ministan harkokin wajen Iran Abbas Araqchi ya gana da shugaban kasar Masar Abdel Fattah el-Sisi a yau Litinin. Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Arakchi ya isa birnin Alkahira da yammacin jiya Lahadi domin tattaunawa da manyan jami’an kasar Masar. A yayin wannan ziyara, Araqchi ya gana da ministan harkokin wajen Masar Badr Abdel Aty da shugaban kasar Masar Abdel Fattah el-Sisi inda suka tattauna batutuwan baya-bayan nan a dangantakar da ke tsakanin kasashen biyu, da ci gaban yankin, musamman batun kalubalantar laifukan haramtacciyar kasar Isra’ila, da kuma wasu batutuwan kasa da kasa. Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Iran Isma’il Baqa’i ya sanar da Shirin ministan harkokin...
Wani shafin yanar gizo na sojojin Amurka ya tabbatar da cewa dakarun kasar Yemen ne suka kaiwa jirgin Truman mai dakon jiragen sama hari Wani shafin yanar gizo na sojojin Amurka ya amince da cewa: Dakarun kasar Yemen ne suka lalata jirgin Truman. Shafukan yanar gizo na rundunar sojin Amurka Stars and Stripes sun watsa rahoton a yau Litinin cewa: Jirgin dakon jiragen sama USS Harry S da Truman sun dawo Amurka bayan da rikici ya yi tsanani a yankunan da suke shawagi. An lura cewa manyan bangarorin jirgin dakon jiragen saman Amurka a teku sun samu matsalolin fashe-fashe wanda hakan ke bayyana cewa; Jirgin Ruwan Truman da ma’aikatansa sun samu matsalolin ne a cikin tekun Bahar Maliya. Shafukan Stars...
Sojojin Yemen sun kai jerin hare-hare har sau 4 kan filin jirgin saman Ben Gurion tare da wasu wurare masu muhimmanci a cikin Isra’ila Sojojin Yemen sun sanar da aiwatar da hare-haren soji masu tsanani guda hudu a kan filin jirgin sama na Lod, wanda aka fi sani da “Ben Gurion” a haramtacciyar kasar Isra’ila, da kuma wasu muhimman wurare a yankunan Jaffa, Ashdod da Umm al-Rashrash a cikin Palasdinu da aka mamaye. Rundunar sojin Yemen ta bayyana a cikin wata sanarwa da ta fitar a yau cewa: Rundunarta ta kai wasu hare-haren soji masu inganci a kan tashar jirgin saman Lod da ke yankin Jaffa da aka mamaye da makamai masu linzami. Dakarun sojin sun tabbatar da cewa: wannan...
Sojojin mamayar Isra’ila sun kai hari kan fararen hula da suka yi tawaga zuwa wajen raba kayan agajin jin kai a garin Rafah Rahotonni sun bayyana cewa: A rana ta biyu a jere, sojojin mamayar Isra’ila suna ci gaba da aiwatar da kisan kiyashi kan al’ummar zirin Gaza da ke fama da yunwa. Shafin yanar gizo na Falestine Today ya watsa rahoton cewa: A safiyar yau Litinin 2 ga watan Yunin shekara ta 2025, sojojin mamayar Isra’ila sun aiwatar da wani sabon laifi ta hanyar kai hare-hare kan Falasdinawa a kusa da cibiyar bada agajin Amurka da ke birnin Rafah. Ya zuwa yanzu dai wannan aika-aika ya yi sanadin shahadan Falasdinawa 3 tare da raunata wasu 60, ba a ma...
Wani yaro ɗan shekara 15 ya rasa ransa bayan mahaifinsa ya harbe shi bisa kuskure, yana zaton biri ne. Wannan lamari mai ban tausayi ya faru ne a gonar magidancin inda shi da ɗan nasa suke aiki, a yankin Iye Ekiti da ke Ƙaramar Hukumar Ilejemeje ta Jihar Ekiti. Kwamishinan ’Yan Sanda na Jihar Ekiti, Joseph Eribo, ya tabbatar da faruwar lamarin a yau a Ado-Ekiti. Ya bayyana cewa manomin ya daɗe yana fama da hare-haren birai a gonarsa kuma ya kai bindiga domin kare amfanin gonarsa. Jirgin soji ya kashe ’yan sa-kai 20 da ke fatattakar ’yan bindiga a Zamfara An lakaɗa wa Mataimakin Firinsifal duka saboda hana satar a jarabawa Binciken farko ya nuna cewa mahaifin ya lura...
Wani yaro ɗan shekara 15 ya rasa ransa bayan mahaifinsa ya harbe shi bisa kuskure, yana zaton biri ne. Wannan lamari mai ban tausayi ya faru ne a gonar magidancin inda shi da ɗan nasa suke aiki, a yankin Iye Ekiti da ke Ƙaramar Hukumar Ilejemeje ta Jihar Ekiti. Kwamishinan ’Yan Sanda na Jihar Ekiti, Joseph Eribo, ya tabbatar da faruwar lamarin a yau a Ado-Ekiti. Ya bayyana cewa manomin ya daɗe yana fama da hare-haren birai a gonarsa kuma ya kai bindiga domin kare amfanin gonarsa. Jirgin soji ya kashe ’yan sa-kai 20 da ke fatattakar ’yan bindiga a Zamfara An lakaɗa wa Mataimakin Firinsifal duka saboda hana satar a jarabawa Binciken farko ya nuna cewa mahaifin ya lura...
Wasu ’yan daba sun yi wa Mataimakin Firinsifal na wata makarantar sakandare dukan tsiya a wani mummunan harin da suka kai masa saboda ya hana wani ɗalibi satar jarabawa. A yayin da ake ci gaba da jarabawar kammala sakandare ta WASSCE da ake yi a halin yanzu ne, Mista Rotifa, mataimakin shugaban wata makaranta mai zaman kanta mai suna Child Development College da ke Akure, hedikwatar Jihar Ondo, ya hana ɗalibin satar amsa. Bayan haka ne ’yan daban sun tsare Mista Rotifa suka yi masa dukan kawo wuƙa bayan sun jawo shi daga motar ’yan sanda, kafin a ceto shi a kai shi asibiti. Lamarin ya faru ne bayan Mista Rotifa ya ƙwace wayar salula da wani ɗalibi ke amfani...
Ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Manchester United ta sanar da ɗaukar ɗan wasan gaban ƙasar Brazil Matheus Cunha daga Wolverhampton Wanderes akan kuɗi fam miliyan 62.5, Cunha zai zama ɗan wasa na farko da Ruben Amorim zai saya a wannan bazarar yayin da yake ƙoƙarin sake gina ƙungiyar da ta ƙare a mataki na 15 a gasar Firimiya, Manchester United za ta kammala yarjejeniyar ɗaukar Cunha da zarar an buɗe kasuwar saye da sayarwar yan ƙwallo a ƙasar Ingila. Ɗan wasan mai shekaru 26 ya rattaba hannu kan kwantiragin shekaru biyar a United tare da zaɓin ƙarin shekara, Cunha ya bar Wolves a matsayin ɗan wasa mafi tsada da ta taɓa sayarwa a tarihinta bayan da yarjejeniyar ɗaukar ɗan wasan ta...
Aƙalla mutane 20 ne suka mutu bayan wani hari da jiragen sama na sojojin Najeriya (NAF) ya kai domin fatattakar ’yan bindiga a a Jihar Zamfara. Jiragen sojin sun kashe wasu ’yan sa-kai bisa kuskure, a yayin da ’yan sa-kan suke ƙoƙarin fatattakar ’yan bindiga da suka kai hari a yankin Mani a Ƙaramar Hukumar Maru. Jiragen sojin sun kai hare-haren ne domin fatattakar ’yan bindiga da suka kai wa manoma hari a kan babura da rana tsaka. Mazauna yankin sun ce bayan ’yan bindiga sun sace manoma sama da 50 ne jirgin sojin ya amsa kiran gaggawa, amma aka samu kuskure ya kashe wasu ’yan sa-kai da ke ƙoƙarin fatattakar maharan. Bom ɗin Boko Haram ya kashe fasinjoji 9...
Aƙalla mutane 20 ne suka mutu bayan wani hari da jiragen sama na sojojin Najeriya (NAF) ya kai domin fatattakar ’yan bindiga a a Jihar Zamfara. Jiragen sojin sun kashe wasu ’yan sa-kai bisa kuskure, a yayin da ’yan sa-kan suke ƙoƙarin fatattakar ’yan bindiga da suka kai hari a yankin Mani a Ƙaramar Hukumar Maru. Jiragen sojin sun kai hare-haren ne domin fatattakar ’yan bindiga da suka kai wa manoma hari a kan babura da rana tsaka. Mazauna yankin sun ce bayan ’yan bindiga sun sace manoma sama da 50 ne jirgin sojin ya amsa kiran gaggawa, amma aka samu kuskure ya kashe wasu ’yan sa-kai da ke ƙoƙarin fatattakar maharan. Bom ɗin Boko Haram ya kashe fasinjoji 9...
A wani yunkuri na rage adadin yara da suka daina zuwa makaranta, Gwamnatin Jihar Kaduna ta kaddamar da shiri mayarda yara 200,000 zuwa makaranta a cikin shekaru hudu masu zuwa, karkashin shirin Reaching Out-of-School Children (ROOSC). An bayyana wannan shiri ne a wani taron bita na kwanaki biyu da aka shirya tare da haɗin gwiwar Save the Children. A cewar, wakilin Ma’aikatar Ilimi ta Jihar Kaduna, Salisu Baba Lawal shirin zai shafi dukkan ƙananan hukumomi 23 a faɗin jihar. “Wannan shiri na Gwamnatin Jihar Kaduna ne tare da haɗin gwiwar abokan ci gaba da masu aiwatar da ayyuka,” in ji shi. “Gwamnatin Jihar Kaduna ta samo lamunin tallafin kudi domin aiwatar da wannan shiri da...
A wani lokaci yau Litini ne ministan harkokin wajen Iran Abbas Araghchi zai fara ziyarar kwanaki biyu a kasashen Masar da Lebanon. Yayin ziyarar Araghchi zai gana da manyan jami’an Masar da na Lebanon domin tattauna dangantakar da ke tsakanin kasashen biyu dama rikicin yankin. Ziyarar Araghchi a Masar za ta gudana ne bisa gayyatar takwaransa na Masar Badr Abdelatty. Ana sa ran ministan harkokin wajen na Iran zai gana da shugaban Masar Abdel Fattah al-Sisi, da takwaransa Badr Abdelatty, da kuma wasu masu fada a ji a fannin tattalin arzikin Masar. Da yake karin haske kan manufar ziyarar, mai kula da harkokin Iran a Alkahira ya ce, rikice-rikicen yankin da suka hada da hare-haren wuce gona da iri na...
Kasashen Larabawa karkashin jagorancin Saudiyya sun bayyana rashin jin dadinsu ga Isra’ila, kan hana su ziyartar yankunan Falasdinawa Ministocin harkokin wajen kasashen Larabawa sun bayyana rashin jin dadinsu ga gwamnatin Isra’ila, game da rashin amincewa da tawagar kungiyar kasashen ta ziyarci yankin da aka mamaye a Gabar Yamma da kogin Jordan don tattaunawa da shugaban Falasdinawa. A wani taron manema labarai, ministan harkokin wajen Saudiyya, Yarima Faisal bin Farhan Al Sa’ud, ya ce matakin da Isra’ila ta dauka kamar watsi ne da tayin zaman lafiya. A dai tsara a wannan Lahadi ne ministocin kasashen Saudiyya, Hadaddiyar Daular Larabawa, Masar, Jordan, Qatar, da Turkiyya, karkashin jagorancin ministan harkokin wajen Saudiyya Yarima Faisal bin Farhan za su isa birnin Ramallah domin ganawa...
Iran ta gargadi kasashen yamma aka daukar duk wani irin mataki kan ta a daidai lokain da ake shirin gudanar da taron gwamnonin hukumar kula da makamashin nukiliya ta duniya a mako mai zuwa. Mataimakin ministan harkokin wajen kasar Iran mai kula da harkokin shari’a da na kasa da kasa ya yi watsi da rahoton da hukumar ta IAEA ta fitar kan shirin nukiliyar Iran na zaman lafiya, yana mai gargadin daukar matakin da ya dace. Kazem Gharibabadi ya yi wadannan kalamai ne, bayan da hukumar ta IAEA ta yi zargi a cikin wani rahotonta na sirri ga kasashe mambobinta cewa Iran ta gaza bayar da rahoton ayyukanta na nukiliya a wasu wurare uku da ba a bayyana ba, tare...
Jami’ai a Falasdinu sun ce akalla mutum 31 ne sukayi shahada sannan wasu sama da 150 sun jikkata, bayan wani hari da Isra’ila ta kai kusa da wurin rabon abinci a birnin Rafah. Dama shugaban hukumar MDD da ke kula da yan gudun hijirar Falasdinawa, Philippe Lazzarini, ya ce rabon kayan agajin ya zama tarkon mutuwa. Lamarin dai ya faru ne a kusa da wata cibiyar rarraba kayan abinci da gidauniyar agaji ta Gaza (GHF) ke gudanarwa, wani kamfani mai zaman kansa da ke samun goyon bayan Isra’ila da Amurka da kungiyoyin agaji na kasa da kasa suka yi suka. Kakakin kungiyar Hamas Sami Abu Zohri yayi Allah wadai da gwamnatin Isra’ila kan harin da ta aikata a rabon kayan...
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Shin wanne ya fi zafi – takaicin rasa matsuguni ko alhinin rashin sanin halin da ɗan uwa na jini yake ciki? Wannan ne halin da wasu al’ummomi a Ƙaramar Hukumar Mokwa ta Jihar Neja suke ciki, bayan da suka tsinci kansu tsamo-tsamo a tsakiyar wata mummunar ambaliyar ruwa. Wasu mutanen da dama dai sun yi batan dabo a wannan ibitila’i, wanda ya yi sanadiyyar rayukan mutanen da adadinsu ya haura 150. NAJERIYA A YAU: Yaya Girman Matsalar Rashin Tsaro A Shekaru Biyun Tinubu? DAGA LARABA: “Sai Na Tara Kudin Cin Abinci Na Nake Iya Siyan Audugar Al’ada” Shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci zai yi nazari ne a kan yadda wadannan dubban...
Mahukuntan kasar Saudiyya sun sanar da cewa a ranar hawan arfa na bana, za a fassara hudubar da za a yi da harsuna 34 daga cikinsu da akwai Hausa da filatanci. Wasu harsunan Afirka da za a fassara hudubar ta Arfa da su, sun hada yarabanci, Sawahili, Somali da kuma Amharic na kasar Habasha. A bisa sanarwar da kasar Saudiyya ta yi na ganin watan zulhijja, a ranar 27 ga watan Mayu, za a yi hawan Arfa a ranar 5 ga watan na Mayu.
Sa’oi kadai da su ka gabata jiniyar gargadi ta kada a cikin garuruwa da sansanonin ‘yan share wuri zauna 300 a HKI saboda makami mai linzami da mutane Yemen su ka harba. Kafafen watsa labarun ‘yan sahayoniya sun ambaci cewa; an rufe filin saukar jiragen saman a “Ben Gorion” da kuma dakatar da kai da komowar jiragen sama. Kafafen watsa labarun na HKI sun ambaci cewa; Miliyoyin mutane ne su ka gudu zuwa Mabuya. Wannan sabon harin dai na sojojin Yemen yana zuwa ne a karkashin abinda sojojin na Yemen su ka kira, kakaba takunkumi na sama da ruwa akan HKI, tare da yin kira ga kamfanonin jiragen sama da na ruwa da su kauracewa zuwa wannan haramtacciyar kasa. Filin...
Mataimakin shugaban kungiyar Iraniyawa masu bayar da kyautar gabban jikinsu ga mabukata, Umid Qabadi, ya bayyana cewa; A cikin shekaru 25 da su ka gabata, yadda ake kyautar gabban jiki domin yin dashe a duniya ya karu da kaso 70%, kuma Iran ce ta farko wajen yin dashen koda, har ma ana yi ma ta kirari da; Sarauniyar dashen koda.” A yayin wani taro na girmama masu bayar da kyautar gabban jikin nasu domin yi dashe ga mabukata a gundunar Qazwin, mataimakin shugaban kungiyar Umid Qabadi ya ce; Iran ce ta farko a duniya wajen yin dashen gabobi ga marasa lafiya mabukata. Qabadi ya yi ishara da wajabci ganin an bunkasa wannan al’ada ta bayar da gabobin jiki domin yin...
Sanatocin Arewa sun bayyana alhini da jimami kan haɗarin mota da ya yi sanadin mutuwar wasu daga cikin ‘yan wasan Jihar Kano da ke dawowa daga Gasar Wasanni ta Kasa da aka kammala a Jihar Ogun. A cikin wata sanarwa da Shugaban ƙungiyar Sanatocin Arewa, Sanata Musa Yar’adua ya sanya wa hannu, ƙungiyar ta miƙa ta’aziyyarta ga iyalan mamatan da kuma Gwamnatin Kano, inda ya bayyana lamarin a matsayin babban rashi ga ƙasa baki ɗaya. ‘Yan Wasan Da Tauraruwar Ronaldo Da Messi Ta Hana Su Haskawa Gwamnatin Kano Ta Ba Iyalan Mamatan Wasanni Tallafin Naira Miliyan Ɗaya Kowane Sanata Yar’adua ya yi addu’ar Allah ya jikan waɗanda suka rasu, ya kuma bai wa waɗanda suka jikkata fatan samun sauƙi cikin...
barka.” Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Lawan ya kuma jajantawa iyalan wadanda suka mutu da kuma wadanda suka samu raunuka daban-daban sakamakon fashewar. Ya kuma yi addu’ar Allah ya jikan wadanda suka rasu ya kuma ba su Aljanatul Firdaus. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Ya bayyana kamen na su biyo bayan kama wasu alhazai biyu – Ibrahim Umar Mustapha da Muhammad Siraj Shifado a filin jirgin sama na Mallam Aminu Kano, da ke Kano a ranar Litinin 26 ga watan Mayu. An kama mutanen biyu ne a lokacin da ake tantance fasinjojin jirgin na Ethiopian Airline ET 940 da zai tafi zuwa Jedda, ta kasar Saudiyya. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Haka kuma an yi zaratan ‘‘yan kwallo irin su Johan Cruyff da Eusébio da Gerd Müller mahaifin Muller na yanzu da Zinedine Zidane da Ronaldo na Brazil da sauransu amma tabbas ba a samu zazzafar muhawara ba saboda bbau kafafen sadarwa na zamani wadanda yanzu kusan su ne suka hura wutar zazzafar muhawarar a sassa daban-daban na duniya da ake Kallon kwallon kafa. A yanzu dai Messi ne ya fi lashe Ballon d’Or, inda yake da guda takwas: 2009, 2010, 2011, 2012, 2015, 2019, 2021 da 2023, sai Cristiano Ronaldo mai guda biyar: 2008, 2013, 2014, 2016 da 2017. Sannan Messi ya zo na biyu sau biyar, shi kuma Cristiano Ronaldo ya zo na biyu sau shida, sannan dukkansu sun...

Ministan Harkokin Wajen Iran Ya Tattauna Darakta-Janar Na Hukumar Kula Da Makamashin Nukiliya Ta Duniya
Ministan harkokin wajen Iran ya tattauna da Grossi kan sabbin abubuwan da suka shafi tattaunawar nukiliyar Iran Ministan Harkokin Wajen Iran Abbas Araqchi da Darakta Janar na Hukumar Kula da Makamashin Nukiliya ta Duniya Rafael Grossi sun tattauna batutuwan baya-bayan nan da suka shafi tattaunawar nukiliya da kuma dage takunkumin da aka kakabawa Iran a wata tattaunawa ta hanyar wayar tarho. A yayin tattaunawar, bangarorin biyu sun yi nazari kan sabon ci gaban da aka samu a shawarwarin nukiliyar da kuma dage takunkumin. Sun kuma tattauna rahoton da hukumar ta IAEA ta fitar kan Iran. Haka nan kuma yayin da yake ishara da yadda Iran ke ci gaba da ba da hadin kai ga hukumar ta IAEA, da aiwatar da...

Jamhuriyar Musulunci Ta Iran Ta Gargadi Hukumar Kula Da Makamashin Nukiliya Ta Duniya Da Wasu Kasashe
Iran ta gargadi hukumar kula da makamashin nukiliya ta duniya da wasu kasashe Mataimakin ministan harkokin wajen kasar Iran mai kula da harkokin shari’ar kasa da kasa Kazem Gharibabadi, ya gargadi hukumar kula da makamashin nukiliya ta kasa da kasa IAEA da wasu kasashen duniya kan ci gaba da bin tafarki maras kyau da suka yi a baya, yana mai jaddada cewa Iran za ta dauki natakin da ya dace daidai ayyukan da sauran bangarori suka dauka. Mataimakin ministan harkokin wajen kasar Iran mai kula da harkokin shari’a na kasa da kasa ya mayar da martani a jiya Lahadi kan rahoton babban daraktan hukumar kula da makamashin nukiliya ta duniya Rafael Grossi kan wasu batutuwan kariya da suka shafi Jamhuriyar...
Yanzu haka, akalla ana iya karbar sama da Naira miliyan 100 daga wannan PAYE a kowane wata. Wasu hanyoyin samun kudaden shiga, sun hada da haya na kasa (ground rent), harajin haya (tenement rate), da harajin wuraren kasuwanci. Har ma da noma, ana sa wa haraji a Suleja, duk da cewa; gwamnan jihar manomi ne. Ya dace gwamnati ta tabbatar da cewa; ana samar da kayayyakin more rayuwa masu inganci a Suleja, ko da don a samu karin haraji ne. Idan har gwamnatin tarayya ba ta yaba da sadaukarwar da Suleja ta yi ba, to akalla Gwamnatin Jihar Neja; ya kamata ta fi mayar da hankali wajen samar da ci gaba a Suleja, domin karrama gudunmawar da garin ke bayarwa...
Ma’aikatar lafiyar kasar Sudan ta bayyana cewa: Ana ci gaba da daukan matakan ganin an shawo kan ci gaba da yaduwar masifar kwalara a kasar Gidan talabijin na Al-Alam ya watsa rahoton cewa: A halin da ake ciki a fannin kiwon lafiya a birnin Khartoum fadar mulkin kasar bayan bullar cutar kwalara yana ta kokarin ya shawo kan matsalar tare da killace mutanen da suka kamu da cutar a wurare na musamman a babban birnin kasar Khartoum, rahotonni sun bayyana cewa: Cutar ta bazu cikin sauri a birnin. Sannan ma’aikatar lafiya ta Sudan da kungiyoyi da dama suna ci gaba da kokarin shawo kan cutar don kada ta zama annoba wadda za ta yadu zuwa jihohi da dama. Wakilin gidan...
Kungiyar Tattalin Arzikin Kasashen Yammacin Afrika ECOWAS, tare da haɗin gwiwar Kungiyar Haɗin Kan Masu Kiwon Gargajiya ta Afrika CORET, ta shirya taron horaswa domin ƙarfafa fahimta kan tsarin ciyar da ɗalibai a makarantu, musamman a cikin al’ummomin makiyaya a Jihar Kaduna. Da yake ƙaddamar da taron a Ladugga, cikin Karamar Hukumar Kachia ta Jihar Kaduna, Ko’odinetan Shirin na CORET, Dr. Abdu Umar Ardo, ya bayyana cewa wannan horo wani bangare ne na ƙoƙarin tallafa wa shirin ciyar da ɗalibai a wasu makarantun Fulani da aka zaɓa. Wannan shiri, wanda ke samun goyon bayan haɗin gwiwa daga Swiss Cooperation, na nufin tallafa wa makarantun Fulani da ke Ladugga a Kaduna da kuma Maigatari a Jihar Jigawa,...
Gwamna Yusuf wanda a halin yanzu yake kasar Saudiyya don gudanar da aikin hajjin 2025, ya bayar da umarnin ware ranar Litinin 2 ga watan Yunin 2025 a matsayin ranar hutu domin bai wa al’ummar damar yin jimami tare da yi wa wadanda suka rasu addu’a. Ya kuma yi kira ga limamai da daukacin al’umma a fadin jihar, da su yi addu’o’i na musamman ga wadanda abin ya shafa da kuma karfafa wa iyalansu da suka rasu. Gwamna Yusuf ya tabbatar da cewa, gwamnati na daukar matakan tallafawa wadanda suka jikkata da kuma iyalan wadanda abin ya shafa. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na...
Hon. Nasiru ya kara da cewa Gwamna Radda ya yi kokari wajen yaki da matsalolin tsaro wanda suka addabi Jihar Katsina, inda ya bayyana cewa ana samun sauki sosai a wannan bangare. Ya ce gwamnati ta gyara makarantu da asibitoci a fadin Jihar Katsina, inda aka maida su na zamani tare da daukar ma’aikatan lafiya da kuma malaman makaranta da yawansu ya kai 7,000, wanda ya ce ko haka aka tsaye suna da hujja da dalilin mara masa baya. Idan za a iya tunawa a makon da ya gabata ne, ‘yan majalisun tarayya guda 15 dukkansu na jam’iyyar APC suka ayyana Gwamna Radda a matsayin wanda za su goya baya a zaben 2027. Sai dai kuma ana dora ayar tambaya...
A nasa jawabin, shugaban kwamitin shirya musabakar karatun alkurani na karamar hukumar Igabi, Malam Abubakar Sadik Muhammad (Abu Asim), ya ce duk irin nasarar da kwamitin ya samu, ya samu ne bisa goyon bayan da Honarabul Yusuf Ibrahim Zailani yake ba su. Ya ce shi ne kashin bayan samun nasarar da suka yi a fadin duniya. Ya bukaci daukacin iyaye da su kara zage damtse wajen ganin ‘ya’yansu sun samu ilimi nagartacce da kuma sanya ido wajen kula da tarbiyyarsu. Haka zalika, kwamitin shirya musabakar karatun alkurani ya karrama Zailani da lambar yabo bisa irin gudummawar da yake bai wa addinin Musulunci a ciki da wajen Jihar Kaduna. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu...
Sam-sam hakan ba shi da wani alfanu domin yana kawo matsaloli da dama wanda babu lokacin lissafosu. Kalubalen da ka iya afkuwa kuwa shi ne; wadansu ‘yan matan ba sa tan-tance wadanda za su sa da wadanda ba za su saka ba, har da masu saka ‘yan’uwan miji, kawaye da ‘yan’uwa na cikin dangi duk a bi a cakuda su guri guda, kuma ba sa yin komai a lissafance ba sa tunanin a cikin yawan al’umman da ke ciki har da shaidani ciki ba, dan akwai wacce abu ya faru da ita daga bude group na biki (sabe the date) abu ya dawo babbar rigima har ta kai ga ‘police station’ kuma ba komai ya kawo hakan ba sai rarrabuwar...
Iran ta tabbatar da cewa ta samu shawarar da Amurka ta gabatar mata daga hannun kasar Oman game da shirin nukiliyar kasar na zaman lafiya da ake tattaunawa a kai. Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Araghchi ya tabbatar da cewa Iran ta samu wani bangare na shawarwarin daga Amurka daga Oman mai shiga tsakani kan batun a wani sakon da ya wallafa a shafinsa na X. Ya karbi sakon ne daga hannun takwaransa na Oman Badr Albusaidi, wanda ya gudanar da wata gajeriyar ziyara a Tehran. Saidai ministan harkokin wajen Iran din bai bayyana abinda shawarwarin ke kunshe da ba, amma ya jaddada cewa za a duba su a kuma mayar da amsa wacce ta yi daidai da muradin...
Bayanai na nuni da cewa gwamnatin Isra’ila ta hana tawagar ministocin harkokin wajen kasashen Larabawa da dama shiga gabar yammacin kogin Jordan da ta mamaye domin wani taro a birnin Ramallah. Isra’ila dai ta ce ba za ta amince da tawagar ministocin kasashen Larabawa karkashin jagorancin Saudiyya su ziyarci yankin Isra’ila saboda ta lura hukumomin Falasdinawan na shirin yin amfani da ziyarar ne wajen farfado da kiran samar da kasar Falasdinawa. Wani jami’in Isra’ila ya shaidawa tashar talabijin ta CNN a ranar Juma’a cewa gwamnatin sahyoniyawan ba za ta hada kai da hukumar Falasdinu ta PA ba da ke neman karbar bakuncin tawagar ministocin harkokin wajen kasashen Larabawa karkashin jagorancin Saudiyya. Jami’in ya bayyana ziyarar a matsayin tsokana, yana mai...
Wani rahoto da ofishin kula da ayyukan jin kai na Majalisar Dinkin Duniya ya fitar, ya nuna cewa Gaza na fuskantar bala’i mafi muni tun soma yaki a Zirin a watan Oktoban 2023. Wakilin Majalisar Dinkin Duniya na musamman kan hakkin bil adama a yankunan Falasdinawa da aka mamaye ya zargi gwamnatin Isra’ila da yin amfani da batun agajin jin kai da gangan domin ci gaba da aiwatar da munanan laifukan da take aikatawa a Gaza. Francesca Albanese a cikin wata sanarwa da ta fitar ta ce: “Dukkan wadannan matakan an boye su ne a karkashin sunan agaji don karkatar da hankulan kasashen duniya.” A wani labarin kuma Kakakin Majalisar Dinkin Duniya Stéphane Dujarric ya shaida wa manema labarai a...
Iran ta soki sabon rahoton da shugaban hukumar kula da makamashin nukiliya ta duniya IAEA ya fitar, tana mai cewa rahoto ne dake kunshe da tuhume-tuhume mara tushe kan shirin nukiliyar kasar. A wata tattaunawa ta wayar tarho da babban darektan hukumar kula da makamashin nukiliya ta duniya IAEA, ministan harkokin wajen Iran Abbas Araghchi ya bayyana cewa, Tehran za ta mayar da martani ga duk wani matakin da bai dace ba daga kasashen Turai da Amurka. Faransa, Jamus da kuma Ingila, tare da goyon bayan Washington, suna son yin amfani da wannan rahoto don aiwatar da wani tsari da zai ba da damar maido da takunkumin Majalisar Dinkin Duniya kan Iran. A cikin rahoton nasa, Rafael Grossi ya bayyana...
An watsa shirin bidiyo na musamman na bikin Duanwu na babban rukunin gidajen rediyo da talabijin na kasar Sin, wato CMG na shekarar 2025 a kafofin sadarwa masu yawa a yau Asabar, wato ranar bikin Duanwu. Shirin yana habaka al’adun gargajiya na bikin Duanwu ta hanyoyin fasahar kirkira, kamar wakoki, da wasan kwaikwayo, da raye-raye na fikira, da kide-kiden jama’a, da wasannin Kung Fu da sauransu.(Safiyah Ma) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Ƙungiyar Gwamnonin Jihohin Arewa ta bayyana ambaliyar ruwa mai tsanani da ta faru a Mokwa, Jihar Neja, a matsayin babbar ibtila’i, yana mai kira da a ɗauki matakan gaggawa don tallafi da hana sake faruwar hakan. Shugaban Kungiyar kuma Gwamnan Jihar Gombe, Muhammadu Inuwa Yahaya, ya bayyana haka a yayin mika ta’aziyyarsa ga gwamnati da al’ummar Jihar Neja kan ambaliyar da ta faru a ranar Laraba, 28 ga Mayu, 2025, sakamakon ruwan sama mai kamar da bakin ƙwarya da ya yi sanadin rasa rayuka, bacewar mutane, da lalacewar gidaje, gonaki, da kayan more rayuwa. Ya yaba da agajin gaggawa daga Gwamnatin Jihar Neja karkashin jagorancin Gwamna Mohammed Umaru Bago da kuma kokarin hukumomin agaji wajen aikin ceto da tallafa wa...
Bayan mintuna 90 na wasan ba tareda wani ya doke wani ba sai alkalin wasa ya bayar da damar bugun daga kai sai mai tsaron raga, Jamaica ta ci kwallaye 4 inda Nijeriya ta ci dukkan kwallaye 5 da yan wasan suka buga, hakan ya sa yaran na Eric Chelle suka lashe gasar Unity Cup ta bana da ta kunshi kasashen Ghana, Trinidad And Tobago, Jamaica da Nijeriya. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp

Hadin Gwiwar Sin Da Kasashe Masu Tasowa Ya Dade Da Zama Kan Gaba A Bangaren Hadin Gwiwar Sin Da Kasashen Waje
An gudanar da bikin cika shekaru 30 da kafuwar asusun hadin gwiwar kasashe masu tasowa na MDD a birnin New York, babban birnin Amurka. Yayin bikin, zaunannen wakilin Sin dake MDD, Fu Cong, ya fitar da jawabi cewa, bangaren Sin ya yaba da sakamakon hadin gwiwa mai inganci da asusun ke goyon baya. Kuma Sin za ta ci gaba tsayawa tsayin daka kan goyon bayan ginshikin ci gaban MDD, da goyon bayan ra’ayin bangarori daban daban na gaskiya da kuma daukar hadin gwiwar dake tsakanin Sin da kasashe masu tasowa a matsayin abin dake kan gaba a cikin hadin gwiwar da Sin ke yi da kasashen waje. An kafa asusun hadin gwiwar kasashe masu tasowa a shekarar 1995, wanda ofishin...
Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Aragchi ya bayyana cewa JMI ta gina shirinta na makamashin nukliya ne kan fahinta da kuma kundin tsarin mulkin kasar wanda yayi tir da mamaya da kuma babakere. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto ministan yana fadar haka a safiyar yau Asabar a hubbaren Imam Ruhullah Al-khomaini (q) wanda ya kafa JMI. Ministan da sauran manya-manyan ma’aikata a ma’aikatar harkokin wajen kasar sun je hubbaren Imam ne don jadda bai’a ko alkawali da shi kan tafiya a kan tafarkin da ya barsu a kai. A cikin wani wuri a Jawabinsa Ministan ya kara da cewa a cikin kundin tsarin mulkin JMI ya zo kan cewa Iran ba zata danne wata kasa...
Kamfanin Barakat, mai samar da magunguna a nan JMI ya kaddamarda sabbin magunguna har 23 wanda kamfanin ya samar a cikin gida daga ciki har da riga kafi mai suna HPV. Kamfanin dilancin labaran IP na kasar Iran ya bayyana cewa wannan ci gaban da kamfanin Barakat ya samu mataki ne mai girma a fagen samar da magungunan da kasar Iran take bukata a cikin gida. Kuma wannan zai bude kofar samar da magunguna ko riga kafi masu tsada da wuyan samu a duniya na cututtuka daji ko (cancer) a kasar. Ministan kiwon lafiya na JMI Mohammad Reza Zafarqandi, a jawabinda da ya gabatar a bikin gabatar da magungunan ya ce, gamayyar kamfanonin samar da magunguna na kasar Iran wato...
Kungiyar Gwamnonin Najeriya (NGF) ta bayyana alhininta bisa rasuwar wasu ‘yan wasa daga jihar Kano a wani hadarin mota. A cikin wata sanarwa da shugaban kungiyar kuma gwamnan jihar Kwara, AbdulRahman AbdulRazaq ya fitar, ya ce hadarin ya faru ne yayin da tawagar jihar ke dawowa daga gasar wasanni ta kasa da aka kammala a jihar Ogun. Kungiyar ta NGF ta mika ta’aziyyar ta ga iyalan ‘yan wasan, gwamnatin jihar Kano,da ma kasa baki daya. Kungiyar ta roki Allah Madaukakin Sarki da Ya ji kan ‘yan wasan, Ya kuma ba iyalansu hakurin jure wannan babban rashi. Ali Muhammad Rabi’u
A karon farko, rundunar tsaron Indiya ta tabbatar da cewa ta rasa wasu jiragen yaƙi a yayin arangama mai tsanani da suka fafata da Pakistan a farkon watan Mayu. Wannan sanarwa ta fito ne daga bakin Babban Hafsan Tsaro na Indiya, Anil Chauhan, a taron Shangri-La Dialogue, babban taron tsaro na Asiya, a Singapore. Tun da farko, jami’an Indiya sun yi ta musanta duk wata asarar jiragen sama a cikin wannan arangama, wanda aka fara ne bayan wani hari da aka kai wa masu yawon bude ido a yankin Kashmir da Indiya ke mulka a watan Afrilu, wanda Indiya ta dora alhakinsa kan Pakistan. Ita kuwa Pakistan, ta yi ikirarin cewa ta harbo jiragen Indiya da dama, ciki har da...
Kungiyar Hamas wacce take iko da zirin gaza ta bukaci masu shiga tsakanin Amurkawa su ngamtar da ita kan cewa HKI zata dakatar da yaki ta kuma fice daga zirin gaza. Amma shawarar da Steve Witkoff ya gabatar bata kunshi wani abu wanda zaia gamsar da kungiyar ta amince da wani sulhu ba. Jihad Taha kakakin kungiyar ya bayyana cewa Hamas tana nazarin shawarar da Witskoff ya gabatar da tsagaita wuta a gaza wanda ya amince da dakatar da wuta na wucin gadi sannan a sake komawa yaki da kuma shigo a kayakin agaji. Y ace shawarar bata ambaci ficewar sojojin HKI daga yankin ba. Taha ya bayyana cewa shawarar bata da wani abin dogaro wanda Hamas da kungiyoyin masu...
Shugaban hukumar bada agajin gaggawa a jihar Naija na tarayyar Najeriya NSEMA ya basa sanarwan cewa yawan mutanen da suka rasa rayukansu sanadiyyar ambaliyar ruwa a ranar Alhamis data gabata a karamar hukumar Mokwa ya kai 151 bayan an sake gano karin gawakin mutane 36. Jaridar Daily Trust ta Najeriya ta nakalto Abdullahi Arah yana cewa banda wadanda suka rasa rayukansu mutane 11 ne suka ji rauni. Sannan mutane 3018 suka kauracewa gidajensu sanadiyyar ambaliyar ruwa bayan ruwan sama na sa’oii masu yawa. Arah yace gidaje 503 ne suka rushe a jihar sannan wasu 265 suka lalace. Banda haka akwai gadoji biyu da hanyoyi biyu wadanda ruwan ya sharesu.
Hukumomin ƙasar Saudiyya sun sanar cewa a bana za a gabatar wa mahajjata huɗubar Ranar a cikin harsuna uku na Najeriya. Harsunan Najeriya guda uku da za a gabatar da Huɗubar Ranar Arfa da su sun ne Hausa da Fulatanci da kuma Yarbaci. Harsunan huda uku na daga cikin karin harsunan duniya guda 34 da hukumomin Saudiyya suka sanar cewa za a gabatar da Huɗubar a cikinsu.
Tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa kuma ɗan takarar shugaban ƙasa na Jam’iyyar PDP a zaɓen 2023, Atiku Abubakar, ya zargi gwamnatin Shugaba Bola Tinubu, da yin “amfani da talauci a matsayin makami” domin juya ’yan Najeriya. Da yake jawabi a Abuja ranar Asabar a wajen lacca na cika shekaru 60 da haihuwar tsohon Gwamnan Jihar Ribas, Rotimi Amaechi, mai taken “Amfani da Talauci a Najeriya,” Atiku ya yi zargin cewa gwamnati tana amfani da matsalar tattalin arziki don sarrafa ’yan kasa. Ya ce, “Abin da muke fuskanta a halin yanzu a Najeriya shi ne gwamnati tana amfani da talauci a matsayin makami.” Atiku ya yi nuni da bambancin yanayin rayuwa a yanzu da lokacin ƙuruciyarsa, inda ya ce a lokacin Kano...
Ƙungiyar Gwamnonin Nijeriya (NGF) ta bayyana baƙin ciki da alhini kan mummunan haɗarin mota da ya yi ajalin wasu ‘yan wasa daga jihar Kano, yayin da suke dawowa daga gasar wasanni ta ƙasa da aka kammala a jihar Ogun. Shugaban NGF kuma gwamnan jihar Kwara, AbdulRahman AbdulRazaq, ya fitar da wata sanarwa da ya sanya wa hannu da kansa a yau Asabar, yana mai miƙa ta’aziyyarsa ga iyalan mamatan da gwamnatin jihar Kano. Mutane 21 Sun Mutu A Tawagar Ƴan Wasannin Kano A Hatsarin Mota Ahmed Musa Ya Angwance Da Matarsa Ta 4 A Kano “Muna miƙa ta’aziyyar ga iyalan ‘yan wasan, gwamnatin jihar Kano da kuma ɗaukacin ma’abota wasanni a faɗin kasar nan,” in ji sanarwar. Gwamna AbdulRazaq ya...
Karatu, rubutu,da kuma dabarun lissafi wasu dabaru ne da ake samu ta hanyar iulimi. Wadannan dabarun suna bada dama ta dogaro da kai da kuma samarwa kai aiki. Karatu yana bude hanyar sanin ilimi da labarin duniya. Saboda mutane suna fara kasuwanci ne idan har za su iya kasafi,da kuma gane abubuwan da aka kashe a kalla. Ilimin iya karatu da rubutu,da kuma iya samar da hanayar da za aji ra’ayoyi,hakan na kara iya dogaro da kai da kuma samun a rika jin babu wata kasala ko faduwar gaba. Ilimi yana taimakawa mutane wajen yadda wasu daga zama Sanuwar ware. Yin makaranta yana koyawa mutane duk wani matakin da za su dauka ya kasance mai ma’ana, wannan kuwa yana sa...
Aƙalla mutum 20 ne aka tabbatar sun mutu sakamakon wani mummunan hatsarin mota da ya rutsa da tawagar Jihar Kano da ke dawowa daga gasar wasannin motsa jiki ta ƙasa (NSF) da aka kammala a Jihar Ogun. Lamarin na ban tausayi ya faru ne a ranar Asabar a garin Dakatsalle, kimanin kilomita 50 daga Kano, yayin da tawagar ke gab da isa gida. Rahotannin farko daga masu bada agajin gaggawa da shaidun gani da ido sun nuna cewa waɗanda suka rasa rayukansu a hatsarin sun haɗa da ’yan wasa da ɗan jarida, ma’aikatan lafiya da jami’an gudanar da harkokin wasanni. Shugaban ƙungiyar marubutan wasanni ta Najeriya (SWAN) reshen Kano, Zahraddeen Saleh, ya tabbatar da wannan mummunan lamari. Ya kuma ƙara...