Sin Ta Tsaurara Matakan Kula Da Kyamarorin Dake Bainar Jama’a Domin Kare Sirrikan Mutane
Published: 10th, February 2025 GMT
A yau Litinin, kasar Sin ta sanar da sabbin ka’idojin kyautata kare sirrikan jama’a yayin kare tsaron al’umma.
Firaministan kasar Sin Li Qiang ne ya rattaba hannu kan wata dokar majalisar gudanarwar kasar, domin fitar da ka’idojin, wadanda za su fara aiki daga ranar 1 ga watan Afrilu.
Ka’idojin na da nufin tafiyar da harkokin da suka shafi kula da tsare-tsaren kyamarorin da aka kafa domin tsaron al’umma da kare sirrika da hakkoki da muradu da ma bayanan daidaikun mutane.
এছাড়াও পড়ুন:
Sama Da Masu Sayayya Daga Ketare 220,000 Ne Suka Halarci Bikin Baje Kolin Canton Karo Na 137
Bikin baje kolin na wannan karo da ake gudanarwa a birnin Guangzhou dake kudancin kasar Sin daga ranar 15 ga watan Afrilu zuwa ranar 5 ga watan Mayu, an shirya shi ne cikin matakai uku. Matakin farko ya mayar da hankali ne kan masana’antu masu ci gaba, na biyu a kan ingantattun kayayyakin gida, na uku kuma a kan kayayyakin dake sa kaimi ga inganta rayuwa. (Mohammed Yahaya)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp