Atiku da Obasanjo suna ganawar sirri
Published: 10th, February 2025 GMT
Ɗan takarar shugaban ƙasa na Jam’iyar PDP a zaɓen 2023, Atiku Abubakar, ya yi ganawar sirri da tsohon Shugaban Ƙasa kuma tsohon uban gidansa, Olusegun Obasanjo.
Obasanjo da Atiku sun yi ganawar ne a yayin ziyarar da tawagar Atiku ta kai gidan Obasanjo da ke mahaifarsa a Jihar Ogun.
A ranar Litinin ne Atiku tare da rakiyarsa ciki har da tsohon Gwamnan Jihar Kuros Riba, Liyel Imoke, da tsohon Gwamnan Sakkwato Sanata Aminu Waziri Tambuwal da kuma Sanata Abdul Ningi mai wakiltar Bauchi ta Tsakiya.
Isar tawagar Atiku da tawagarsa gidan Obasanjo ke da wuya shugabannin biyu suka sanya labule domin ganawar sirri.
উৎস: Aminiya
এছাড়াও পড়ুন:
An kama tsohon minista kan zargin kisan kai domin tsafi a Nijar
Antoni Janar na Kotun Ɗaukaka Ƙara da ke birnin Yamai a Nijar, ya bayyana cewa an kama tsohon Ministan Harkokin Waje, Ibrahim Yacoubou, bisa zargin hannunsa a cikin wata aika-aika ta kisan kai domin yin tsafi.
A cewar Maazou Oumarou, lamarin ya samo asali ne daga wani binciken ’yan sanda da aka fara gudanarwa tun a ranar 29 ga Yuli, 2025.
KEDCO ya ƙaryata asibitin AKTH kan mutuwar majinyata saboda ɗauke wuta Dole sai mun tantance wa’azi kafin a yi —Gwamnan NejaYa bayyana cewa, an soma gudanar da binciken ne dangane da yunƙurin kisa a wani yanki da ke wajen birnin Yamai, lamarin da ya kai ga cafke ababen zargin a garin Dosso.
Wani mutum mai suna Mahamadou Noura ne ya bayyana cewa shi ne ya yi yunƙurin kisan, tare da wasu kashe-kashe guda shida da ya aiwatar a baya, bisa umarnin wasu mutane, ciki har da tsohon ministan Ibrahim Yacoubou.
Mutumin ya shaida wa mahukunta cewa ya aikata hakan ne domin yin tsafi da gawarwakin, a madadin wasu mutane da suka haɗa da: Issa Ali Maiga da Ismael Morou Karama da Elhadji Bilya da kuma Issa Seybou Hama.
TRT ya ruwaito cewa tuni dai an cafke duk ababen zargin, yayin da Kotun Ɗaukaka Ƙarar ta umurci ’yan sanda da su ci gaba da bincike tare da ɗaukar ƙarin matakan da za su tabbatar da gaskiya.
Sanarwar ta ce: “Manufar wannan mataki na shari’a ita ce a tattara cikakken rahoto da ke ƙunshe da dukkan abubuwan da suka faru, sannan a miƙa shi ga ɓangaren gurfanarwa.”
Mai shigar da ƙara a ɓangaren gwamnati ya ce, la’akari da girman wannan lamari, wajibi ne a gudanar da bincike cikin gaggawa.
Haka kuma ya buƙaci al’umma da su mutunta ’yancin kotu tare da bayar da cikakken goyon baya domin fayyace gaskiya.
Ana iya tuna cewa, Ibrahim Yacoubou na daga cikin manyan jami’an da aka kama bayan juyin mulkin Nijar na ranar 26 ga Yuli, 2023, sai dai daga bisani an ba shi beli na wucin gadi a cikin watannin baya.