Ba Laifi A Binciki Gwamnatin Mahaifina, Amma A Yi Da Zuciya Ɗaya – Bello El-Rufai
Published: 10th, February 2025 GMT
Abubuwan da ke faruwa a siyasar jihar a baya-bayan nan sun nuna cewa El-Rufai da Gwamna Sani suna takun saka. A watan Yunin 2024 ne Majalisar Dokokin Jihar Kaduna ta ba da shawarar a binciki El-Rufai kan zargin karkatar da kudaden al’umma.
Amma da yake magana a yayin tattaunawar, Bello ya ce, “Babu daya daga cikinsu (Sani da El-Rufai) da ya ba ni labarin rikicin; amma na fahimci cewa, komai ya wuce.
Da aka tambaye shi ko zai iya sasanta mahaifinsa da Sani, Bello ya ce, “Ba aikina ba ne. Aikina shi ne in mayar da hankali wajen taimaka wa al’ummar mazabar Kaduna ta Arewa.”
এছাড়াও পড়ুন:
Gwamnatin Zamfara Ta Nemi Karin Tallafi Ga ‘Yan Gudun Hijira
Gwamnatin Jihar Zamfara ta roki Hukumar Raya Kasashen Waje ta Kasa (FCDO), Premier Urgence Internationale (PUI), da sauran masu ruwa da tsaki da su kara tallafa wa ‘yan gudun hijirar da ke jihar.
Kwamishinan Bada Agaji na Jiha Alhaji Salisu Musa Tsafe ne ya yi wannan kiran a lokacin da yake jawabi ga mahalarta taron na kwana guda kan shirin ceton rayuka da karfafawa da kuma juriya (LEARP) wanda kungiyar FCDO ta dauki nauyin shiryawa a Abuja.
A wata sanarwa dauke da sa hannun Daraktan Yada Labarai na Ma’aikatar, Bashir Kabiru Ahmad, Kwamishinan ya bayyana cewa a halin yanzu jihar na karbar dubban ‘yan gudun hijira daga al’ummomi sama da 1,008 a fadin kananan hukumomin 14, kamar yadda aka gani a cikin rajistar zamantakewa na jihar.
Alhaji Musa Tsafe ya bayyana cewa, tallafin da ake bukata ya hada da bangarorin Rayuwa, Karfafawa, samun tallafin Kudi da Manufofi da sauran abubuwan da za a iya yi da nufin rage radadin halin da ‘yan gudun hijira ke ciki a jihar.
Alhaji Tsafe ya yabawa abokan aikin raya kasa bisa yadda suke ci gaba da tallafawa ‘yan gudun hijira da sauran marasa galihu a Zamfara.
A cewarsa, aikin da aka tsara domin aiwatar da shi da kungiyar Premier Urgence International (PUI) za ta yi zai kasance muhimmin taimako ga al’ummar jihar Zamfara.
Ya bayyana taron a matsayin wani ci gaba a kokarin jihar na inganta rayuwar ‘yan gudun hijira da marasa galihu musamman mata da yara.
Alhaji Tsafe ya tabbatarwa da abokan huldar cewa jihar Zamfara karkashin Gwamna Dauda Lawal ta samar da tsarin siyasa da samar da yanayin da kungiyoyin agaji ke gudanar da ayyukansu yadda ya kamata.
REL/AMINU DALHATU.