A rana Juma’a da ta gabata, aka kaddamar da gasar wasannin kankara ta nahiyar Asiya karo na 9, a birnin Harbin na lardin Heilongjiang na kasar Sin. Wannan gasa ta kasance babbar gasar wasannin kankara ta kasa da kasa karo na 2 da Sin ta karbi bakuncinta, biyo bayan gasar wasannin Olympics na lokacin sanyi da ta gudana a birnin Beijing na Sin, a shekarar 2022.

An ce, gasar wasannin kankara ta wannan karo ta samu halartar ‘yan wasa fiye da 1270 da suka zo daga kasashe da yankuna 34 dake nahiyar Asiya, alkaluman da suka kai matsayin koli a tarihi. Inda har wasu kasashen da ba sa samun yanayi mai sanyi da muhalli mai kankara a cikin gida, kamarsu UAE, da Vietnam, da Indonesia, da Thailand, da dai sauransu, su ma suka tura tawagogi su halarci gasar.

Wata babbar ma’ana ta gasar ta wannan karo, ita ce tabbatar da hadin kan kasashen nahiyar Asiya. Ko da yake tattalin arzikin nahiyar na ta samun ci gaba cikin matukar sauri cikin shekaru 50 da suka gabata, sauyawar yanayin al’amuran siyasa na duniya, da takarar da ake yi tsakanin kasashe daban daban, suna ci gaba da haifar da kalubale a nahiyar. Bisa la’akari da wannan yanayin da ake ciki, taken gasar wasannin kankara ta nahiyar Asiya ta wannan karo na “tabbatar da hadin kan kasashen nahiyar Asiya” ya nuna bukatar dake akwai, gami da burin jama’ar kasashen Asiya na karfafa zaman lafiya da ci gaban tattalin arziki a kasashensu.

A wajen bikin kaddamar da gasar wasannin kankara ta wannan karo, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gabatar da shawarwarin karfafa niyyar tabbatar da zaman lafiya, da ci gaban tattalin arziki, da cudanya, da kauna, tsakanin kasashen Asiya, gami da kasashen duk duniya baki daya, wadanda suka nuna yadda kasar Sin ke kokarin sauke nauyin dake wuyanta, na nemo wa duniya hanyar samun ci gaba mai dacewa, a matsayinta na wata babbar kasa. (Bello Wang)

উৎস: Leadership News Hausa

কীওয়ার্ড: gasar wasannin kankara ta ta wannan karo nahiyar Asiya

এছাড়াও পড়ুন:

Araghchi : Za’ayi Tattaunawar Iran da Amurka ta gaba a Rome bayan taron E3

Ministan harkokin wajen Iran Abbas Araghchi ya ce za a yi taro karo na hudu na shawarwari tsakanin Tehran da Washington kan shirin nukiliyar Jamhuriyar Musulunci ta Iran a birnin Rome na kasar Italiya a ranar Asabar mai zuwa.

M. Araghchi ya fadawa manema labarai a gefen taron majalisar ministocin gwamnatin kasar na mako-mako yau Laraba cewa, inda ya ce taron na Rome zai kasance gabanin wani taro a ranar Juma’a na tsakanin Tehran da kasashen Turan nan uku da ake wa lakabi da E3 wato – Ingila, Faransa da kuma Jamus wadanda suka sanya hannu kan yarjejeniyar nukiliyar Iran ta 2015.

Ya ce rawar da kasashen Turai uku ke takawa ta ragu sakamakon manufofinsu a tattaunawar da aka dade ana yi, don haka a shirye muke mu gudanar da zagaye na gaba na shawarwari da su a birnin Rome.

Babban jami’in diflomasiyyar ya kara da cewa, Tehran na da burin warware batun nukiliyarta cikin lumana.”

Da aka tambaye shi game da halin da ake ciki na baya-bayan nan na kudaden da Iran ta toshe saboda takunkumin da kasashen yamma suka kakaba mata, Araghchi ya ce daskararrun kudaden na daga cikin takunkumin da ya zama dole a dagewa iran.

Kawo yanzu Iran da Amurka sun yi tattaunawa har uku ta farko a Oman, ta biyu a Italiya sai kuma wace aka gudanar a ranar Asabar data gabata a Oman.

Dukkanin bangarorin na cewa akwai fata mai kyau a jerin tattaunawar da suka gabata.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Araghchi : Za’ayi Tattaunawar Iran da Amurka ta gaba a Rome bayan taron E3
  • Tarayyar Afirka ta dage takunkumin da ta kakabawa Gabon
  • Yadda ta kaya a wasannin kusa da na ƙarshe na Gasar Zakarun Turai
  • Karin Wata Kasa Da Bai San Ta Ba A Doron Duniya
  • Arsenal Da PSG: Wa Zai Yi Nasara A Gasar Zakarun Turai A Yau?
  • Boko Haram ta kashe masu zaman makoki 7 a Chibok
  • Shin Amurka Na Iya Komawa Kan Kadaminta A Matsayin Cibiyar Masana’antun Duniya?
  • Sama Da Masu Sayayya Daga Ketare 220,000 Ne Suka Halarci Bikin Baje Kolin Canton Karo Na 137
  • Yadda matar gwamna ta sa mata gasar haihuwar ’yan uku
  • Iran Da Rasha Sun Jaddada Yin Aiki Tare A Fagen Kiwon Lafiya