Kasashe 79 Sun Yi Watsi Da Matakin Trump Na Kakabawa Kotun ICC Takunkumi
Published: 8th, February 2025 GMT
Kasashe 79 na duniya sun yi watsi da matakin da shugaban kasar Amurka Donald Trump ya dauka na kakabawa kotun hukunta manyan laifuka ta duniya ICC takunkumi, suna masu cewa matakin na raunana tsarin dokokin kasa da kasa.
Wadannan kasashen da suka hada da Canada, Jamus, Faransa, Afirka ta Kudu da kuma Mexico, a wata sanarwar hadin gwiwa na cewa irin wadannan matakan na kara barazanar rashin hukunta masu manyan laifuka.
Har ila yau a cikin sanarwar, kasashen 79 sun jaddada cewa takunkumin da Amurka ta kakabawa kotun ta ICC na iya yin illa ga sirrin bayanan da suka shafi wadanda abin ya shafa, da shaidu da kuma jami’an shari’a, wadanda ‘yan asalin wadannan kasashe ne.
Sanarwar ta zo ne sa’o’i bayan da Trump ya sanya hannu kan wani umarni na zartarwa na sanya takunkumi na kudi da hana biza ga ma’aikatan ICC da iyalansu.
A sanarwar hadin gwiwa da kasashen sun nuna yin nadamar duk wani yunkuri na kawo cikas ga ‘yancin cin gashin kan kotun.
Shugaban Amurka Donald Trump a ranar Alhamis ya ba da izinin kakaba takunkumin tattalin arziki da tafiye-tafiye kan mutanen da ke aiki kan binciken kotun hukunta manyan laifuka ta kasa da kasa da ya shafi ‘yan kasar Amurka ko kawayenta irinsu Isra’ila.
Matakin dai ya zo daidai da ziyarar da firaministan Isra’ila Benjamin Netanyahu wanda kotun ICC ke nema ruwa a jallo dangane kan aikata laifukan yaki a zirin Gaza, ke ziyara a Amurka, saidai kotun ta yi ICC, ta ce wannan matakin ba zai katse mata hamzari ba wajen gudanar da aikinta.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Amurka ta sanya Najeriya cikin ƙasashen da ake yi wa Kiristoci kisan ƙare dangi
Gwamnatin Amurka ƙarƙashin Donald Trump ta sake sanya Najeriya cikin jerin “Ƙasashe Masu Matsala ta Musamman” saboda zargin yi wa Kiristoci kisan ƙare dangi.
Wannan zargi ya biyo bayan jawabin da Mataimakin Shugaban Najeriya, Kashim Shettima, ya yi a taron Majalisar Ɗinkin Duniya a kwanan baya.
Barcelona ta shiga zarwacin Victor Osimhen Za mu ci gaba da shirye-shiryen babban taronmu — PDPA lokacin taron Shettima ya bayyana halin da ake ciki a Gaza a matsayin abin tausayawa, inda ya hi kira da a tabbatar da zaman lafiya ta hanyar kafa ƙasashe biyu masu zaman kansu.
Bayan jawabin nasa, wasu ƙungiyoyi suka fara yaɗa labarin cewa ana yi wa Kiristoci kisan ƙare dangi a Najeriya, duk da cewa mutane da dama sun ƙaryata jita-jitar.
A ranar Juma’a, Trump ya wallafa wani rubutu a shafinsa na X, cewa Kiristoci na fuskantar barazana a Najeriya.
Ya yi iƙirarin cewar masu tsattsauran ra’ayi suna yi wa Kiristoci kisan kiyashi a Najeriya .
Ya umarci ɗan Majalisar Amurka, Riley Moore da shugaban kwamitin kasafin kuɗi na Majalisar, Tom Cole, su binciki lamarin, sannan su gabatar masa da rahoto.
Shugaban ya ƙara da cewa ƙasarsa ba za ta zuba ido yayin da irin wannan “ta’addanci” ke faruwa a Najeriya da sauran ƙasashe ba.
Ya lashi takobin cewar Amurka za ta ci gaba da kare Kiristoci a duniya baki ɗaya.
Bayan wannan furuci, wasu sun zargi Trump da amfani da matsalar tsaron Najeriya don samun goyon bayan siyasa.
Har yanzu Gwamnatin Najeriya ba ta yi martani a kan lamarin ba, amma jami’an gwamnati a baya sun bayyana cewa rikice-rikicen da ake fama da su a ƙasar suna da nasaba da ayyukan ta’addanci, fashi, da rikicin ƙabilanci, ba addini ba.
Kalmar “Ƙasa Mai Matsala Ta Musamman” na nufin ƙasashen da Amurka ke ganin suna take haƙƙin ’yancin addini, kuma hakan na iya sa wa ta ƙaƙaba wa Najeriya takunkumai.
Idan ba a manta Najeriya ta fara shiga jerin irin waɗanda ƙasashe tun a shekarar 2020.