Ba Mu Amince Da Yi Wa Masu Daukar Nauyin Ta’addanci Shari’a A Sirrance Ba
Published: 7th, February 2025 GMT
Hujjar mu a nan ita ce, kundin tsarin mulkin Nijeriya, sama yake da kowanne dan kasar da kuma sauran dokokin kasar, duba da cewa, kundin ya bayar da damar a yi Shari’ar a bisa adalci kuma a bayyane, ga wadanda ake tuhumar da aikata laifi.
Bugu da kari, dole ne mu tuhumi matakan da mahukuntan kasar suka dauka na yiwa wadanda ake tuhumar Shari’ar a, asirce.
Akwai dimbin tambayoyi a zukatan ‘yan Nijeriya wanda kuma suke bukatar amsa, misali, a ina ne aka cafke su? ta yaya ne, aka kama su? yaushe ne, aka gurfanar da su, a gaban Kotu? Shin an barsu sun dauki Lauyoyin da za su tsaya masu gaban Kotu? har tsawon wanne lokaci ne, suke ci gaba da fuskantar Shari’a kuma kan wanne laifi ne, Kotu ke tuhumarsu?, me ya sanya ake yi masu Sharia’a a, asirce?
Tabbas, ‘yan Nijeriya na bukatar amsar wadannan tambayoyin, duba da cewa, kamata ya yi, a ce, ana yin masu Shari’ar bisa bin ka’ida, ko dai mutum dan kasa ne ko kuma bakin haure ne, ya kamata a ce, ana yi masu Shari’ar a bayya ne.
Yi wa mutanen, Shari’ar a, asirce ya savawa ka’ida duba da cewa, kundin tsarin mulkin Nijeriya, ya tanadi a bai wa, duk wanda ake zargi, ‘yancin da yi masa adalaci, kan tuhumar da ake yi masa.
Wannan Shari’ar da ake yiwa mutanen a asirce, hakan ya jefa ‘yan Nijeriya a cikin bakin duhun, sanin hakikanin yadda Shari’ar ke tafiya, hujojin da aka gabatar a kansu a gaban Kotu tare da kuma cewar, wadanda Kotun ke tuhuma, a kan wanne takamaiman laifi ne, aka gurnar da su kuma wanne irin hukuncin da aka yanke masu.
Hakan ya nuna cewa, rashin bin ka’ida a yi masu Shari’ar, tare da taka dokar kasa da kuma take ‘yancin ‘yan Adam.
Kazalika, hakan ya sanya nuna rashin aminta da Gwamnatin Tarayya, na cewa, ko za yi hukuncin bisa gaskiya.
Abin tambaya a nan shi ne, ta yaya irin wadannan gungun tantiran ‘yan ta’addar, musamman ‘yan ta’addar Boko Haram da suka fara aikita ta’addancin su tun a 2009, a kuma ce wai za yi masu Shari’a asirce?
‘Yan Nijeriya na bukatar sanin shi wadanne mutane ne, ke taimakawa ‘yan ta’addar wajen aikata ta’asarsu.
A gafe daya kuma, ‘yan ta’addar na ci gaba da kai farmaki ga sansanonin dakarun soji tare da kuma hallaka su da kuma kashe sauran fararne Hula, ciki har da dattijai, mata da kuma yara, inda ta’asar ta su, ta mayar da yaran marayu, matan kuma suka zama zawarawa ba tare da sun aikatawa ‘yan ta’addar wani laifi ba.
‘Yan ta’addar, sun zama tamkar, wasu mala’ikun mutuwa sanadiyyar kisan da suke yi, hakan ya janyo tarwatsa mafarkin wadanda lamarin ya rutsa da su da kuma tarwatsa su, daga matsugunan su, da suka gada tun daga kaka da kakanni.
Har zuwa yau, ‘yan makarantar Boko, musamman ‘ya’ya mata ana ci gaba da yin garkuwa da su, a wasu sassan kasar nan, tare da kuma yadda ‘yan ta’addar ke tilasta su, su aure su da kuma sanya su a aikin bauta.
‘Yan Nijeriya na ci gaba da hadiye fishinsu duba da cewa, wadanda suka dauki nau’yin ‘yan ta’addar da suka aikata masu ta’asar, amma Gwamnatin Tarayya ta yi uwa ta kuma yi makarviya, wajen kin yiwa ‘yan ta’addar da masu daukar nauyinsu Shari’a a asirce.
A namu ra’ayin domin ‘yan Nijeriya su yi ammana da Shari’ar da ake yiwa wadnda ake tuhumar a, asirce, ya zama wajbi Gwamnatin Tarayaya ta bayyana su, ta hanyar wallafa sunayensu, hotunansu, kanannan hukumomin da suka fito da kuma jihohin su na haihuwa, irin laifin da suka aikata aka kaisu gidan kaso da kuma irin hukuncin da aka yanke masu, a cikin a Jaridun kasar.
Yin hakan zai bai wa kamfanoni masu zaman kansu yanke duk wata nau’in hada-hadar kasuwanci da su da kuma hana hukumomin gwamnati daukar su, aiki.
Muna shawartar Gwamnatin Tarayya cewa, da ta sake yin tunani, kan dabarun da ta dauka, na yiwa wadnada ake tuhumar, Shari’ar asirce.
Daukar wannan shawarar na da matukar mahimmanci, musamman domin a tabbatar da yin gaskiya da adalci tare da kuma kare kimar ‘yancin Adam da kuma girmama dokar kasa.
Hakazalika, Gwamnatin Tarayya, ta tabbatar da yi masu Sharia’r bisa gaskiya, a bar su, su dauki Lauyoyi da za su tsaya masu, kuma hujjojin da aka gabatar kan zarginsu, su kasance na gaskiya ne, wadanda kuma za a iya gabatarwa, a gaban Kotu.
Abu ne, mai kyau a yaki da ta’addanci, amma ya kamata a yi hakan, ta hanyar mutunta ‘yancin daidaikun mutane, tabbatar da yin gaskiya da adalci da kuma mutunta, ‘yancin ‘yan Adam.
Batun yi wa masu aikata ta’addanci Shari’a ko kuma masu daukar nauyin aikata ta’addanci a kasar nan a, asirce, abu ne da ya savawa turbar mulkin Dimokiradayyar Nijeriya.
কীওয়ার্ড: Shari a Gwamnatin Tarayya a yi masu Shari yan Nijeriya yan ta addar masu Shari a tare da kuma duba da cewa ake tuhumar
এছাড়াও পড়ুন:
Faransa Ta Bayyana Wuce Gona Da Irin ‘Yan Sahayoniyya Kan Falasdinawa Da Ayyukan Ta’addanci
Ma’aikatar Harkokin Wajen Faransa ta bayyana cewa: Laifukan da aka aikata a Yammacin Kogin Jordan na Falasdinu ayyukan ta’addanci ne
Ma’aikatar harkokin wajen Faransa ta tabbatar da cewa tashe-tashen hankula da laifuffukan da tsagerun yahudawan sahayoniyya suke yi a yammacin gabar kogin Jordan da aka mamaye sun zama ayyukan ta’addanci, biyo bayan kashe wani mai fafutukar yaki da mamayar da tsagerun ‘yan sahayoniyya suka yi.
Kakakin ma’aikatar harkokin wajen ya ce: “Faransa ta yi Allah-wadai da wannan kisan gilla da kakkausar murya, da kuma dukkan ayyukan ta’addanci da gangan da masu tsattsauran ra’ayi ke yi kan Falasdinawa, wanda ke karuwa a ko’ina cikin yankunan Gabar Yammacin Kogin Jordan.” Ya kara da cewa, wadannan ayyukan wuce gona da irin, hakikanin ayyukan ta’addanci ne.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Jagora: Iran Ta Bayyana Karfinta Da Jajircewarta A Yakin Kwanaki 12 Ga Duniya July 29, 2025 Mutum daya Yayi Shahada 4 Sun Ji Rauna Sanadiyar Hare-Haren HKI A Lebanon July 29, 2025 EU Tace Zata Dakatar Da HKI Daga Cibiyar Bincikenta Saboda Gaza July 29, 2025 Ma’aikatar Leken Asirin JMI Ta Ce Ta Gano Shirin Kashe Manyan Mutane 35 a kasar July 29, 2025 Najeriya: Likitoci a Lagas Sun Shiga Yajin Aiki July 29, 2025 Wani Dan Majalisar Iran Ya Yi Kira Ga A Yi Siyasar Kin Gabatar Da Bayanai A Tattaunawa Da Kasashen Turai July 29, 2025 Sojojin HKI Sun Ci Gaba Da Kashe Kawunansu July 29, 2025 Kasar Holland Ta Hana MInistocin HKI Biyu Shiga Cikin Kasarta July 29, 2025 Manjo Janar Musawi: Ko Kadan Ba Mu Yarda Da Amurka Ba July 29, 2025 Araqchi: Iran Zata Mayar Da Martanin Da Ba Zai Yiwu A Boye Ba Kan Duk Wani Harin Wuce Gona Da Iri Kanta July 29, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci