HausaTv:
2025-05-01@09:46:14 GMT

Daliban Kasar Bangaladesh Sun Kona Gidan Tsohon Shugaban Kasa

Published: 6th, February 2025 GMT

Rahotanni da suke fitowa daga kasar ta Bangaladesh sun ce, a jiya Laraba da marece ne wasu dalibai da sauran mutanen gari sun ka cinna wuta a cikin gidaje masu yawa, da su ka hada da na tsohon shugaban kasa Mujibur Rahman. Abinda yake faruwa yana nuni ne da dambaruwar siyasa da kasar take ci gaba da fuskanta da kuma rashin gamsuwar da mutanen kasar nunawa akan halin da ake ciki.

Masu bin diddigin abinda yake faruwa a cikin  kasar ta Bangaladesh suna cewa, kai hari a gidan Mujibur Rahman da ake girmamawa a fadin  kasar yana nuni da zurfin matsalar da kasar take ciki. Masu Zanga-zangar suna bayar da taken yin kira ga juyin juya hali a kasar a lokacin da suke yin kone-kone.

উৎস: HausaTv

এছাড়াও পড়ুন:

Ministan Harkokin Wajen Kasar Iran Ya Tattauana Da Shugaban Hukumar IAEA

Shugaban hukumar makamshin Nujkliya ta MDD ya zanda da ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Aragchi kan al-amuran da suka shafi shirin nukliyar kasar Iran da kuma tattaunawar da ake gudana tsakanin ta da Amurka.

Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta bayyana cewa a tattaunawa ta wayar tarho tsakanin jami’an guda biyu a jiya Lahadi, Grossi shugaban IAEA ya bayyana cewa ya ji dadin yadda JMI ta zabi tattaunawa da AMurka dangane da shirinta na makamashin Nukliya. Ya kuma bayyana cewa hukumarsa a shirye take ta gabatar da duk wani taimakon da JMI take bukata a yayin tattaunawar.

A nashi bangaren Abbas Araqchi ya bayyana cewa kasar Iran a shirye take ta bada hadin kai ga hukumar ta IAEA kamar yadda yarjeniyar NPT take bukata da kuma dokokin kasa da kasa.

Abbas ya fada masa inda aka kai ya zuwa yanzu a tattaunawa ba kai tsaye ba tsakanin Iran da Amurka, a biranen Mascat na kasar Omman da kuma Roma na kasar Italiya.

Ya zuwa yanzu dai kasashen biyu sun gudanar da taro har sau uku dangane da shirin Nukliyar kasar ta Iran, kuma bangarorin biyu sun bayyana amincewarsu da yadda tattaunawar take tafiya.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Dubban Mutanen Burkina Faso Sun Yi  Gangamin Nuna Goyon Bayan Shugaban Kasa Ibrahim Traore
  • Nazarin CGTN: Ana Kara Bayyana Rashin Gamsuwa Da Sabuwar Gwamnatin Amurka Daga Ciki Da Wajen Kasar
  • Jaridar The Guardian Mafi Yawan ‘Yan Gudun Hijiran Sudan Ne A Gidan Yarin Kasar Girka
  • Karin Wata Kasa Da Bai San Ta Ba A Doron Duniya
  • Sin Na Maraba Da Karin Abokai Daga Kasa Da Kasa Su Ziyarci Kasar
  • Shugaban Kasar Yana Maraba Da Masu Zuba Hannun Jari A Kasarsa Daga Kasashen Waje
  • Jiragen Yakin Amurka Sun Kashe Mutane Da Dama A lardin Sa’ada Na Kasar Yemen
  • Falasdinu: Mahmud Abbas Ya Nada Magaji Da Kuma Mataimakasa
  • Al-Shara Ya Ki Abincikewa Da Tsarin Tarayya Wanda Kurdawan Kasar Siriya  Suke Bukata
  • Ministan Harkokin Wajen Kasar Iran Ya Tattauana Da Shugaban Hukumar IAEA