‘Yan Sanda Sun Mika Bakin Haure 165 A Birnin Kebbi
Published: 6th, February 2025 GMT
Rundunar ‘yan sandan jihar Kebbi, ta kama wasu bakin haure 165 da aka ce sun fito ne daga kasashen da ke amfani da harshen Faransanci tare da mika su ga hukumar kula da shige da fice ta kasa dake jihar domin gudanar da bincike.
A cikin wata sanarwa da kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, SP Nafiu Abubakar ya fitar kuma ya mika wa gidan rediyon Najeriya a jihar Kebbi, ya ce, bisa rahoton bayanan sirri, an gano sama da mutum dari biyu a wani gida mai dakuna uku da ke unguwar Kuwait a cikin birnin Birnin Kebbi.
Sanarwar ta ce, tawagar jami’an ‘yan sanda da ke sashin binciken manyan laifuka (SCID) ne suka kai samame unguwar inda suka yi nasarar cafke mutane dari da sittin da biyar (165).
Ya bayyana cewa, yayin da ake gudanar da bincike, an gano cewa, dukkan wadanda ake zargin sun fito ne daga kasashen da Faransa ta yiwa mulkin mallaka da suka hada da Burkina Faso, Jamhuriyar Benin, Jamhuriyar Nijar, Mali da Ivory Coast.
A cewar sanarwar, bincike ya kara nuna cewa, wadanda ake zargin suna zaune ne a Najeriya ba tare da wasu takardu masu inganci ba kuma ana zarginsu da hannu a cikin shirin Qnet Ponzi.
Sanarwar ta ce, bayan kammala binciken farko da rundunar ta gudanar, an mika wadanda ake zargin bakin haure zuwa hukumar shige da fice ta kasa reshen jihar Kebbi, domin ci gaba da bincike da kuma daukar matakin da ya dace.
PR/ Abdullahi Tukur
উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa
এছাড়াও পড়ুন:
An Fitar Da Kudaden Farfado Da Sassan Birnin Beijing Da Bala’in Ambaliyar Ruwa Ya Shafa
Yau Talata, kwamitin kwaskwarima da raya kasar Sin, ya fitar da kudin Sin RMB yuan miliyan 200, kwatankwacin dalar Amurka miliyan 28, domin tallafawa wajen farfado da sassan birnin Beijing da bala’in ambaliyar ruwa ya shafa, musamman ma fannin sake gina ababen more rayuwar jama’a na sufuri, da samar da ruwan sha, da kiwon lafiya, da na hidimomin al’umma a gundumomin Miyun da Huairou, a kokarin ganin rayuwa ta dawo kamar yadda take a wuraren, an kuma dawo da ayyuka kamar yadda aka saba.
Ban da haka kuma, ma’aikatar kudi, da ma’aikatar lura da ayyukan gaggawa ta kasar sun zuba kudin Sin yuan miliyan 350, kwatankwacin dalar Amurka miliyan 49 don tallafawa biranen Beijing, da Tianjin, da lardunan Hebei, da Shanxi, da Jilin, da Shandong, da Guangdong, da Shaanxi da jihar Mongolia ta Gida, ta yadda za su samu zarafin gudanar da ayyukan ceto, da rage radadin bala’u, da kuma taimakawa wadanda bala’in ya shafa. (Tasallah Yuan)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp