Aminiya:
2025-11-03@04:12:34 GMT

An yi garkuwa da tsohon Shugaban Hukumar NYSC Janar Tsiga

Published: 6th, February 2025 GMT

’Yan bindiga su yi garkuwa da tsohon Shugaban Hukumar Masu Yi Wa Kasa Hidima (NYSC), Manjo-Janar Maharazu Tsiga (ritaya).

Rahotanni daga mahaifarsa Jihar Katsina na cewa maharan sun yi garkuwa da Janar Tsiga ne a ranar Laraba da dare.

Bayanan sun bayyana cewa ƙauyensu Tisga da ke ƙaramar hukumar Ƙanƙara ta Jihar Katsina ne maharan suka yi awon gaba da shi tare da wasu mutum shida.

উৎস: Aminiya

এছাড়াও পড়ুন:

An raba wa iyalan jami’an ’yan sandan da suka rasu a bakin aiki a Borno N63.4m

Rundunar ’yan sandan Jihar Borno ta raba zunzurutun kuɗi naira miliyan 63.4 ga iyalan jami’anta 84 da suka rasa rayukansu a bakin aiki.

Rundunar ta raba kudin ne a ƙarƙashin tsarin inshorar rayuwa da kuma tsarin kula da lafiyar iyali na Sufeto Janar na ’yan sanda.

 

An gudanar da rabon kuɗin ne a ranar Alhamis a Maiduguri babban birnin jihar kamar yadda Kakakin rundunar a jihar, ASP Nahum Kenneth Daso, ya bayyana a cikin wata sanarwa.

A cewar sanarwar, Kwamishinan ‘yan sanda na jihar, CP Naziru Abdulmajid, wanda ya wakilci Sufeto Janar na ‘yan sanda, IGP Kayode Egbetokun, shi ne ya gabatar da takardun cakin kudin ga iyalan waɗanda suka ci gajiyar tallafin.

“Harkokin da suka shafi jami’anmu da iyalansu ya kasance babban fifiko ga rundunar,” in ji CP Abdulmajid yayin taron.

Ya ce wannan shiri na nuna tausayi da rikon amana, da kuma jagoranci mai nagarta daga Sufeto Janar wajen girmama jaruman da suka sadaukar da rayukansu domin tabbatar da zaman lafiya da tsaron ƙasa.

Kwamishinan ya kuma yi kira ga iyalan da suka amfana da tallafin da su yi amfani da kuɗaɗen yadda ya dace, musamman wajen tallafa wa ilimi, kiwon lafiya, da jin daɗin rayuwar iyalansu gaba ɗaya.

Ya yaba wa Sufeto Janar bisa ci gaba da tsare-tsaren jin daɗin jami’an rundunar, yana mai bayyana su a matsayin muhimman hanyoyin da ke samar da agaji da kwanciyar hankali ga iyalan waɗanda suka rasa masoyansu.

A nata jawabin a madadin iyalan da suka amfana, Misis Nana Goni ta nuna godiya ga Sufeto Janar bisa goyon bayan da ya bayar, tana mai tabbatar da cewa za su yi amfani da kuɗaɗen yadda ya kamata don inganta rayuwar iyalansu.

Rundunar ta bayyana cewa wannan rabon tallafi ya sake tabbatar da jajircewarta wajen kula da walwala da mutuncin jami’anta da iyalansu, musamman waɗanda suka sadaukar da rayukansu wajen kare al’umma.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Dalilin Da Ya Sa Hukumar NIWA Ta Fara Gyaran Hanyoyin Ruwa A Jihar Legsa
  • Dalilin Gwamnatin Jihar Kuros Riba Na Raba Wa Manoma Taraktoci
  • An yi garkuwa da Mataimakin Shugaban Majalisar Dokokin Kebbi
  • Gwamnatin Jigawa Za Ta Gina Gidaje 52 A Babban Birnin Jihar
  • ’Yan bindiga sun sace fasinjoji a cikin motocin bas a Kogi
  • Rundunar Sojin Nijeriya Ta Shirya Wa Janar Musa Faretin Gama Aiki
  • An raba wa iyalan jami’an ’yan sandan da suka rasu a bakin aiki a Borno N63.4m
  • NPA Da Ƙungiyar Injiniyoyi Ta Yi Haɗaka Don Bunƙasa Tashoshin Jiragen Ruwa
  • Shugabannin Kudancin Kaduna za su karrama Janar  Christopher Musa 
  • Ranar Foliyo Ta Duniya: Muna Fatan Ganin Karshen Cutar Foliyo A Jihar Katsina -Zulaihat Dikko Radda