Iran Ta Samu Ci Gaba A Kowane Fanni A Cikin Shekaru 40
Published: 2nd, February 2025 GMT
Jagoran juyin juya halin Musulunci na Iran, Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya yaba da ci gaban da Iran ta samu a fagage daban-daban, yana mai cewa kasar ta samu bunkasa a dukkan bangarori cikin shekaru 40 da suka gabata.
Iran ta yau ba Iran ce ta shekaru 40 da suka gabata ba – mun ci gaba ta kowane fanni,” in ji shi.
Jagoran ya jaddada cewa “Abin da ya bambanta Iran da sauran al’ummomi da yawa shi ne jajircewar mutanen kasar na yin Allah wadai da Amurka a matsayin mai zalunci, makaryaciya, mayaudariya da girman kai.”
Jagoran ya bayyana hakan ne a wata ganawa yau Lahadi tare da mahardatan musabaka ta Al’kur’ani mai tsarki karo na 41 da aka gudanar a Tehran babban birnin kasar Iran.
Har ila yau Ayatullah Khamenei ya jinjinawa irin sadaukarwar da kungiyoyin gwagwarmayar Falastinawa suke yi kan gwamnatin Isra’ila.
“In Allah ya yarda, Gaza za ta yi galaba a kan gwamnatin Sahayoniya,” in ji shi.
Ayatullah Khamenei ya jaddada nasarar da al’ummar Gaza suka samu kan gwamnatin sahyoniyawa da gwamnatin Amurka a matsayin misali na tabbatar da abin da ake ganin ba zai taba yiwuwa ba.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Iran ta sha alwashin ci gaba da aiwatar da manufofinta na raya dangantakarta da Nijar
Iran ta sha alwashin ci gaba da aiwatar da manufofinta na raya dangantakarta da Jamhuriyar Nijar.
Mataimakin shugaban kasar na farko Mohammad-Reza Aref ya ce Iran na ci gaba da aiwatar da manufofinta na raya dangantakarta da Nijar da sauran kasashen nahiyar Afirka bisa tsarin juyin juya halin Musulunci.
Aref ya bayyana hakan ne a lokacin da yake ganawa da ministan man fetur na kasar Nijar Sahabi Oumarou wanda ke Tehran, inda yake jagorantar wata tawaga, domin halartar taron hadin gwiwar tattalin arzikin Iran da Afirka karo na uku.
Ya ce da gaske ne gwamnatin Iran mai ci a yanzu tana son raya dangantakar da ke tsakaninta da kasashen Afirka ciki har da Nijar dangane da batutuwan da suka dace.
Ya kara da cewa, “Kasancewar manyan jami’an Nijar a taron da kuma kwamitin hadin gwiwa wani mataki ne mai ban sha’awa na inganta hadin gwiwa tsakanin kasashen biyu.”
Mataimakin shugaban kasar ya jaddada cewa, bunkasa alaka da Nijar abu ne mai matukar muhimmanci, “idan aka yi la’akari da matsayinta kan ci gaban yanki da na kasa da kasa da kuma ra’ayi daya kan batutuwan Falasdinu da Lebanon.”
A yayin da yake tsokaci ga kiran da ministan na Nijar ya yi na inganta alaka a fannin noma, man fetur, da makamashi mai dorewa, Aref ya bayyana wadannan fannoni guda uku a matsayin muhimman batutuwan da suka shafi dangantakar Iran da Nijar, wadanda ya ce kwamitin hadin gwiwa zai duba su.
Yayin da yake tsokaci kan dangantakar tattalin arziki, ya ce, ya kamata kamfanoni masu zaman kansu na kasashen biyu su zuba jari don ciyar da matakin hadin gwiwa zuwa matsayi mafi girma.