HausaTv:
2025-08-01@06:54:10 GMT

Masar Ta Yi Kira Ga HKI Da Ta Janye Sojojinta Daga Kudancin Lebanon

Published: 2nd, February 2025 GMT

Ma’aikatar harkokin wajen kasar Masar ta fitar da sanarwa da a ciki ta bukaci Isra’ila da ta janye sojojinta daga kudancin Lebanon tana mai cewa wannan wani abu ne mai matukar muhimmanci.

Ministan harkokin wajen kasar ta Masar Badar Abdulatif ya ce, wajibi ne ga Isra’’ila da ta janye sojojin nata daga Lebanon ba tare da wani sharadi ba, domin ba za a kyale ta akan koda taku daya na kasar Lebanon ba.

A karkashin  sharadin tsagaita wutar yaki da aka yi a ranar 27 ga watan Nuwamba na 2024, Isra’ila za ta janye sojojinta daga cikin kasar ta Lebanon a ranar 26 ga watan nan na Janairu.

Ya zuwa yanzu dai an tura sojojin Lebanon da kuma na MDD a cikin garuruwan dake kan iyaka da Falasdinu dake karkashin mamaya,sai dai duk da hakan HKI tana ci gaba da zama a cikin wasu gargruwan na wannan yankin.

A makon da ya shude ne dai Amurka da kuma gwamnatin Lebanon su ka karawa Isra’ila wa’adin zuwa 18 ga watan Fabrairu domin su janye daga kasar.

Ministan harkokin wajen kasar ta  Masar ya ce, ci gaba da zaman sojojin HKI a cikin Lebanon ya sabawa doka, kuma babu wani dalili da zai sa ta rika kai wa farafen hula hare-hare.

উৎস: HausaTv

এছাড়াও পড়ুন:

 Wani Dan Majalisar Iran Ya Yi Kira Ga A Yi Siyasar Kin Gabatar Da Bayanai A Tattaunawa Da Kasashen Turai

Dan majalisa mai suna muhammad Mirzai ya ce; Kasashen turai sun zaku, akan su sami bayanai akan girman asarar da aka yi wa cibiyoyin Nukiliyar Iran don haka ya zama wajibi Iran din ta yi amfani da siyasar barinsu a cikin duhu.

A yayin zaman da majalisar shawarar musulunci ta Iran ta yi a yau Talata, dan majalisar ya kuma yi bayani akan kallafaffen yakin kwanaki 12, ya yi ishara akan yadda HKI ta yi amfani da kirkirarriyar fasaha da kuma wasu hanyoyi na leken asiri,amma duk da haka ta ci kasa, saboda jagoranci mai cike da fasaha na jagora, da kuma yadda al’ummar kasar ta yi tsayin daka da goyon bayan tsarin musulunci.

Haka nan kuma ya ce; Daga cikin manufofin da HKI ta Shata cewa za ta cimmawa a yayin yakin, shi ne samar da sauyi a cikin wannan yankin, shi ya sa da dama daga cikin hukumomin kasashen larabawa su ka fahimci cewa raunana Iran yana nufin raunana kasashensu.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  •  Shugaban Kasar Lebanon Aun Ya Ce Mun Aike Wa  Amurka Sakwanni Akan Dakatar Da Hare-haren HKI
  • Hare-hare: ’Yan bindiga sun raba mutum 5,000 da muhallansu a Katsina
  • Malta Zata Amince da Samuwar Falasdinu a Cikin Watan Satumba Mai Zuwa
  • Amurka Ta Ce HKI Ba Zata Fice Daga Kasar Lebanon Ba Sai An Kwance Damarar Hizbullah
  • DAGA LARABA: Dalilan al’ummomi na rungumar gwaji kafin aure
  • Fiye Da Kamfanoni 30,000 Masu Zuba Jari Daga Waje Aka Kafa A Sin A Rabin Farkon Bana
  • Remi Tinubu ta bai wa waɗanda harin Benuwe ya shafa tallafin Naira biliyan ɗaya
  • Remi Tinubu ta ba da tallafin Naira biliyan ɗaya ga waɗanda harin Benuwe ya shafa
  • Gwamnatin Zamfara ta amince da naɗin sabon Sarkin Katsinan Gusau
  •  Wani Dan Majalisar Iran Ya Yi Kira Ga A Yi Siyasar Kin Gabatar Da Bayanai A Tattaunawa Da Kasashen Turai