Yadda Khalifan Sheikh Ibrahim Inyass ya yi wa Tinubu addu’ar nasara
Published: 1st, February 2025 GMT
Shugabannin Ɗariƙar Tijjaniyya bisa jagorancin Khalifa Sheikh Muhammad Mahi Inyass, sun ziyarci Shugaba Bola Ahmed Tinubu a fadarsa.
A yayin ziyarar, Khalifan Sheikh Ibrahim Inyass kuma ɗansa, Khalifa Sheikh Muhammad Mahi, da tawagarsa sun halarci Sallar Juma’a tare da Shugaba Tinubu a Fadar Shugaban Ƙasa.
Malaman sun kuma gudanar da addu’o’in neman taimakon Allah da zaman lafiya da kwanciyar hankali da ci-gaba da kuma albarka ga Najeriya.
Khalifa Muhammad Mahi Inyass, ɗa ga Jagoran Tijjaniyya Sheikh Ibrahim Inyass, ya jinjina wa Gwamnatin Tinubu, inda ya yi wa shugaban ƙasa addu’ar samun nasara da ƙarin basira da nasara a shugabanci domin kawo gagarumar ci-gaba a Najeriya.
Masu yi wa ƙasa hidima za su karɓi N77,000 daga Fabrairu – Shugaban NYSC ’Yan bindiga sun kashe mutum 3 sun sace 24 a ZamfaraKhalifa Mahi Inyass ya shaida wa manema labarai cewa tawagar ta taso ne musamman daga ƙasar Senegal, mahaifar Sheikh Ibrahim Inyass, domin halartar Maulidin Tijjaniyya na Sheikh Inyass na wannan shekara.
Ya ba wa Shugaba Tinubu tabbacin goyon baya da addu’o’i musamman daga mabiya ɗarikar Tijjaniyya sam da miliyan 400 da ke Najeriya da sauran wurare.
’Yan tawagar sun haɗa da Sheikh Ibrahim, babban ɗan Sheikh Dahiru Usman Bauchi, da dai sauran shugabannin Ɗariƙar Tijjaniyya.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Darikar Tijjaniyya Inyass Mahi Ibrahim Inyass Tijjaniyya Sheikh Ibrahim Inyass
এছাড়াও পড়ুন:
Microsoft ya ƙwace shafukan wasu kamfanoni 340 a Najeriya
Kamfanin Microsoft ya sanar da ƙwace shafukan yanar gizo na wasu kamfanoni 340 a Najeriya bayan samunsu da laifin sarrafa fasahohin kamfanin ba bisa ƙa’ida ba, musamman satar bayanan mutane.
Sanarwar da Microsoft ya fitar ta ce matakin ya biyo bayan wani umarni da wata kotu a Amurka ta bayar tun a farkon wannan wata, wadda ta bai wa kamfanin damar ɗaukar matakin ladabtarwa ga waɗanda ke amfani da fasaharsa ba tare da izini ba.
An kama ɗaya daga cikin manyan kwamandojin IPOB An tattauna yadda za a inganta walwalar malamai a GombeSteven Masada, mataimakin shugaban sashen lauyoyi na Microsoft da ke kula da laifukan intanet, ya bayyana cewa waɗannan kamfanoni sun ɗauki bayanan abokan hulɗarsu sama da 5,000, inda suka yi amfani da shafukan kutse domin samun bayanan sirri.
A cewarsa, ɗaya daga cikin shafukan da suka fi haddasa damuwa shi ne wani da ake kira Raccoon0356, wanda ke da mabiya fiye da 850 a manhajar Telegram. Wannan shafi ne ke bai wa wasu damar samun kayan aikin kutse don shigar bayanan sirri na Microsoft da wasu hukumomi.
Microsoft ya bayyyana Joshua Ogundipe, mazaunin Najeriya a matsayin wanda ke jagorantar wannan shafi da ke kan manhajar Telegram, kuma bai bayar da amsa a saƙon da aka aike masa ba, don ya kare kanshi game da ayyukan da kamfanin ya ce yana aikatawa.
Kamfanin na Microsoft ya ce ya gano yadda Joshua ya jima tare da ƙwarewa wajen satar bayanan mutane, inda a tsakanin 12 zuwa 28 ga watan Fabrairun wannan shekara, ya yi kutse a shafukan hukumomi sama da 2,300, mafi yawansu na Amurka.