Aminiya:
2025-06-15@21:34:29 GMT

Gwamna Buni ya zama Shugaban Ƙungiyar Gwamnonin Tafkin Chadi

Published: 31st, January 2025 GMT

Gwamnonin tafkin Chadi da suka haɗa da Nijeriya da Nijar da Kamaru da Chadi, sun zaɓi gwamnan Jihar Yobe, Mai Mala Buni a matsayin sabon shugaban ƙungiyar gwamnonin yankin.

Sanarwar na cewar, an zaɓi Gwamna Buni ne a ranar Juma’a a ƙarshen taron ƙungiyar gwamnonin tafkin Chadi karo na 5 da aka gudanar a Maiduguri.

’Yan bindiga sun kashe mutum 3 sun sace 24 a Zamfara Direba cikin barasa ya murƙushe sojoji sun mutu a Legas

Tun farko shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ne wanda mataimakin shugabansa Kashim Shettima ya wakilta ya bayyana buɗe taron da gwamnatin Jihar Yobe ta shirya.

Gwamna Buni a jawabinsa na karramawa ya yaba wa shugaba Tinubu bisa yadda ya samar da jagoranci ga ƙasa da yankin a cikin mawuyacin hali.

Ya gode wa takwarorinsa Gwamnonin yankin tafkin Chadi, da wakilai da sauran masu ruwa da tsaki saboda halartar taron da kuma bayar da gudunmawarsu wajen samun nasarar taron.

“Ina miƙa godiya ta ga mai girma shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, bisa jagorancinsa da jajircewarsa wajen samar da zaman lafiya da tsaro da ci gaban yankin tafkin Chadi.”

“Ina da yaƙinin cewa, mun sanya zamanmu a nan a cikin ‘yan kwanakin nan ya zama abin tunawa da albarka tare da yin adalci a kan taken taron “Sake gina tafkin Chadi: Ƙarfafa Ci gaban yankin, sadaukar da kai ga zaman lafiya, haɗin gwiwa tsakanin ƙasashen yankin, tsaro da ci gaba mai ɗorewa ga al’ummar yankin.” in ji shi.

Gwamnan ya bayyana fatansa yana mai cewa “a matsayina na mai masaukin baki ina fatan za mu aiwatar da dukkan darussa da ƙudurorin wannan taro  don ci gaban wannan yanki.

“Saboda haka, muna sa ran samun ƙarin haɗin gwiwa, tallafi da rabon albarkatun da ake buƙata don aiwatar da burinmu na gina kyakkyawan yanki mai wadata ga jama’armu.

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: Nijeriya da Nijar da Kamaru da Chadi

এছাড়াও পড়ুন:

Cikin Shekaru 2, Tinubu Ya Karɓo Bashi Fiye da Shugabannin Nijeriya 3 – Obi

Ya kammala da cewa, “Gwamnatin ta yi amfani da kuɗaɗe da yawa fiye da gwamnatocin Yar’Adua, Jonathan, da Buhari jimilla, amma babu wani cigaba da aka samu.”

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Cece-Kuce Ya Barke Bayan Ganduje Da Shugaban APC Na Arewa Maso Gabas Sun Nemi A Sauya Shettima A 2027
  • Takarar Tinubu: Rikici ya ɓarke a APC bayan Ganduje ya ƙi goyon bayan Shettima
  • Abokin Takarar Tinubu: Rikici ya ɓarke a APC bayan Ganduje ya ƙi goyon bayan Shettima
  • Martanin sojojin Iran ga Isra’ila zai zama mafi muni idan aka ci gaba da kai hari (Pezeshkian)
  • Cacar Baki Ta Kaure Tsakanin Fadar Shugaban Kasa Da Peter Obi Kan Tallafin Mai
  • Taron Koli Na Sin Da Kasashen Yankin Tsakiyar Asiya Karo Na Biyu Zai Ingiza Manufar Kara Dunkulewar Sassan Yankin
  • Masana Ilimin Nukiliyar Iran Sun Yi Shahada
  • Harin Isra’ila a kan Iran ya jefa yankin Gabas ta Tsakiya cikin zama dar-dar
  • Majalisar Tarayya Na Ƙoƙarin Zama Ƴar Amshin Shata – Saraki
  • Cikin Shekaru 2, Tinubu Ya Karɓo Bashi Fiye da Shugabannin Nijeriya 3 – Obi