Dangantakar Cinikayya Da Sin Ta Budewa Afrika Kofar Samun Ci Gaba
Published: 31st, January 2025 GMT
An bayyana dangantakar cinikayya tsakanin kasar Sin da Afrika a matsayin wadda ta taimaka wajen gaggauta ci gaba da samar da irin zamanantarwar da nahiyar ke bukata domin ta kasance cikin takara a duniya.
Muya Guo, shugabar sashen Sin a bankin Stanbic na Kenya ne ta bayyana haka yayin wata hira a Nairobin Kenya, inda ta ce dangantakar cinikayya tsakanin Sin da Afrika tare da jarin da kasar ta nahiyar Asiya ke zubawa, sun dora nahiyar kan tafarkin samun ci gaba, yayin da ta zamanantar da muhimman bangarori kamar na kere-keren kayayyaki.
A cewarta, makomar dangantakar tattalin arziki tsakanin Sin da Afrika na da haske, wadda ke samun karin kuzari daga jarin da bangarori masu zaman kansu da gwamnatin Sin ke zubawa, tana cewa, za a kara mayar da hankali kan ayyukan da suka shafi bangarorin makamashi da kere-kere da ababen more rayuwa.
Ta kuma bayyana cewa, karin kamfanonin Sin masu kera kayayyaki sun kafa sansanoninsu a kasar Kenya, inda suke daukar mutanen wurin aiki da koyar da fasahohi, lamarin dake bayyana kuzarin dangantakar tattalin arziki dake tsakanin bangarorin biyu. (Mai fassara: Fa’iza Mustapha)
এছাড়াও পড়ুন:
Nazarin CGTN: Ana Kara Bayyana Rashin Gamsuwa Da Sabuwar Gwamnatin Amurka Daga Ciki Da Wajen Kasar
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp