Isra’ila ta kashe Palasdinawa 10 ta kama 12 bayan musayar fursunoni 110
Published: 31st, January 2025 GMT
Kungiyar Hamas ta sanar da sunayen mutum uku da za ta mika wa kasar Isra’ila a Gaza a ranar Asabar a ci gaba da musayar fursunonin yaki tsakaninsu.
Bayan sako ’yan Isra’ila uku da ’yan kasar Thailand biyar a ranar Alhamis, Rundunar Qassam , sashen sojin Hamas ta sanar ranar Juma’a cewa wadanda kungiyar za ta sako su ne Ofer Kalderon da Keith Siegel da kuma Yarden Bibas.Hakan na zuwa ne bayan a cikin dare jiragen yakin Isra’ila sun kashe Palasdinawa 10 a sansanin ’yan gudun hijira na Jenin da ke garin Tammun da ke yankin Yammacin Kogin Jordan.
Kazailka ’yan sandan Isra’ila sun kama Palasdinawa 12 a yankin Gabashin Birnin Kudus a yayin da suke murnar sako ’yan uwansu 110 da Isra’ila ta yi daga gidajen yarinta a wani bangare na yarjejeniyar zaman lafiya a Zirin Gazan.
An ɗaure zawarawa a gidan yari kan aikata zina Tubabbun ’yan Boko Haram 5,000 sun koma cikin jama’aJami’an tsaro na Isra’ila na ci gaba da kai hare hare da tsare Palasdinawa ne duk yarjejeniyar zaman lafiyar da ake aiwatarwa a Zirin Gazan.
Kawo yanzu Palasdinawa 47,460 ne aka kashe, tare da jikkata wasu 111,580 tun daga ranar 7 ga Oktoban 2023 da aka fara wannan yaki.
An kashe wasu kimanin 1,139 a Isra’ila a lokacin da kungiyar Palasdinawa ta Hamas ta kai hai a ranar, inda ta yi garkuwa da wasu kimanin 200, ciki har da baki ’yan kasashen waje.
‘Yan sandan Isra’ila sun kama wasa Palasdinawa 12 da ke murnar sako ’yan uwansu 110 daga gidajen yarin Isra’ila a wani bangare na yarjejeniyar zaman lafiya a Zirin Gazan.
Jami’an tsaron Isra’ilar sun tsare mutanen ne a yankin Gabashin Birnin Kudus saboda suka murnar sako Palasdinawa da Isra’ila ta tsare a gidajen yarinta.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Isra ila Palasdinawa
এছাড়াও পড়ুন:
Shugaban hukumar zabe ta jihar Bauchi ya rasu
Shugaban Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta jihar Bauchi (BASIEC), Ahmed Makama Hardawa, ya rasu.
Marigayin ya rasu ne ranar Talata a Abuja, bayan ya yi fama da gajeruwar jinya.
Gwamnan Jihar Bauchi, Bala Mohammed ne ya tabbatar da rasuwarsa a cikin wata sanarwa ranar Laraba.
Muna tafe da karin bayani…