JMI Ta Cika Shekaru 46 Cib Da Nasarrar Juyin Juya Halin Mususlunci A Kasar, Wani Irin Ci gaba Ne Ta Samu A Cikin Wannan Lokacin
Published: 30th, January 2025 GMT
A ranar 11 Ga Watan Fabarainu na wannan shekarar ne JMI take cika shekaru 46 cib da samun nasara, da kuma kafa JM a Iran, wadanne nasarori ne kasar ta samu a cikin wannan lokaci?.
Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto kadan daga cikin nasarorin da kasar ta samu daga ciki.
01-Tsawon shekarun da Iraniyawa suke rayuwa ya karu daga 55 zuwa 76.
02-JMI ta iran ce kasa ta farko a duniya, a saurin ci gaba, a mafi yawan fannonin ilmi, wannan bisa rahoton manya-manyan cibiyoyin bincike da sanin hakan a duniya.
03-A bangaren ci gaban kayakin aikin likita, da kiwon lafiya, JMI ce ta farko a yankin gabas ta tsakiya sannan ita ce ta 17TH a duk duniya, shi ma bisa rahotannin cibiyoyin bincike da gano hakan a duniya.
04-JMI tana daga cikin kasashen duniya da suka sami ci gaban a zo a gani a bangarorin masu muhimmaci na aikin likita, wanda ake kira da turanci (stem cells) da kuma radio pharmaceuticals).
05-JMI ta shiga cikin kasashe 12 a duniya wadanda suke da dukkan abinda ake bukata na fasahar shiga cikin sararin samaniya. Sannan ta shiga cikin kasashe 5 a duniya wadanda suke da fasahar amfani da makamashin nukliya.
06-JMI ce kasa ta 13TH a fagen karfin soje, na 5 a fagen fasahar kera jiragen yaki wadanda ake sarrafasu daga nesa, sannan na 10 TH a fagen kera jirgen ruwa yaki mai tafiya karkashin ruwa, wato (subnerins ).
07-kungiyoyin wasanni motsa jiki mata kadai sun sami lambobin yabo kama daga zinari, azurka da tagulla har 7,961 a wasannin kasa da kasa. Sannan mata 335 ne suka zama alkalai a wasannin daban-daban a cikin shekara ta 2024 kadai.
Wannan kadannan Kenan daga irin ci gaban da JMI ta samu a cikin ci gaba a cikin al-amura daban daban a duniya.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
CMG Ta Kammala Gabatar Da Rahoto Kan Ganawar Shugabannin Sin Da Amurka
Babban rukunin gidajen rediyo da talabijin na Sin CMG, ya gabatar da labarin ganawar da aka yi jiya Alhamis tsakanin shugabannin Sin da Amurka a Busan na Korea ta Kudu, cikin harsuna 85. Kuma zuwa yau Juma’a, mutanen da suka karanta rahotanni masu alaka da ganawar ta hanyoyin watsa labarai na dandalin CMG sun kai miliyan 712. Haka kuma, kafafen watsa labarai na kasa da kasa 1678, sun wallafa tare da tura rahotanni da bidiyon labaran CMG na harsuna daban daban game da ganawar, har sau 4431.
Har ila yau a wannan rana, an gudanar taron tattaunawa na kasa da kasa kan bude kofa da kirkire kirkire da ci gaba na bai daya a kasar Uruguay, wanda CMG da hadin gwiwar ofishin jakadancin Sin dake kasar suka shirya a Montevideo babban birnin Uruguay. (Mai fassara: FMM)
ShareTweetSendShare MASU ALAKA