Jirage sun yi karo a sararin samaniya a Amurka
Published: 30th, January 2025 GMT
An zaƙulo gawarwakin mutane 19 bayan wani jirgin fararen hula da jirgin sojoji sun yi karo a sararin samaniya a ƙasar Amurka.
A cikin daren Laraba ne wani jirgin Kamfanin American Airlines dauke da fasinjoji 60 da ma’aikata hudu ya yi karo da wani helikwaftan sojojin Amurka, ƙirar Black Hawk, mai ɗauke da mutane a birnin Washington DC.
Jiragen da suka yi karo sun auka a cikin kogin Potomac, inda a halin yanzu ake aikin ceto, tun baya aukuwar hatsarin jiragen daga misalin ƙarfe 9 na dare.
Jami’an gwamnati sun tabbatar da cewa jirgin fasinjan na dauke da iyalai da kuma tawagar ’yan wasa Skating, bayan sun kammala atisaye.
DR Congo: Sojoji sun ƙaddamar da gagarumin hari kan ’yan tawayen M23 —Shugaba Tshisekedi Kungiyar NLC ta kira zanga-zanga kan ƙarin kuɗin wayaKafar yaɗa labaran ƙasar Rasha ta ce ’yan wasan Skating Dan ƙasar ma’aurata, Evgenia Shishkova da Vadim Naumov, suna cikin jirgin.
Ma’auratan sun lashe Gasar Skating na Duniya da aka gudanar a Amurka a shekarar 1994.
Sakataren Tsaron Amurka, Pete Hegseth, ya ce rundunar tsaron kasar ta fara bincike kan hatsarin jiragen, a yayin da Shugaba Donald Trump ya bayyana cewa hatsarin mummunan abu ne kuma da za a iya kauce wa.
Shugaban Hukumar Kashe Gobara na Birnin Washington DC, John A Donnelly Sr, ya ce aikin ceton yana da matukar sarkakiya, a yayin da aka dakatar da suka da tashin jirage zuwa ƙarfe 4 na yamma agogon GMT.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Hatsari jirage Washington DC
এছাড়াও পড়ুন:
Iran Ta Ce Amurka Ce Bayan Hare-haren Da Aka Kai Zahidan
Alkalin alkalan JMI Gholamhussain Muhsen Ejei, ya bayyana cewa, babu shakka gwamnatin kasar Amurka tana da hannu a hare-haren da ake dangantawa da kungiyar yan ta’adda ta Jaishul Zulm da ya faru a cikin wani kotu a garin Zahidan na lardin sistan Baluchistan a cikin yan kwanakin da suka gabata.
Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto alkalin alkalan yana fadar haka a lokacinda ya kai ziyara a gaisuwar wadanda abin ya shafa. Ya kuma bukaci mataimakinsa ya gabatar da dukkan bukatun da wadanda abin ya shafa suka gabatar.
A cikin maganar sa alkalin alkalan ya bayyana cewa, an halaka mutane uku a musayar wuta da yan ta’addan a kusa da kotun. Sannan JMI ta samar da shahidai 6 sannan wasu 22 suka ji rauni.
Yankin Sistan Baluchistan dai ya dade yana fama da hare-hare na wannan kungiyar, kuma tana da sansani a cikin kasar Pakistan wacce take makobtaka da kasar a kudu maso gabacin kasar.