Sin Ta Yi Kira Ga Kasa Da Kasa Su Ci Gaba Da Tallafawa UNRWA Wajen Gudanar Da Ayyukanta
Published: 30th, January 2025 GMT
Yayin da dokar haramtawa hukumar kula da ‘yan gudun hijirar Palasdinu ta MDD (UNRWA) yin aiki a Isra’ila ke gab da fara aiki, kwamitin sulhu na majalisar ya kira wata budaddiyar muhawara dongane da batun, inda wakilin Sin da wakilan sauran kasashe suka sake bayyana goyon bayansu ga hukumar.
Wakilin Sin na dindindin a MDD Fu Cong, ya yi kira ga Isra’ila da ta daina dakatarwa da kai wa hukumar hari, kana ta dakatar da zartar da dokoki masu ruwa da tsaki, yana mai kira ga kasashen duniya su ci gaba da goyon bayan hukumar wajen gudanar da ayyukanta da marawa MDD da kwamitin sulhun baya, wajen daukar matakan gaggawa domin tabbatar da hukumar ta gudanar da ayyukanta.
A cewar Fu Cong, goyon bayan hukumar na da alaka da kiyaye ikon tsarin dokokin kasa da kasa da kuma huldar kasashe da bangarori daban-daban da kiyaye rayukan miliyoyin ‘yan Gaza da kwanciyar hankalin yankin yamma da kogin Jordan da kuma warware batun Palasdinu a siyasance.
Fu cong ya kuma nanata cewa MDD da kwamitin sulhu na da nauyin daukar matakai na gagagwa da suka dace, domin tabbatar da hukumar na gudanar da ayyukanta da kuma kare yunkurin kakaba matakin ladaftarwa na bai daya kan al’ummar Gaza. (Mai fassara: Fa’iza Mustapha)
এছাড়াও পড়ুন:
CMG Ta Kammala Gabatar Da Rahoto Kan Ganawar Shugabannin Sin Da Amurka
Babban rukunin gidajen rediyo da talabijin na Sin CMG, ya gabatar da labarin ganawar da aka yi jiya Alhamis tsakanin shugabannin Sin da Amurka a Busan na Korea ta Kudu, cikin harsuna 85. Kuma zuwa yau Juma’a, mutanen da suka karanta rahotanni masu alaka da ganawar ta hanyoyin watsa labarai na dandalin CMG sun kai miliyan 712. Haka kuma, kafafen watsa labarai na kasa da kasa 1678, sun wallafa tare da tura rahotanni da bidiyon labaran CMG na harsuna daban daban game da ganawar, har sau 4431.
Har ila yau a wannan rana, an gudanar taron tattaunawa na kasa da kasa kan bude kofa da kirkire kirkire da ci gaba na bai daya a kasar Uruguay, wanda CMG da hadin gwiwar ofishin jakadancin Sin dake kasar suka shirya a Montevideo babban birnin Uruguay. (Mai fassara: FMM)
ShareTweetSendShare MASU ALAKA