An Watsa Bidiyon Dandanon Shagalin Murnar Bikin Bazara Na CMG A Karon Farko A Najeriya
Published: 28th, January 2025 GMT
A ranar 25 ga wata, agogon Najeriya, ofishin karamar jakadiya kasar Sin dake Legas, da tawagar Sinawa wadanda ke kasar, sun gudanar da jerin ayyuka don yin maraba da murnar bikin Bazara na shekarar maciji bisa kalandar gargajiyar Sinawa. An gudanar da bikin nune-nunen abinci, da nune-nunen kayayyaki, da liyafar maraba bi da bi, wanda ya samu halartar mutane sama da 2,000 da suka hada da Sinawa dake kasar da abokai ‘yan Najeriya.
Kafin an fara liyafar a maraice, an watsa bidiyon dandanon shagalin murnar bikin Bazara na shekarar maciji na babban gidan rediyo da talibijin na kasar Sin na CMG, Kyan hoton bidiyon mai kayatarwa kuma mai cike da ma’anar kimiyya da fasaha ya matukar burge bakin da ke wurin, ya kuma tada sha’awa mai karfi na yawancin baki ‘yan Najeriya, masu kallo sun kalli bidiyon a tsanake kuma sun yi kyakkyawar tafawa ma bidiyon. (Mohammed Yahaya)
এছাড়াও পড়ুন:
Jagora: Za’a Gaggauta Ci Gaba A Ilmi Da Fasahar Tsaron Sojojin Kasar
Jagoran juyin juya halin musulunci Imam Sayyid Aliyul Khaminae ya bayyana cewa JMI zata gaggauta ci gaba a fasahar tsaron kasa da kuma fasahar zamani a dukkan fagage bayan yakin kwanaki 12 da HKI da Amurka.
Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto Jagoran yana fadar haka a cikar kwanaki 40 da shahadar manya-manyan kwamandojin sojojin kasar da kuma masana fasahar Nukliya a kasar. Jagoran ya kara da cewa dukkan ilmomi tsaron kasa da kuma fasaha za su cilla da saura don samun ci gaba. A sakon da jagoran ya aikawa mutanen kasar ya yi tir da hare-haren da HKI da kuma Amurka suka kaiwa kasar Iran, sannan yay aba da sojojin kasar Iran kan duka mai karfin da suka yiwa makiya.
Yace: Babu shakka an yi rashin manya-manyan kwamandojin sojojin kasar Kamar Bakiri salami, Rashid Hajizadeh shadmani da sauransu, abun yayi mana nauyi, hakama mun rasa masana fasahar Nukliya Tehranchi da Abbasi, amma kuma muna godiyar All..makiya basu cimma mummunan manufofinsu a kan Iran ba. Yace: Manufar HKI na maida kasar Iran baya ya kasa kaiwa ga nasara,. A ranar Jumma’a 13 ga watan yunin da ya gabata ne jiragen yakin HKI suka kai hare-hare a wurare da dama a cikin nan birnin Tehran. Inda suka kai wadannan manya-manyan mutane ga shahada. Sannan kafin kasar Yakin wanda suka nemi a tsaida shi sun dauki darasi.