’Yan sanda sun yi ƙarin haske kan barazanar harin ’yan ta’adda a Kano
Published: 27th, January 2025 GMT
Rundunar ’yan sandan Jihar Kano ta yi ƙarin haske dangane da barazanar harin ’yan ta’adda da ta yi gargaɗin aukuwarsa a bayan nan.
Da yake yi wa manema labarai jawabi, Kwamishinan ’Yan sandan Kano, Salman Dogo Garba, ya ce sun ɗauki matakan da suka dace biyo bayan barazanar harin ’yan ta’adda musamman a yayin taron Maulidin Shehu Ibrahim Inyass na ƙasa da aka gudanar ranar Asabar a jihar.
“Mun ankarar da jama’a sannan muka ɗauki matakan da suka dace domin tunkarar lamarin,” in ji CP Garba.
Ya bayyana cewa wasu daga cikin waɗanda ake zargin dangane da lamarin sun tsere daga jihar a sakamakon bayanan sirri da rundunar ta tattara.
“Mun kuma samu nasarar cafke wani mutum guda da ya shigo Kano ya samu mafaka a wani coci.
“Haka kuma mun samu ababen fashewa da sauran kayayyakin da aka yi yunƙurin kai harin da su,” a cewar CP Garba.
Kwamishinan ya jaddada muhimmancin tattara bayanan sirri domin daƙile duk wata barazana da ƙoƙarin haɗin gwiwa tsakanin masu ruwa da tsaki wajen tabbatar da tsaro.
CP Garba ya kuma yi tsokaci irin ƙalubalen da suke fuskanta dangane da yadda ake siyasantar da duk wani lamari musamman a wurare irin Jihar Kano, sai dai ya nanata cewa za su ci gaba da sauke nauyin da ya rataya a wuyansu na tabbatar da kiyaye da doka da oda.
“Komai sai an siyasantar da shi a Jihar Kano hatta abincin da muke ci. Sai dai ina ƙara tabbatar da cewa rundunar ’yan sandan da nake jagoranta ba za ta yi ƙasa a gwiwa ba wajen tabbatar da tsaro a jihar nan.
“Tun daga kan iyaye da kakanni nake cikin ɗariƙar Tijjaniyya saboda haka ba zan gushe ba wajen zama jakada na zaman lafiya da tabbatar da tsaro ba.
Kwamishinan ya ƙara tabbatar wa al’ummar jihar cewa rundunar ’yan sandan za ta ci gaba faɗi tashin domin daƙile duk wata barazana da za ta kawo cikas ga zaman lafiya da tsaron jihar.
Ya buƙaci al’umma da suka kasance masu lura da sanya ido domin bai wa hukumomin tsaro haɗin kai na tabbatar da tsaro a jihar.
Ya kuma miƙa godiya ga duk waɗanda suke bai wa jami’an tsaro goyon baya na wanzar da aminci a jihar.
A bayan nan ne dai aka zargi rundunar ’yan sandan jihar da yunƙurin hana gudanar da Maulidin Shehu Inyass na ƙasa bayan gargaɗin da ta yi kan barazanar harin ’yan ta’adda a jihar.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Yan Sanda yan ta adda Jihar Kano tabbatar da tsaro barazanar harin yan ta adda
এছাড়াও পড়ুন:
Gwamnatin Kano ta gayyaci Mai Dubun Isa da Shehi Tajul-Izzi kan shirya muƙabala
Hukumar Tace Fina-Finai da Dab’i ta Jihar Kano ta haramta shirya duk wata muƙabala tsakanin mawaƙan yabon Annabi (S.A.W), tare da gayyatar mawaƙa Usman Maidubun Isa da Shehi Mai Tajul’izzi su bayyana a gabanta.
Hukumar ta kuma gayyaci mawaƙan ne tare da sauran waɗanda suka jagoranci muƙabalar da fitattun mawaƙan biyu suka yi ranar Litinin, da su bayyana a gabanta cikin sa’o’i 24.
Kukan al’umma kan lalacewar hanyar Dukku DSS ta maka Sowore da Facebook a Kotu kan cin zarafin TinubuHakan na zuwa ne ƙasa da kwana ɗaya bayan ɓullar wata muhawara da aka yi tsakanin Usman Maidubun Isa da Shehi Mai Tajul’izzi kuma ta karade shafukan sada zumunta, wacce hukumar ta bayyana a matsayin karya dokokin aikinta.
Shugaban hukumar, Abba El-Mustapha ne ya sanar da hakan ranar Talata, inda ya ce ɗaukar matakin wani yunƙuri ne na tabbatar da zaman lafiya, daidaito da bin doka tsakanin mawaƙan nishaɗi da na addini.
El-Mustapha, a cikin wata sanarwa da kakakin hukumar, Abdullahi Sani Sulaiman ya fitar, ya kuma ce an haramta duk wata nau’in muƙabala daga mawaƙan addini a jihar ba tare da izinin hukumar ba.
A yayin da yake ƙaddamar da wani kwamitin bincike da shugaban hukumar ya naɗa karkashin Daraktan Ayyuka na Musamman a hukumar, Isah Abdullahi, El-Mustapha ya umarci waɗanda aka gayyatar da su bayyana a gaban kwamitin domin amsa tambayoyi.
Hukumar ta ce shirya irin waɗannan muhawara ba tare da izininta ba ya saɓa doka kuma zai iya jawo hukunci mai tsanani ga wanda suka karya.
Hukumar ta kuma jaddada ƙudirinta na ci gaba da kula da ayyukan mawaƙan da masu nishaɗantarwa a faɗin jihar tare da yin kira ga jama’a da su zauna lafiya sannan su ci gaba da ba ta haɗin kai a ayyukanta.