Mutum Biyu Sun Mutu a Ruwa a Jihar Kano
Published: 27th, January 2025 GMT
Wani magidanci mai suna Rabiu Sani mai shekaru 30 ya rasa ransa bayan ya zame cikin wani tafki a lokacin da yake diban ruwa a garin Kunture da ke karamar hukumar Ungogo.
Jami’in hulda da jama’a na hukumar kashe gobara ta jihar Kano, Saminu Yusif Abdullah, ya tabbatar wa manema labarai faruwar lamarin a Kano.
A cewarsa, hukumar ta samu kiran gaggawa daga jami’in ‘yan sanda, Silas Munkaila, inda nan take aka tura tawagar ceto zuwa wurin.
Saminu ya yi nuni da cewa, duk da kokarin da suka yi, an tabbatar da rasuwar Rabiu.
Haka zalika, wata budurwa mai suna Binta da ke fama da damuwa da tabin hankali ta rasa ranta bayan ta fada rijiya a garin Danbare da ke karamar hukumar Kumbotso.
Jami’in hulda da jama’a ya bayyana cewa, an mika gawarwakinta ga iyayenta domin yi mata jana’iza kamar yadda addinin Musulunci ya tanada.
Saminu ya bayyana damuwarsa kan yadda matsalar nutsewar ruwa ke kara ta’azzara a Kano, ya kuma bukaci jama’a da su yi taka-tsan-tsan wajen samun ruwa a budaddiyar rijiya domin kare afkuwar irin wannan hadari.
KHADIJAH ALIYU/Wababe
উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa
এছাড়াও পড়ুন:
Gwamnatin Kano za ta sabunta masallacin da aka kona masallata 23 a kan N150m
Gwamnatin Jihar Kano ta amince da kashe Naira miliyan dari da hamsin da ɗaya da dubu dari takwas da sittin da uku (N151,863,895.97) domin sake gina wani masallaci da wani matashi ya cinna wa wuta a yayin da jama’a ke tsaka da sallar Asuba a cikin jam’i a Tiga Gadan da ke Karamar Hukumar Gezawa, a watan Mayun bara.
Aikin sabunta masallacin ya kunshi gina makarantar Islamiyya tare da ofis da bandaki da kuma rijiyar burtsatse mai amfani da hasken rana tare da tankin ruwa na sama.
Kwamishinan Yada Labarai da Harkokin Cikin Gida na Jihar Kano, Ibrahim Abdullahi Wayya, ya sanar amincewar sake gina masallacin ya biyo bayan alkawarin da Gwamna Abba Kabir ya yi a lokacin da ya ziyarci wurin da abin ya faru.
Ya yi kira ga mutanen kauyen Gadan da su saka wannan karimci ta hanyar bayar da goyon bayan da ake bukata don tabbatar da nasarar kammala aikin, da kuma samar da kariya ga sabbin gine-ginen.
Yadda kotu ta yanke wa wanda ya kona mutane a cikin masallaci hukuncin rataya a Kano Amarya ta kashe uwargida da wuka a Katsina An yanke wa wanda ya yi wa agolarsa fyaɗe ɗaurin rai-da-raiA ranar Litinin ne Babbar Kotun Musukunci ta yanke wa Shafi’u Abubakar hukuncin kisa ta hanyar rataya saboda kona masallacin, wanda ya yi sanadin mutuwar mutane 23.