Rundunar Sojin Najeriya ta 8 da ke Sokoto ta bayyana ayyukanta na zamantakewar jama’a na yammacin Afirka WASA, a matsayin muhimmin kayan aiki don wanzar da hadin kai da ci gaba a yankin yammacin Afirka.

 

Babban Kwamandan Rundunar, Manjo Janar Ibikunle Ajose ya bayyana haka a wajen taron na bana da aka gudanar a Bataliya ta 26 dake jihar Sokoto.

 

Ajose ya ce hukumar ta WASA tana baiwa hafsoshi da sojoji da iyalansu damar yin mu’amala cikin yanayi mai kyau.

 

Ya bayyana cewa, tarihin wannan biki ya samo asali ne tun a shekarar 1901, a lokacin shigar da Najeriya cikin rundunar sojojin kasashen yammacin Afrika, saboda al’adu daban-daban na sojojin kasashen yammacin Afirka, shi yasa mahukunta a wancan lokaci suka gabatar da WASA duk shekara domin sojoji su shiga.

 

Kwamandan ya yi nuni da cewa zaman lafiya da hadin kai da ake samu a cikin sojojin Najeriya sakamakon manufofin WASA ne a yankin yammacin Afirka.

 

Manjo Janar Ibikunle Ajose ya kuma duba irin nasarorin da rundunar ta samu kan yaki da ‘yan bindiga da sauran tashe-tashen hankula da ke faruwa a yankin Arewa maso Yamma .

 

Ya ce, a shekarar 2024, rundunar ta samu nasarar gudanar da ayyukanta na yaki da ayyukan bata gari a duk fadin Nijeriya.

 

Ya ce nasarorin da aka samu sun hada da kaddamar da runduna ta 248 ta Recce a Illelah, da tura babban hafsan soji na musamman na Bataliya ta 7 a karamar hukumar Gudu a jihar Sokoto da kaddamar da sabbin kayan aiki na sojojin sama da sauran makaman yaki a Sokoto.

 

A cewarsa, abubuwan da suka faru sun haifar da nasarori da dama a ayyukan sojoji na fadin yanki na 8.

 

A nasa jawabin, gwamnan jihar Sokoto, Ahmed Aliyu, wanda ya samu wakilcin mai ba shi shawara na musamman kan harkokin sana’o’i da tsaro, Kanar Ahmed Usman mai ritaya, ya yabawa kokarin rundunar na ci gaba da kulla alaka mai karfi da al’adunsu.

 

Aliyu ya ce bikin ya zama abin tunatarwa ne kan alhakin da ya rataya a wuyansu na bunkasa fahimtar juna, mutunta juna, da hadin kai a tsakanin kungiyoyi da al’ummomi daban-daban a yammacin Afirka.

 

NASIR MALALI/Wababe

উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa

কীওয়ার্ড: wasa yammacin Afirka

এছাড়াও পড়ুন:

Hauhawar farashi ya ragu a watan Agusta — NBS

Hukumar ƙididdigar a Najeriya NBS ta bayyana cewa an samu raguwar hauhawar farashin kaya a watan Agusta idan aka kwatanta da watan Yulin da ya gabace shi.

Cikin sabbin alƙaluman da NBS ta fitar a ranar Litinin sun nuna cewa an samu raguwar kashi 1.76 a watan Agustan saɓanin watan Yulin, wanda ya nuna karo na hudu ke nan a jere hauhawar farashin yana sauka.

NDLEA ta kama ɗan Indiya da ƙwaya ta Naira biliyan 3 a Legas Kundin Bajinta na Guinness ya taya Hilda Baci murna

Rahoton na hukumar NBS na zuwa ne kwanaki bayan da Shugaba Bola Tinubu ya bayar da umarnin karya farashin kayan abinci ƙasar.

A watanin baya-bayan an riƙa samun raguwar hauhawar farashin kayyaki a ƙasar.

Ko alƙaluman da NBS ta fitar a watan Yuni, ta bayyana cewa hauhawar farashi a Najeriya ya sauka zuwa kashi 22.22 daga 22.97 da aka samu a watan Mayu.

A baya dai dai an yi ta kiraye-kirayen gwamnatin ƙasar ta ɗauki matakan rage hauhawarar farashi domin magance tsadar rayuwa da ake fuskanta a ƙasar.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • UNICEF Ya Ba Da Tallafin Kayayyakin Aiki Ga Cibiyoyin Lafiya A Kirikasamma
  • Tinubu ya janye dokar ta-ɓaci da ya sanya a Ribas
  • Shawarwarin Sin: Ingantattun Hanyoyi Masu Sauki Na Warware Sabani
  • Tinubu Ya Taya Amusan Da Gumel Murnar Samun Nasarori A Ɓangarori Daban-daban
  • Sin Ta Daga Zuwa Mataki Na 10 A Jadawalin GII Na Kasashen Dake Kan Gaba A Fannin Kirkire-Kirkire
  • Baqa’i: Kowace Kasa A Duniya Tana Da Hakkin Mallakar Makamashin Nukiliya Na Zaman Lafiya
  • ’Yan bindiga sun kai wa sojoji hari a ranar da ake zaman sulhu
  • Hauhawar farashi ya ragu a watan Agusta — NBS
  • Tattalin Arzikin Sin Ya Samu Ci Gaba Ba Tare Da Tangarda Ba A Watan Agusta
  • Rabin Sojojin Isra’ila da suka ji rauni a yakin Gaza na fama da ciwon damuwa